Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 464

‘Yan Nijeriya na ci gaba da murnar nasarar da Super Eagles ta samu na doke Angola da ci 1-0

Super Eagles ta doke Angola da ci daya da nema, inda ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Cote d’Ivoire yau Juma’a.

Kwallon wanda Ademola Lookman ya zura a minti na 41 ya baiwa Nijeriya nasara.

An fafata tsakanin kasashen biyu a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny mai daukar mutane 33,000 da ke birnin Abidjan.

Tsadar fulawa ta sa masu sana’ar gurasa sun yi zanga-zanga a Kano

Mata masu sana’ar Gurasa sun fito kan titunan birnin Kano don nuna damuwarsu da tsadar fulawa, inda suka yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kawo musu dauki.

Shugabar matan masu sana’ar gurasar, Fatima Auwal Chediyar ‘Yan gurasa, ta ce kafin yanzu, a da, suna sayen buhun N16,000 amma cikin kasa da wata guda farashin ya tashi zuwa N43,000.

Fatima ta kara da cewa an kori ‘ya’yansu daga makaranta domin ba za su iya daukar nauyin karatun su ba da sana’ar da suke da ita ba.

INEC ta yi rantsuwar gudanar da zabe cikin adalci a Adamawa

0

Jami’an Hukumar Zabe a jihar Adamawa sun yi rantsuwar gudanar da zabukan cike gurbi a mazabar Mayo-Belwa da za’a gudanar gobe Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da zaben ne a sassa bakwai na mazabar tsakanin Ibrahim Musa na jam’iyyar APC da kuma Musa Mahmud na jam’iyyar PDP.

Jami’an zabe 28 ne da suka hada da jami’an tattara sakamakon zabe hudu, da masu sa ido su 13 da dai sauransu.

Gwamnonin PDP sun bukaci a samar da yan sandan jihohi a Najeriya

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun koka kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, inda suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da yan sandan jihohi.

Gwamnonin sun yi wannan kira ne a jiya Alhamis a Jos, babban birnin jihar Filato lokacin da suka ziyarci gwamna Caleb Mutfwang, a gidan gwamnatin jihar, biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai, wanda ya yi sanadin asarar rayuka sama da 200 a cikin wata guda tare da lalata dukiyoyin na miliyoyin Nairori.

Gwamnonin da suka kai ziyarar sun hada da Seyi Makinde na jihar Oyo, Ahmadu Fintiri na jahar Adamawa da Peter Mbah na jihar Enugu da Godwin Obaseki na Edo da Ademola Adeleke na Jihar Osun.

Shugaba Erdogan ya karbi bakuncin Firaministan Nijar

0

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Firaministan gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine a ranar alhamis din nan a fadar gwamnatin sa da ke Ankara.

Batun karfafa dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu shine abinda ganawar tasu ta maida hankali

Nijar dai tun da ta raba gari da uwar gijiyarta Faransa take kokari karfafa dangantakar ta da wasu manyan kasashen gabashin Turai irin su Rasha, da Turkiyya

Shugaba Erdogan ya karbi bakuncin Firaministan Nijar

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Firaministan gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine a ranar alhamis din nan a fadar gwamnatin sa da ke Ankara

Batun karfafa dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu shine abinda ganawar tasu ta maida hankali

Nijar dai tun da ta raba gari da uwar gijiyarta Faransa take kokari karfafa dangantakar ta da wasu manyan kasashen gabashin Turai irin su Rasha, da Turkiyya

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun dakatar da kungiyar ‘yan jaridu ta kasa

0

 

Ministan cikin gidan Nijar  janar Toumba ya dauki wannan mataki a cikin wani kudurin doka da ya saka wa hannu a ranar 29 Janairun wannan shekara ta 2024 inda a ciki ya sanar da rushe wannan kungiya har sai baba ta gani

Ko da yake ministan bai sanar da dalilansa ba na daukan matakin amma ya maye gurbin membobin nata da sakatarorin ma’aikatar sa da ta sadarwa wadanda za su jagorancin aikin kungiyar na wani lokaci

To amma sai dai shugaban kungiyar ta Maison de la Presse Ibrahim Harouna ya ce basu da labarin wannan mataki domin kuwa basu samu takarda a hukumance da ta dakatar da ayyukan nasu duk kuwa da yadda take yawo a shafukan sada zumanta na zamani

Kotu tabayar da belin Abdulmajeed Dan bilki kwamanda bisa wasu sharruda.

Wata kotu dake zaman ta a Kano, ƙarkashin jagorancin mai shari’a Abdulaziz Habib, ta bayar da belin Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda bisa wasu sharuddan.

Sharuɗan belin sun haɗa da gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa, Hakimi a Kano ko Sakatare na din-dindin ko kuma bayar da Naira Miliyan daya idan ba’a samu wadannan mutane ba.

Daga bisani an ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga wannan watan da muke ciki na Fabrairu.

An dai tsare fitaccen dan siyasar ne kan kalaman batanci da ya yi wa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Mutane milyan 11.71 ke amfani da lantarki a Nijeriya

Adadin masu amfani da wutar lantarki a Najeriya ya ƙaru da kashi 2.08 cikin 100, daga miliyan 11.47 zuwa miliyan 11.71 na masu amfani da wutar a shekarar 2023.

Bayanin hakan na a cikin wani rahoto da hukumar ƙididdiga ta Ƙasa ta bayyana a yau Alhamis a Abuja.

Rahotan ya ce a duk shekara, adadin masu amfani da wutar lantarki na ƙaruwa, ko a shekarar 2022 an samu ƙaruwar masu amfani da wutar daya kai mutum miliyan 10.94.

Mutane milyan 11.71 ke amfani da lantarki a Nijeriya

Adadin masu amfani da wutar lantarki a Najeriya ya ƙaru da kashi 2.08 cikin 100, daga miliyan 11.47 zuwa miliyan 11.71 na masu amfani da wutar a shekarar 2023.
Bayanin hakan na a cikin wani rahoto da hukumar ƙididdiga ta Ƙasa ta bayyana a yau Alhamis a Abuja.
Rahotan ya ce a duk shekara, adadin masu amfani da wutar lantarki na ƙaruwa, ko a shekarar 2022 an samu ƙaruwar masu amfani da wutar daya kai mutum miliyan 10.94.