Matashi mai shekaru 35 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 55 fyade har ta mutu
Atiku ya soki Tinubu kan matsalar tsaro a Nijeriya.
Atiku ya soki Tinubu kan matsalar tsaro a Nijeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan gazawarsa wajen magance matsalar tsaro a kasar.
Atiku, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya mayar da martani ne kan yawaitar sace-sacen jama’a da kashe-kashen da ake yi a fadin kasar nan.
Atiku ya bayyana damuwar sa kan dalilin da ya sa shugaban kasar ya fara wata ziyarar sirri a kasar Faransa a daidai lokacin da ‘yan fashi da makami da sauran matsalolin tsaro dake kara samun wajen zama a kasar.
Gwamnatin Nasarawa ta musanta sanya hannu wajen kafa kungiyar ’yan banga ta Fulani a jihar.
Gwamnatin Nasarawa ta musanta sanya hannu wajen kafa kungiyar ’yan banga ta Fulani a jihar.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta da hannu wajen kafa kungiyar ’yan banga ta Fulani da aka kafa kwanan nan a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Danladi Jatau domin taya shi murna bisa samun nassara da yayi a kotun koli a fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta zaman lafiya a jihar,inda jaddada cewa tuni jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin ‘yan banga na Fulani.
Ya ce da a ce matakin daga gwamnati ne, da an aika da kudirin dokar ga majalisar dokokin jihar domin tantance wa saboda haka basuda wata masaninya akan kaddamar da yan bangar.
NDLEA ta kama mutane 198 da ake zargi da safarar kwayoyi a Kano.
NDLEA ta kama mutane 198 da ake zargi da safarar kwayoyi a Kano
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da tarwatsa mahadar da ake tattaruwa don safarar miyagun kwayoyi guda 21 a Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar a jihar Kano Sadiq Muhammad-Maigatari ya raba wa manema labarai a Kano.
Ya ce an kama su ne a tsakanin 17 zuwa 26 ga watan Janairu, a cikin shirin hukumar na “Operation Hana Maye” da Kwamandan Hukumar Abubakar Idris-Ahmad ya kaddamar domin yaki da shaye shaye.
A cewarsa, daga cikin mutane 198 da aka kama, 177 maza ne, 21 kuma mata ne.
Sojojin sama na bin hukumar zaben INEC bashi a Nijeriya.
Sojojin sama na bin hukumar zaben INEC bashi a Nijeriya.
Shugaban hafsan sojin saman Nijeriya Air Marshal Hassan Bala Abubakar, ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (INEC) da ta biya wasu basuka da sojojin na sama ke bin ta.
Abubakar Hassan ya yi wannan kiran ne a Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar hukumar ta INEC, karkashin jagorancin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, da suka ziyarci hedikwatar rundunar sojin sama.
Yace ya yi amfani da wannan dama domin tunatar da shugaban INEC cewa akwai kudaden sojojin samar ke bin hukumar INEC da ya kamata a ce an biya.
Kuma biyan wannan kudaden zai ba rundunar ta sojin sama damar, ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin walwala da kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Zulum ya umurci ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu a rajistar zuwa aiki.
Zulum ya umurci ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu a rajistar zuwa aiki
Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta samar da na’urar daukar bayanai ga shugabannin kananan hukumomin jihar.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umarci shugabannin kananan hukumomin da su zauna a yankunansu inda ya bukace su da su sanya hannu a rajistar zuwa aiki a kullum domin tabbatar da kasancewarsu a wuraren aikinsu.
Zulum ya ba da umarnin ne a Maiduguri, babban birnin jihar, yayin da ya jagoranci bikin rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomi 27.
Gwamnan ya umurci ma’aikatar kananan hukumomi da ta gaggauta tura na’urorin daukar bayanai na biometric zuwa kananan hukumomin domin shugabanninsu su rika buga babban yatsa a kullum da karfe 8 na safe, na rana, 2 na rana ko kuma karfe 3:30pm.
Ya ce matakin ya zama dole domin duba rashin zuwa aiki ko kuma kauce wa aiki da kowane shugaba ba tare da dalili na gaske ba kamar yadda wasu yi a baya.
Gwamnan ya bayyana cewa yadda ake samun ingantaccen tsaro a fadin jihar, akwai bukatar shugabannin kananan hukumomin su kasance tare da jama’arsu domin tallafa wa kudirin gwamnatinsa na gyara, sake ginawa, da kuma tsugunar da ‘yan gudun hijira a jihar inda
ya bukace su da su sarrafa karancin albarkatun kananan hukumomin bisa adalci da rikon amana.









%20(1).jpeg)