Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 469

Buhari ya gaza samar da tsaro a tsawon shekaru, Tinubu na neman nanata irin kuskuren – Peter Obi

Dan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar LP a zaben 2023 Mr Peter Obi ya ce tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ya gaza samar da tsaro a kasar nan cikin shekaru 8 da ya shafe yana mulkar kasar.
Peter Obi ya kara da cewa abin takaici, yanzu kuma shugaba Tinubu ba neman nanata irin wannan kuskure na gaza samar da tsaro bayan da karbi jagorancin kasar.
Ya yi kira ga gwamnatin da ta nutsu ta bullo da hanyoyin samar da tsaro a lungu da sako na kasar nan.
Peter Obi dai na magana ne kan sabbin hare-haren da ke neman kunno kai musamman a sassan birnin tarayya Abuja.

‘Yan siyasa ne ke dagula harkokin zabe a Nijeriya – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya yi kukan cewa da yawa daga cikin ‘yan siyasar kasar ne ke dagula lamurran zabukan da ake gudanarwa.
Ganduje na magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin daraktar sa ido kan harkokin zabe da jam’iyyun siyasa Hawa Habibu, inda ya ce yana sane cewa babbar matsalar gudanar da zabe a Nijeriya ita ce batun tsaro, amma ba haka bane, ‘yan siyasa ne babbar matsalar.
Ya ce akwai bukatar hukumar zabe INEC ta bullo da tsarin fadakar da jama’a kan illolin yin karan-tsaye ga harkokin zabe.

Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na farko a 2024

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jagoranci taron farko na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) bayan hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Taron wanda ake gudanarwa a fadar shugaban kasa ya samu halartar ministoci da sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da kuma shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.
NAN ta ruwaito cewa kafin a fara taron FEC, shugaban ya rantsar da Desmond Akawor a matsayin kwamishinan tarayya mai kula da tattara kudaden shiga, rarrabawa da kuma kasafin kudi (RMAFC).
An nada sabon kwamishinan tarayya na RMAFC, bayan rasuwar tsohon kwamishinan RMAFC na tarayya daga Rivers, Asondu Temple, a ranar 1 ga Nuwamba 2023.

Za a kashe N32bn don kwaskwarima ga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro

Kimanin watanni 8 kenan da gina katafaren ginin da a yanzu haka hukumar kula da harkokin tsaro ta kasa ta ware Naira biliyan 31.915 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin yin sabbin gine-gine.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun yawaitar kashe-kashe da sace-sacen al’umma a wasu jihohin Nijeriya, ciki har da babban birnin tarayya Abuja, inda ‘yan bindiga ke sace jama’a daga gidajen su da wuraren kasuwancinsu.

A ranar 21 ga Maris, 2023, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da katafaren ginin ofishin harkokin tsaron na kasa da Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC), wadanda suka lakume biliyoyin Nairori.

A lokacin da yake kaddamar da wasu cibiyoyi guda biyu na zamani a Abuja, ya ce an yi su ne don inganta da magance matsalolin tsaro a kasar nan, musamman ta’addanci ayyukan bata gari.

Sabbin gine-ginen suna dauke da manya-manyan ofisoshi tareda babban dakin taro da cibiyoyin nazari da bincike.

Wani fasinja ya gartsawa ma’aikaciyar Jirgi cizo.

 Fasinja ya gartsa wa ma’aikaciyar jirgin sama cizo

Wani jirgin sama a kasar  Japan da ke kan hanyarsa ta  zuwa Amurka ya koma birnin Tokyo bayan da wani fasinja da ya bugu da giya ya ciji wata mata ma’aikaciyar jirgin da hakan ya tilasta wa matukin jirgin saukar gaggawa.

An ruwaito cewa mutumin mai shekaru 55 da ake kyautata zaton Ba’amurke ne, ya ciji matar a  hannunta, inda har ya ji mata  rauni, kamar yadda mai magana da yawun kamfanin All Nippon Airways ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Lamarin da ya sa matukan jirgin da fasinjoji 159 suka  zuwa filin jirgin Haneda, inda aka mika mutumin ga ‘yan sanda. 

Kafar yada labarai ta kasar Japan TBS ta ruwaito fasinjan yana fadawa masu binciken cewa “bai san ya aikata laifin ba”.

Gwamnatin Kano zata kashe Biliyan 8 wajen gina makarantun firamare 3.

 Gwamnatin jihar Kano za ta kashe N8bn a makarantun firamare guda 3.

Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar.

 A cewar Gwamna Abba kabir Yusuf, makarantun za su kasance da cikakkun wuraren karatu, wanda hakan zai ba da isasshen yanayi ga yaran da suka fito daga sassa daban daban da zasuyi karatu a makarantun don samun ingantaccen ilimi da samun ci gaba. 

Gwamnan ya ce za a samar da manyan makarantun ne a Yankuna Uku dake jihar kuma za’a samar da kayayyakin koyo na zamani don samar da ingantaccen Ilimi a makarantun. 

Ya kuma ce an ware naira biliyan 6 domin gyara dukkan makarantun firamare dake jihar. 

 Yace gwamnati ta amince da gyara wasu cibiyoyi na musamman guda 26 da tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya kirkiro dasu a lokacin gwamnatin sa kuma an kammala 17.

“Za mu ci gaba da ba da kulawa ga samar da kayan aikin koyarwa na yau da kullum dazai ba wa yaranmu damar samun ingantaccen yanayin koyo da koyarwa a jihar kano.

Mahaifiyar Gwamna Abba na addu’ar a mayar da Sanusi mukamin Sarkin Kano

0

A cikin wani fai fan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta an hango mahaifiyar gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, Hajiya Naja’atu Yusuf, na addu’o’in neman a mayar da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu akan karagar mulki. 

Indai za ku iya tunawa gwamnatin data shuɗe ta gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sauke sa.

Mahaifiyar Gwamnan ta yi addu’ar Allah ya mayar da tsohon sarkin kan karagar sarakunan ‘Gidan Dabo’ domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan da ya fara kafin a sauke shi.

Bidiyon wanda aka wallafa a ranar juma’a, wani bangarene na ziyarar taya murna biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ta tabbatar da zaben Abba Gida-Gida.

Buhari ya ziyarci Abuja tun bayan saukarsa daga mulki

0

A karon farko tun bayan da ya mika mulki ga Gwamnatin shugaba Tinubu Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci Abuja Babban birnin kasar a Talatar makon nan. 

Shugaban wanda ya halarci taron kaddamar da littafi wanda hadiminsa Femi Adesina ya wallafa dangane da yadda ya yi aiki tare da shugaba Buhari.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu tare da wasu jiga-jigan gwamnatinsa da ma tsofaffin hadiman gwamnatin Buhari sun halarci taro wanda aka gudanar a otal din Transcorp da ke Abuja.

Atiku ya yi martani kan cefanar da matatar man Fatakwal

0

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce Anƙi zaɓarsa saboda zai sayar da NNPC yanzu gashi gwamnatin Tinubu zata siyar.

Atiku ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na X.

Atiku dai ya mayar da martanin ne kan matakin da kamfanin na NNPC ya dauka na mika matatar mai ta Fatakwal ga wani kamfani mai zaman kansa domin ya cigaba da gudanar da aiki a cikin sa 

Ya bayyana cewa dole ne kamfanin man na NNPC ya bayyana wa ‘yan Najeriya abin da za su samu ta hanyar mika matatar ga kamfanin.

Sabuwar tsadar rayuwa ta tunkaro Nijeriya a 2024

0

Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ta karu da kusan kaso 34 cikin 100 a watan Disambar na shekarar 2023, daga kashi 32.83 da aka samu a watan Nuwamban shekarar ta 2023.

Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta na farashin kayayyaki, na watan Disambar shekarar data gabata 2023, wanda aka fitar a yau Litinin. Hakan ya nuna an samu karuwar kashi 2.72 cikin ɗari, idan aka kwatanta da adadi da aka samu a watan Nuwamba. 

Wannan dai ita ce tsadar abinci mafi muni da aka gani tun shekaru 28 da suka gabata, a cewar wasu majiyoyi. 

Hauhawar farashin ta samo asali ne sakamakon tashin farashin mai da burodi da hatsi da sauransu.