Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 466

An kama shugaban jam’iyyar PDP da ake zargi da safarar makamai zuwa jihar Zamfara

Jami’an tsaron hadin guiwa sun ce sun yi nasarar kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai ga barayin daji a jihar Zamfara.
An gano cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Aminu Ibrahim shi ne shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Birnin Yero ta karamar hukumar Shinkafin jihar, kamar yadda jaridun Solacebase da PRNigeria suka samu tabbacin zargin daga majiyoyi na soji a Zamfara.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa an kama mutanen ukun a ranar Litinin da ta gabata.

Zargin kisan kai ya sa an tsare shugaban karamar hukuma gidan yari a Katsina

Kotun Majistare da ke zamanta a Katsina ta tsare shugaban karamar hukumar Batagarawa Alhaji Bala Garba Tsanni a gidan yari bisa zarginsa da kisa, satar mutum.
Ana zargin shugaban karamar hukumar tare da karin wasu mutane 11 da kisan Dagacin garin Dabaibayawa a cikin karamar hukumar Batagarawa ta jihar, Marigayi Alhaji Dikko Ahmad.
An dai gabatar da su gaban kotu ne karkashin sashe na 59, 249 da 189 na kundin penal code.
Tun da farko dai Alkalin kotun Majistare Abdulkarim A. Umar ya ba da umurni ga ‘yan sanda da su gabatar mata da wadanda ake zargi a ranar 25 ga watan Janairun, 2024.
Tsawon watanni 6 dai sauran mutanen 11 ke tsare a gidan yari, a yayin da aka ba da belin shugaban karamar hukumar.
Da suke gabatar da wadanda ake zargi da aikata wannan lamari, ‘yan sanda sun ce sun kammala bincike a kan batun.
A haka ne, Alkalin kotun ya umurci da a tsare shugaban karamar hukumar Bala Garba Tsanni a gidan yari har sai ranar 7 ga watan Maris mai zuwa na 2024.

Ba haka ake zawarcin shiga jam’iyya ba, Gwamna Abba ya yi wa Ganduje martani

 Ba haka ake zawarcin shiga jam’iyya ba, Gwamna Abba ya yi wa Ganduje martani

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf  ya ce ba shi da niyyar ficewa daga jam’iyyar sa ta (NNPP) da ya ci zabe a karkashinta. 

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne kwana daya bayan da shugaban jam’iyyar APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bashi goron gayyatar komawa jam’iyyar APC.

Gwamna Abba Kabir, wanda kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin Gwamnan jihar Kano a ranar Juma’a 12 ga watan Janairu shi ne kadai gwamna a jam’iyyar NNPP a Nijeriya.

A yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ya gudana a  Kano, Ganduje ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir tare da mambobinsa da magoya bayansa na jam’iyyar NNPP da su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa domin tabbatar da ci gaban siyasar jihar Kano.

Tinubu na rokon Super Eagles da su doke Kamaru a gasar AFCON.

 Tinubu na rokon Super Eagles da su doke Kamaru a gasar AFCON

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya roki ‘yan wasan Super Eagles da su yi duk mai yiwuwa don ganin sun samu nasara a yayin da Najeriya zasu fafata da babbar abokiyar hamayyarta, Kamaru a gobe, domin buga wasan dab da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Cote d’Ivoire. .

An isar da sakon shugaban kasar ga tawagar ta hannun ministan raya wasanni, Sanata John Owan Enoh, inda ya bukaci Super Eagles da su jajirce wajen tunkarar abokan karawarsu a wasan zagaye na 16 mai mahimmanci na gobe asabar.

Kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiya ta musamman ga sanata Enoh, Diana-Mary Tiku Nsan, ta bayyana cewa ‘yan Super Eagles sun sanar da cewa shugaban kasar na bin kungiyar ne domin yayi duk abinda ya dace a kansu, don haka dole ne su rubanya kokarinsu domin ‘yan Nijeriya da suke gida su samu Farin ciki da wannan wasa .

‘Yan Nijeriya na bukatar cikakken bayani kan bashin Dala bilyan 3.3 na kamfanin NNPC.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya kan bashin gaggawa na dala biliyan 3.3 na biyan danyen man fetur, Inda yabayyana cewa yan Nijeriya na bin gwamnati bayani akan batun bashin.

Atiku ya bayyana hakanne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a abuja inda yake cewa kamata yayi gwamnati ta dunga fito da bayanai da al’ummar kasa zasu fahimta bawai tayi shiru ba. 

Gwamnatin tarayya dai tun a shekarar da ta gabata, 16 ga watan Agusta, 2023, ta samu lamuni ta hannun kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) domin bayadda bashin dala biliyan 3.3.

‘Yan bindigar da suka sace mutane 31 a Katsina na neman kudin fansa Naira milyan 60

‘Yan bindigar da suka sace mutane 31 a kauyen Tashar Nagulle cikin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun ce ba za su sako wadannan mutanen ba sai an ba su kudin fansa Naira milyan 60.
Al’ummar yankin ne dai suka sanar da hakan ga jaridar Premium Times a Katsina.
A daren Lahadin da ta gabata ne dai wasu mahara dauke da makamai sun afka kauyen Tashar Nagulle sanye da kayan sojoji, inda suka yaudari al’ummar kauyen cewa su jami’an tsaro ne an turo su ne su kare rayukansu. Sai da mutanen kauyen suka nutsu, sai suka tattara su suka nufi daji su.
‘Yan ta’addar dai sun yi amfani da wayar daya daga cikin mutanen da aka sace, suka kira iyalansa, suka nemi da su kai wa Mai Unguwar kauyen don su yi magana da shi.

Yadda wani dan sanda ya ki karbar tayin cin hancin naira miliyan 1 daga hannun mai garkuwa da mutane

0

Wani dan sanda da ke aiki karkashin rundunar yan sanda ta jihar Kaduna ya
ki karbar cin hancin Naira miliyan 1 da wani kwararren mai garkuwa da mutane ya
bashi.

 

Bayanai sun ce yan sanda sun yiwa dan
garkuwa da mutanen kofar rago ne a wani Otal mai suna Tafa, kuma nan take yayi wa
dan sandan tayin naira miliyan 1 cikin kudin fansar da ya karba, sai dai dan
sandan ya ki karba.

Ko da yake jawabi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ASP Mansir
Hassan ya ce sun sami bayanan sirri ranar 19 ga watan da muke ciki na Agusta
cewa dan garkuwa da mutanen ya sauka a wannan Otal din nan take kuma suka aike
da jami’an su inda suka kama shi.

ASP Mansir ya ce an yi nasarar kwato sama
da naira miliyan 2 da dubu 350 a hannun mai garkuwa da mutanen da aka bayyana
sunan sa da Bello Muhammad mai shekaru 28 dan asalin jihar Zamfara.

Rahoton binciken farko-farko na yan sanda
ya nuna yadda dan bindigar ya shaida musu cewa yana cikin ‘yan ta’adda da ke
addabar yankin dajin Kagarko na jihar Kaduna.

 

 

Yadda gwamnatin Kebbi ta tube rawanin Hakimai

0

 

Gwamnan jihar Kebbi Dr. Naisr Idris

Gwamnatin Kebbi ta sallami wasu dagatai guda uku da ke karkashin
masarautar Gwandu daga kan mukaman su, a sakamakon kama su da laifin cin amanar
gwamnati, barin guraren aikinsu ba tare da izini ba, wasa da aiki da kuma cin
hanci da karbar rashawa.

Da yake sanar da sallamar dagatan guda uku shugaban
hukumar kula da kananan hukumomi ta jihar Alhaji Masur Shehu ya ce kokar ta su
na karkashin dokokin kula da da’ar ma’aikata ta jihar.

Dagatan da aka kora sun hadar da Alhaji Lawal Yakubu,
Mai Arewan Yeldu da Malam Ahmed Sani Sarkin Gabas din Geza da kuma Alhaji Tukur
Aliyu Jagwadejin Bakuwe.

Shehu ya ce hukumar ta jima tana bibiyar ayyukan dagatan kuma ta
tattara gamsassun hujojjin da suka tabbatar da cewa kora ce kadai hukuncin su.

Ya kuma ce kafin daukar wannan mataki
sai da gwamnati ta tuntubi majalisar masu rike da sarautar gargajiya, kuma suka
bada wannan shawara.

Shugaban Rasha Putin ya gana da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Chadi

Shugaba Vladimir Poutine na Rasha ya karbi bakuncin takwaransa na rikon kwaryar Chadi Mahamat Idriss Deby a fadar sa da ke Moscou
Batutuwa da dama ne dai aka tattauna a tsakanin shuwagabannin a yayin wannan ziyara
Kasar Rashar dai na dada samun karbiwa a wajen wasu kasashen Afirka masamman rainon Faransa wadanda dangantaka ke kara tsami tsakanin su da uwar gijiyar tasu
Kazalika wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kishiyar Rasha a Duniya wato Amurka ke son cigaban da rike matsayin ta a wajen kasashen na Afirka domin kuwa ko a cikin wannan mako sai da sakataren harakokin wajen ta Antony Blinken ya ziyarci kasashe hudu na nahiyar ciki kuwa har da Najeriya

Nijar ta karfafa hulda tsakaninta da Iran

Kasar Jamhuriyar musulinci ta Iran ta yi alkawalin karfafa tallafin da take ba wa jamhuriyar Nijar
Mahukunta birnin Teheran din sun bayyana hakan ne a yayin ziyarar Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya kai a kasar ta Iran bayan a makon da ya gabata ya kai irin ta a Rasha
Mataimakin shugaban kasar Iran din Muhammad Mukhber ya bayyana wa tawagar ta Nijar hakan inda ya ce kasar tasa za ta karfafa taimaka wa Nijar domin rage mata radadin takunkumin ECOWAS da aka kakabawa kasar tun bayan juyin mulki