Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 468

Wike zai haramta zirga-zirgar motocin haya marasa alamar Tãzi a Abuja

Ministan babban birnin tarayya Najeriya Nyesom Wike, ya ce nan ba da dadewa ba, hukumar gudanarwar babban birnin tarayyar za ta haramtawa motocin haya marasa fenti da ke nuna alamar tãzi yin aiki a kan titunan birnin ƙasar.

Ministan ya fadi hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, ya bayyana cewa shirin na da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi yankin. 

Jaridar Leadership ta ruwaito Wike yana jaddada bukatar daukar tsauraran matakai don kawar da duk wasu bata gari a ciki da wajen  birnin tarayya Abuja.

Jihohin katsina da Jigawa sune a kangaba wajen mutuwar mutane Dalilin Hatsari inji FRSC.

 Jihohin Katsina da Jigawa ne a sahun gaba wajen yawan mutuwar mutane ta dalilin hatsari a 2023 – FRSC

Hukumar Kiyaye aukuwar haddura ta kasa FRSC ta bayyana cewa a cikin Shekarar 2023,anfi Samun hatsari a hanyoyin, Jigawa, Katsina, Kwara da jihar Osun. 

Jami’in hukumar FRSC Dauda Ali Biu, ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai  yayi a yau litinin, Inda yace saboda Manyan motoci, dake tafiye tafiye a hanyoyin tareda motocin daukar kaya da rashin kyan hanya ya haifar da Lamarin. 

Yace sashin ‘Operation Zero Tolerance’ wani aiki ne na sintiri na musamman da rundunar ta fara a watan Disambar 2023 domin dakile hadurran ababen hawa a Kasar nan.

Tsakanin 15 ga Disamba, 2022, da 15 ga Janairu, 2024, kwamitin binciken ya gudanar da ayyuka na musamman, jimillar hadurran titunan da aka samu yakai 634 kuma  sun faru a duk fadin najeriya, sabanin 535 a wannan lokacin a shekarar 2022, wanda ya nuna karuwar kashi 19 cikin dari na hadduran dake faruwa a najeriya.

NAFDAC ta tabbatar da ingancin Paracetamol a Najeriya.

 NAFDAC ta tabbatar da ingancin Paracetamol a Nijeriya. 

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna da Kayan abinci ta kasa, NAFDAC, ta tabbatar da  maganin paracetamol da ake sayarwa a Najeriya sun cika ka’idojin hukumar.

Darakta Janar a Hukumar NAFDAC, Farfesa Christianah Adeyeye, ta bayyana haka a wani rahoto na baya-bayan nan da ke cewa kusan dukkanin Magani da alluran paracetamol a Najeriya karfinsu yayi  kasa  a matsayin ‘karya da rashin ingantaccen gwaji.

 

Wanda ta bayyana cewa wannan shine kashi 100% na izinin samun cikakken sakamakon gwajin compendia na samfuri 20 na allurai da magungunan paracetamol da aka gwada.

Inda aka inganta gwajin ta amfani da hanyoyin gwajin Pharmacopoeia na Burtaniya. Don haka maganin yanada ingantacciyar sahalewa wajen amfani dashi a Najeriya ba Kamar yadda ake Yada jita jita ba. 

Majalisar Dattawa zata gayyaci Wike kan matsalar tsaro a abuja.

 Majalisar dattawa za ta gayyaci Wike kan matsalar satar mutane a abuja. 

Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya abuja, Ireti Kingibe, ya ce majalisar dattawa za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan karuwar rashin tsaro da ayyukan ta’addanci a Abuja.

Kingibe, ya bayyana hakanne yayin zantawarsa da manema labarai a jiya Lahadi inda ya bayyana cewa Majalisar Dattawa za ta gayyaci Wike da shugabannin hukumomin tsaro kan yawaitar laifuka a abuja.

Yace, Lokacin da Majalisar Dattawa ta dawo aiki, an shirya cewa kwamitin (Majalisar Dattawa) na bukatar ya zauna da ministocin biyu da hukumomin tsaro domin su basu tsare-tsarensu na tsaro domin Kawo Karshen matsalar tsaron a abujar. 

wannan shi ne tsarin da ake gani zai kare al’ummar babban birnin tarayyar abuja. domin da ministan abuja, Kwamishinan yansanda da shugaban DSS, Yakamata suyi tsari maikyau wajen kawarda  Matsalar tsaro a yankin. 

 

Matashi ya hallaka abokin aikinsa a Ja’en da ke Kano

0



Wani matashi ma’aikacin wani kamfani a Kano ya halaka abokin aikinsa a unguwar Ja’en. 
Kawo yanzu ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun jefa borkonon tsohuwa domin kwantar da hankali bayan wata hatsaniya da ta biyo bayan lamarin. 
Mai magana da yawun ‘yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun tura jami’ansu don dawo da doka da oda, amma ya ce kawo yanzu suna kan tattara bayanan dalilin kisan da ma sauran abubuwan da suka faru a kan lamarin.

Bakin talaucin da ya addabi Nijeriya ya ragu da kaso 7%, inji Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi kiyasin cewa bakin talaucin da ake fama da shi a kasashen Nijeriya da Tanzania ya ragu da kaso 7% a cikin shekaru uku da suka gabata.
A cikin wani babban kundi da bankin duniyar ya fitar, ya sanar cewa a cikin shekaru ukun, an kuma samu karuwar samun aikin yi da kaso 8% a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
A cikin kundin, babban mai bibiyar tattalin arzikin Nahiyar Afrika na bankin duniya, Mr Andrew Dabalen, ya sanar cewa hakan ta faru ne ta dalilin amfani da kafafen sadarwar zamani da wayoyin hannu na salula.

Kotu ta umurci gwamnatin Nijar ta biya diyyar daliban da gobara ta hallaka a Maradi

0

 

Wata kotu a jihar Maradi ta umauci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta biya diyyar yara daliban da gobara ta hallaka su a cikin aji.

Babban kotun jihar Maradi ta a umarci gwamnatin Nijar da ta biya milyan 15 na CFA a matsayin diyyar ko wani dalibi da gobara ta hallaka a cikin aji su 34 a ranar 8 ga watan Niwembar 2021

Kazalika kotun ta ce gwamnatin ta biya dalibai 10 da suka ji munanan raunuka milyan 10 na CFA kowannensu.

Za a sake duba batun masarautun Kano – Kwankwaso

0
Sanata Rabiu Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa za a sake duba batun masarautar jihar Kano.

Hakan dai na a cikin wata hira da manema labarai da yayi a ranar Alhamis. Idan zaku tuna tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta raba masarautar Kano gida biyar, sana ta tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu daga karagar mulki.

Tun bayan da kotun koli ta tabbatar da zaben Gwamnan jihar  Abba Yusuf Yusuf, jama’a ke ta kiraye-kiraye na a  dawo da tsohun Sarkin.

Gwamnonin Kaduna, Nasarawa, Kebbi da Gombe sun tsallake siradin kotun koli

Kotun kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Isah Ashiru suka shigar kan nasarar APC a jihar.
A yanzu haka dai kotun kolin ta yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnoni a jihohi 13 da suka hada da Delta da Kebbi da Nasarawa da Delta da Ogun da Gombe da dai sauransu. Kuma galibi ta bar wa gwamnonin da ke kan kujera mukamansa.

Kwastam sun kama taba sigari, giya, ashana da shaken ‘amuru’

Jami’an tsaron hadin guiwa da ke sintirin kan iyakokin kasar nan da ke kula da arewa maso yamma sun sanar da cewa sun yi nasarar kama katan 34 na taba sigari da kwalaben giya.
Kazalika, jami’an sun kuma kama tirela shakare da ashana ta kasar waje da kuma tirela makare da dilolin shadda.
Kwantrolan kwastam da ke kula da shirin Mr IK Oladeji ya sanar a Katsina cewa jami’an sun kuma you nasarar katan 56 na sonadarin mimido da katan 76 na kuskus da ma tirela cike da dilolin gwanjo.
Ya kara da cewa a cikin jihohi 7 da shirin ke kula da shi, an yi nasarar kama ‘yan kasashen waje 21 da suka yi yunkurin shigowa Nijeriya ba bisa ka’ida ba, ta kasar Nijar duk kuwa da sanar da rufe boda da aka yi bayan juyin mulkin soji.
Kwastam din sun sanar cewa sun kuma kama katan 32 na maganin mura wato syrup da buhunan tabar ‘amuru’ da ake shake da ita da ma katan 39 na taliyar spaghetti.
Kazalika, kamen na kwastam bai tsaya nan ba, sai da suka sanar da cewa sun kama katan 1,700na maganin feshin gona da jarkokin man girki 10 da dilolin gwanjo da kuma katan 82 na alawar tsotsa ta lollipop.
Kwantrolan kwastam IK Oladeji ya kara da cewa jami’ansa sun kuma kama buhunan shinkafa 132, sannan sun yi gwanjon man fetur jarkoki 60 da suka kama ga al’ummar jihar Katsina da aka sayar musu kan farashi mai rahusa da ya ce tuni sun saka kudin a asusun gwamnatin tarayya.
Ya ce kudin dutin kayan da aka yi nasarar kamawa cikin makonni biyu daga 2 zuwa 17 ga Janairu, sun kai Naira bilyan 1.2bn