Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 467

Kalaman sanata Ndume ba komai ba ne illa yukurin tunzura ‘yan arewa-Fadar shugabab kasa

0

Gwamnatin tarayya ta mayar wa da sanata Ali Ndume martani
game da kalaman da yayi da ke nuni da cewa gwamnatin na kullawa ‘yan arewa wata
makarkashiya, shine ma dalilin da ya sa zata mayar da wasu sassan CBN da
hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama zuwa jihar Lagos.

Ta cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce wannan
ba komai bane illa yunkurin tunzura ‘yan arewa a kan ‘yan kudu, kuma ba zai yi
nasara ba.

Kalaman na Sanata Ndume sun biyo bayan sanarwar
gwamnati na mayar da wasu sassa masu muhimmanci na babban bankin kasa CBN da
kuma hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama zuwa jihar Lagos ba tare da
bayar da wani gamsashen dalili ba.

Tun bayan fitar wannan labari ne ‚yan arewa ke mayar
da mabanbantan martani, yayin da wasu ke ganin wannan ba komai bane illa
yunkurin mayar da arewa saniyar ware, inda kuma wasu ke da ra’ayin cewa hakan wani
salo ne na shirin raba kasar.

Baya
ga wannan an kuma zargi gwamnatin ta Tinubu da yunkurin mayar da fadar shugaban
kasa kachokan zuwa jihar Lagos, sai dai tuni gwamnatin ta musanta wannan zargi.

Gwamnatin Kogi ta dakatar da albashin ma’aikatan 231. d

 Gwamnatin Kogi ta dakatar da albashin ma’aikata 231.

Gwamnatin jihar Kogi ta dakatar da biyan albashin ma’aikata 231 na ma’aikatan jihar bisa zargin kin bin umarnin gwamnati na sabunta bayanan su ga gwamnatin .

Shugabar ma’aikatan jihar (HOS), Hannah Odiyo, ta bayyana hakan Lokoja babban birnin jihar a wajen bikin kaddamar da katin shaida ga ma’aikatan jihar.

Odiyo tace ce ma’aikatan da abin ya shafa sun kasa bin umarnin gwamnatin jihar Kogi na sabunta bayanan su.

Hakan yasa hukumar ta dakatar da biyan albashin ma’aikatan da abin ya shafa tun watan Nuwamba 2023 har zuwa yau.

Saudi Arabia za ta amince a fara sayar da giya ga wadanda ba musulmi ba

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa wannan ne karon farko da ake sa ran kasar za ta dauki mataki irin wannan.

Wadanda ba musulmi ba na ofisoshin Jakadanci dai ne za su amfana da wannan mataki idan an dauka, ta yadda ba sai sun yi amfani da hanyar diflomasiyya ba wajen shigar da giyar a Saudi Arabia ba.

Doka ce mai karfi hana sayar da giya tun a shekarar 1952 a kasar Saudiyya.

Tinubu yabar Najeriya zuwa Kasar Faransa.

 Tinubu yabar Najeriya zuwa Kasar Faransa. 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yammacin Larabarnan ya bar Abuja zuwa Paris, babban birnin kasar Faransa, don wata ziyarar sirri.

 A wata sanarwa da mai bawa shugaban kasar  shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce shugaban zai dawo Najeriya a makon farko na watan Fabrairu.

Ajuri Ngelale ya bayyana cewa shugaban Zai yi ziyarar ne zuwa birnin Paris din don wata ziyarar sirri Wanda Ake sa ran zai shafe fiye da mako guda.

Sanata Ali Ndume ya gargadi Tinubu kan mayar da CBN da FAAN zuwa Lagos.

 Sanata Ali Ndume ya gargadi Tinubu kan mayar da Wasu ofisoshin CBN, da Ma’aikatar FAAN zuwa Lagos. 

 Sanata Ali Ndume, ya gargadi Shugaban Najeriya Bola Tinubu cewa za a samu matsala a siyasance idan har ya dage sai ya koma wasu ma’aikatun Babban Bankin Najeriya (CBN) da hedikwatar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN). zuwa Legas.

Ndume ya bayyana haka a wata hira da Yayi da manema labarai inda yake bayyana rashin amincewa da wannan mataki na shugaban kasa Tinubu domin wannan ba abune da zai haifarda  da mai ido ba a siyasance. 

Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne babban bankin kasa CBN, a wata sanarwa ta cikin gida tace, ta  mayar da wasu ofisoshinta zuwa Legas saboda cunkoson da wasu ma’aikatu ke yi.

Gwamnatin ta sanar da cewa za ta mayar da hedikwatar FAAN domin tabbatar da gudanar da ayyuka na musamman da kuma rage kashe kudade.

 

Gwamna Raɗɗa ya umarci jami’an gwamnatinsa su ayyana kadarorin da suka mallaka

0

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya bayar da tabbacin cewa duk masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati a jihar za su bayyana kadarorin su.

Raɗɗa ya bayar da wannan tabbacin ne a jiya Litinin a lokacin da ya karbi baƙuncin shugaban hukumar da’ar ma’aikata, Barista Murtala Aliyu Kankia, a fadar gwamnatin jihar.

A jawabin nasa shugaban hukumar da’ar ma’aikata, Barr. Aliyu Kankia ya bayyana irin rawar da Ofishin sa ke takawa, ba wai kawai sa ido kan bayanan kadarori ba, har ma da tabbatar da bin ka’idojin na da’a ga jami’an gwamnati.

Jami’an DSS sun cafke shugaban Miyetti Allah na ƙasa

0

Jami’an tsaro na farin kaya, sun kama shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo.

Rahotanni sunce kamun nasa ya biyo bayan kirkiro wata ƙungiyar yan sakai da Miyetti Allah ta ƙirƙira jihar Nasarawa.

An cafke Bodejo a yau Talata a babban ofishin Miyetti Allah da ke kusa da Cocin Goshen da misalin karfe 3:40 na yammacin yau Talata.

Ana zargin kwamishina da mallakar digiri ‘dan Kwatano’ Taraba

0

Ana zargin kwamishinan matasa da ci gaban wasanni na jihar Taraba Joseph Joshua da mallakar digiri na bogi daga wata jami’a a jamhuriyar Benin.

Zargin yana kunshe ne a cikin wata takardar ƙorafi da aka rubuta zuwa ga hukumar tsaro ta farin kaya da rundunar yan sandan jihar.

Wani lauya mai zaman kansa a jihar, Nasiru Muhammad, ne ya rubuta takardar koken a ranar 15 ga watan Janairu a madadin wani mai fafutuka Sulaiman Adamu.

Gwamnatin Taraba ta haramta zirga-zirgar babura

Gwamnatin jahar Taraba ta haramta amfani da babura kowane iri a cikin babban birnin jihar daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

A sanarwar da ta fito bayan taron kwamitin harkokin tsaro da gwamna Agbu Kefas ya naɗa ta ce an ɗau Matakin ne a kokarin  kawar da ayyukan bata gari a fadin jahar baki daya.

A yan makwanni da suka gabata anyi wa wani ma’aikacin gwamnati kisan gilla ta amfani da babur kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.

Tinubu na son a sulhunta tsakanin Kwankwaso da Ganduje

0
Ganduje da Kwankwaso 

Shugaba Tinubu ya fara yunkurin sasanta jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso da kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

A cewar jaridar Daily Trust wasu majiyoyi sun tabbatar mata a jiya Litinin cewa Tinubu ya bayyana aniyarsa ga shugabannin biyu na su sasanta kansu.

Wasu majiyoyi na kusa da Ganduje sun tabbatar da cewa Tinubu ya bukaci shugaban jam’iyyar da ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kano ranar Alhamis mai zuwa, tn are da fara aikin hadin kai a tsakaninsu.