Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 470

Tinubu ya kashe N3.4 wajen tafiye-tafiye tun hawansa mulki

0

Shugaba Tinubu ya kashe ƙasa da Naira biliyan 3.4 wajen tafiye-tafiyen cikin gida da ƙasashen waje a cikin watanni shida tun bayan ɗarewarsa mulki.

Adadin kuɗaden ya kai kashi 36 cikin 100 na N2.49bn da aka ware domin tafiye-tafiyen shugaban kasa a cikin kasafin kudin shekarar 2023 data gabata.

Shugaban kasar ya kuma amince da zunzurutun kudi har Naira biliyan 3 don siyan mota masu sulke kirar Mercedes Benz S-class 580 guda uku da kuma samar da wasu motoci a fadar gwamnatin sa.

A shekarar da ta gabata, Tinubu ya sha suka kan tafiya da ƴan rakiya taron majalisar dinkin Duniya kan sauyin yanayi, inda aka kashe N2.78bn.

‘Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Katsina

‘Yan ta’adda sun kai hari a sansanin sojoji da ke kauyen Nahuta na karamar hukumar Batsari a jihar Katsina
Majiyar DCL Hausa ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 11 na daren Lahadi wayewar Litinin, inda maharan suka shiga cikin gari suka debi dukiyoyin al’umma.
Bayanai sun ce maharan sun yi nasarar kona motocin sojojin guda biyu.
Kazalika, an ga wasu daga cikin mutanen kauyen Nahuta su na barowa a cikin motoci su na dawowa Batsari a wani abu kama da gudun hijra.
Bai dai fi kilomita 7 daga kauyen Nahuta zuwa cikin garin Batsari.

Sarkin Kano na 14 ya caccaki APC kan zaben Kano

0

Sarkin Kano na 14 , Muhammadu Sanusi II, ya caccaki ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC, a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, kan kin amincewa da kayen da yasha tun da farko.

Ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo na karatun da yake gabatar wa a shafukan sada zumunta.

Yace, tafiyar dan adawar kotun koli da ta daukaka kara, inda ya kai ga shan kayi, hakan ya nuna karara bai yadda da kaddara ba.

“Sun so su kwaci abinda mutane suka zaɓa da ƙarfi ta hannun Alkalai.”

“Dimokuraɗiyya ake, kuma al’umma su suka zabi abin su, hanasu abinda suka zaɓa zalunci ne.” inji tsohon Sarkin.

An kama barayin janareton masallaci a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da satar janareta da batirin da ke haska futilun masallaci mai amfani da hasken rana a wani masallaci da ke Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Mansir Hassan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kaduna ranar Asabar.
Mansir ya ce jami’an tsaro sun kama fara kama daya daga cikinsu mai suna Basiru Rabiu da ake zargin a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Hunkuyi.
Sanarwar ta bayyana cewa yadda aka hangi mutumin na labewa tare da yin kwanto a kusa da Masallacin Juma’a suka nuna shakku kuma aka kama shi.
Yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin cewa ya saci janareta da batir mai amfani da hasken rana a masallatan kauyen Hunkuyi da Nahuce.
Inda ya tabbtar da cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wani mutum msi suna Mansir Umar wanda shi ma yake a hannun jami’an tsaron.

Abba ya nada Ganduje mukami a Kano

0

 Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sanar da nada tsaffin gwamnonin jihar Kano, matsayin mambobin zauren dattawan jihar Kano.

Yayin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Gwamna Yusuf ya ce zauren zai kunshi tsaffin gwamnonin da mataimakansu da tsaffin shugabannin majalisa da mataimakansu da tsaffin alkalan kotun koli da na kotun daukaka kara ‘yan jihar Kano da tsaffin sanatoci da malaman addini. 

Labari mai alaka: Martanin Abba Gida-Gida kan hukuncin kotun koli

Gwamnan ya dora wa zauren alhakin bai wa gwamnati shawara ta karshe kan duk wani muhimmin batu da ya taso wa jihar Kano.

Labari mai alaka: Yadda magoya bayan NNPP suka yi murna a Kano

Tsadar shinkafa ‘yar Hausa ta gigita mutanen Kano

0

 

dcl hausa

Farashin Naira dubu 47,500 na buhun shinkafar gida ya ɗaga hankalin al’ummar Kano.

Wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa buhun shinkafa ta gida a yanzu ana siyar da ita kan N47,500.

Wani dan kasuwan shinkafa mai suna Alhaji Maikano Bello ya ce a zancen nan da ake, ana sayar da ton daya na shinkafa akan naira N450,000 sabanin N320,000 a watan Disamba na shekarar da ta  gabata da aka sayar.

Alhaji Mai-Kano Bello ya yi bayanin cewa yawaitar buqatar shinkafar ce ta jawo tsadar da ake fama da ita a dan lokacin nan.

Da yiwuwar EFCC ta ci gaba da binciken Bello Matawalle kan batun kudin da suka Naira bilyan 70

Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce a shirye take ta kakkabe batun nan da ke zargin tsohon Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan badakalar kudi Naira bilyan 70 a lokacin yana gwamna.
Da yake yi wa masu zanga-zanga bayani a hedikwatar hukumar, mukaddashin mai daraktan hulda da jama’a na hukumar Wilson Uwajaren, ya tabbatar musu da cewa za a yi adalci kan batun.
Da sanyin safiyar Juma’ar nan ne dai wasu mutane dauke da kwalaye karkashin kungiyar Zamfara Alternative Forum suka durfafi hedikwatar hukumar EFCC a Abuja inda suke neman hukumar da ta sake dawo da batun sabo kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Mr Uwajaren ya ce ba ma wannan batun ba, duk wani batu da ke gaban hukumar za a kakkabo shi, don tabbatar da an yi wa kowa adalci.

Murna bayan da Abba ya kayar da Gawuna a kotun koli

0

 

a tabbata Abba Zama Daram! Alkalan kotun kolin Najeriya sun bai wa duniya mamaki bayan da suka sanya kafa suka yi fatali da hukunce-hukuncen da kotun sauraren kararrakin zabe da ta daukaka kara suka yi, wanda ya kwacewa Abba Nasarar da tun farko hukumar zabe ta bashi.

Alkalan  kotun koli sun ce akwai lam’a cikin hukunce-hukuncen da kotunan suka yanke da farko, kuma babu yadda za’a yi su zuba idanu suna kallon wannan gagarumin kuskure ya wuce tun da dai ai su ba makafi bane, a don haka sun dawo wa da Engr. Abba Kabir Yusuf kuri’unsa  dubu 165 da kotun sauraren kararrakin zabe ta debe wa Abba tun da farko.

Alkalan sun ce sun jinge nasarar da kotunan da suka gabata suka bai wa jam’iyyar APC ta Dr. Nasiru Gawuna, kuma ma kada su sake jin an tayar da wannan magana ko da teburin mai shayi ne saboda kuskuren da kotunan biyu da suka gabata suka yi. 

Da ma dai Engr. Abba Kabir Yusuf shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri’u sama da miliyan daya, kuri’un da ake ganin kakaf Najeriya babu wani gwamna da ya taba samun makamantan su a tarihi. To amma duk da wannan hukunci, magoya bayan Dr. Gawuna wadanda a watannin da suka gabata suka yi ta mafarkin ganin gwanin na su a gidan Gilas, sun bayyana wa DCL Hausa martaninsu.

Da wannan hukuncin dai siyasar Kwankwasiyya ta kara samun karfi a jihar Kano kuma tuni magoya bayan jam’iyyar suka fara murna tare da yi wa juna farin cikin tsallake siradin da ya so ya yi awon gaba da nasarar da INEC ta ayyana musu tun da farko. Jami’in yada labarai na jam’iyyar NNPP Nuhu Yankaba shi ne ya fara bayyana wa DCL Hausa murnarsa.

To yanzu ko’ina makomar Dr. Nasiru Yuzusf Gawuna da jam’iyyarsa ta APC ke nan? Ga babban lauyan Najeriya Professor Lawan Yusufari.

A yanzu dai za a zura ido don ganin irin salon da siyasar jihar Kano za ta dauka bayan wannan hukunci da aka kwashe wata da watanni ana jiran zuwan sa zuwansa.  

A tarihin gwamnonin da suka Mulki jihar Kano ta hanyar siyasa Engr. Abba Kabir Yusuf shi ne na. Kafin wannan nasar da kotun koli ta tabbatar masa, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ne aka fara zaba a shekarar 1979 a jam’iyyar PRP, sai Alhaji Abdu Dawakin Tofa sai kuma Alhaji Sabo Bakin Zuwo, dukkaninsu ‘yan jam’iyyar PRP. Sanata  Kabiru Ibrahim Gaya ya take musu baya a jam’iyyar  NRC. Daga nan sai Rabi’u Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da kuma Abdullahi Umar Ganduje

Kotun koli ta yanke hukunci kan zaben Legas za’a koma kan na Bauchi

 Kotun koli ta yanke hukunci kan zaben Legas za koma kan na Bauchi

Kotun Ƙolin Nigeria ta tabbatar da gwamnan jihar Lagos Babajide Sanya- Olo a matsayin halastacce gwamnan jihar.

Kotun Ƙolin ta mai alƙalai guda 7 ta yanke hukuncin ne a yau juma’a.

Idan za’a iya tunawa  cewa jam’iyyar LP da dan takarar ta Rhodes Vivour ne suka daukaka karar bayan da suka ga cewa basu gamsu da hukuncin Kotun daukaka kara ba.

A yau Gawuna da Abba Gida-Gida za su san makomarsu a mulkin Kano

0

 

Rana ba ta karya, a yau ne kotun kolin Nijeriya za ta kawo karshen turka-turka da nuna wa juna yatsa da jam’iyyar APC da NNPP suka dade suna yi kan sahihancin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris na shekarar da ta gabata.

Engr. Abba Kabir Yusuf, shi ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’a sama da miliyan 1 yayin da babban abokin takararsa na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’u kimanin 890,000.

To sai dai kuma yayin da Abba da magoya bayansa ke tsaka da murnar samun wannan nasara, kwatsam sai kotun sauraren kararrakin zabe ta ce ba shi ne ya sami nasara ba saboda ta gano kuri’a sama a dubu 160 da aka ce ba su da shaidar tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, don haka na sata ne.

Wannan dai a ganin wasu na zama tamkar wani sabon abu, la’akari da yadda sad‘arar kundin dokar zabe ta 2022 ta ce ko da babu tambarin hukumar INEC a jikin takardar zabe matukar baturen zabe ya kirga ta to tana a matsayin halastacciyar kuri’a.

Jam’iyyar NNPP ba ta amince da wannan bayani na kotu ba don haka ta garzaya zuwa kotun daukaka kara, amma kuma can din ma da alama ba ta sauya zani ba, kasancewar alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Tribunal inda anan ma suka kara da cin tarar Abba Kabir Yusuf kudi har naira miliyan guda ladan bata wa Nasiru Yusuf Gawuna lokaci.

Kotun ta kuma kara fayyace manyan dalilan da suka yi wanchakali da nasarar Abba ciki kuwa har da rashin mallakar katin zama dan jam’iyyar NNPP kafin tsayawa takara, abin da ke nufin kai tsaye ma jam’iyyar ba ta da dan takara.

To amma abin da ya daure wa ‘yan jam’iyyar NNPP da dama kai shi ne yadda kotun ta iya bayyana wannan a matsayin hujjar kwace nasarar, kasancewar ta sha yanke hukunce-hukunce da ke cewa batun zama dan jam’iyya ko akasin haka kafin tsayawa takara ba hurumin kotu ba ne hurumin ‘ya’yan jam’iyya ne.

Wani babban da ya janyo cece-kuce shi ne yadda takardar hukunci ta nuna cewa Abba Kabir Yusuf ne ya yi nasara a kotun ba Gawuna ba, abin da wasu suka ce kalaman alkalan ya sha bambam da rubutunsu, lamarin da ya kara haifar da rudani tsakanin siyasar jihar Kano mai matukar muhimmanci a arewacin Nijeriya.

Maganin ka da ayi kar a fara! Watakila tun a wannan karin magana ya sa NNPP ta yi gaggawar kai kokenta gaban kotun koli don ta fayyace me wannan shubuha ke nufi da kuma ba ta karin hujjoji na ganin darikar siyasar Kwankwasiyya ta ci gaba da mulkin jihar Kano.

Shin mene ne manyan korafe-korafen jam’iyyar APC mai kara?

APC na zargin jam’iyyar NNPP da aringizon kuri’a da kuma amfani da kuri’un da ba su da inganci wajen kara yawan kuri’un da Abba Kabiru Yusuf ya samu.

Tana kuma zargin NNPP da hada kai da matasa wajen tayar da tarzoma a runfunan zaben da APC din ke da rinjayen magoya baya, a yayin da take ganin ya dace hukumar zabe ta ayyana zaben gwamna a matsayin wanda bai kammala ba, la’akari da cewa an ayyana na ‘yan majalisu da dama a matsayin wanda bai kammala ba, kuma a tare a ka yi su.

Korafi na uku shi ne yadda NNPP din ta gaza mika sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takara kafin cikar wa’adin da hukumar INEC ta kayyade.

Akwai kuma yadda shi gwamnan na Kano ya mallaki katin shaidar zama dan jam’iyyar NNPP bayan ya zama gwamna, abin da suka ce ya zama gwamna karkashin inuwar jam’iyyar ta NNPP amma lokacin kuma yana PDP.

Tawagar lauyoyin jam’iyyar ta APC sun biyo bayan wadannan hujjoji da suka bayyana wa kotu da bukatar ta kwace nasarar da Abba ya samu kuma ta mika ta ga Nasiru Gawuna ba tare da ba ta lokaci ba.

NNPP ta musanta

Da alama wadannan maganganu ba su zauna dai-dai a kunnuwan lauyoyin jam’iyyar NNPP musamman Bashir Tudun Wuzurci ba, kasancewar ya soke su ta hanyar fayyace wa kotu cewa babu wata ingantacciyar magana a ciki, kuma ma yana bukatar kotun ta yi watsi da su.

Da farko dai Barrista Bashir Tudunwuzurci ya ce ba gaskiya ba ne cewa NNPP din ta yi amfani da kuri’un bogi, a cewarsa ba ya cikin hakkin jam’iyya duba takardar kuri’ar da ke dauke da tambari ko akasin haka don haka idan akwai mai laifi bai wuce hukumar ta INEC ba, kuma bai kamata a hukunta jama’ar Kano da laifin da hukumar INEC din ta aikata ba.

Kan batun rashin katin zama dan jam’iyya kafin zabe kuwa, lauyan ya dage kan cewa Abba Kabir Yusuf yana da katin zama dan jam’iyya kafin ma ya tsaya takara don haka wannan farfaganda ce kawai ta abokan hamayya.

Yayin da yake zuba ingilishi a gaban alkalai, lauyan na NNPP ya ce jam’iyyar ta mika sunan Abba cikin lokaci kamar yadda doka ta tanada, don haka babu wani dalili da APC ta dogara da shi kan wannan zargi.

NNPP na ganin cewa karar da APC ta shigar bata lokaci ne da kuma yunkurin jefa kanawa sama da miliyan 1 da suka zabi Abba cikin fargaba don haka akwai bukatar kotu ta yi watsi da wannan kara.

Bahaushe yace ranar wanka ba’a boyen cibi, yau ne dai kowanne daga cikin mutanen da ke hammaya da juna zai san makomarsa kuma kowanne bangare na nuna kwarin gwiwar cewa kotun koli za ta biya masa bukata.

Yayin tattaunawarsa da DCL Hausa, lauyan masu kara wato APC Barista Abdul Fagge ya ce suna da yakinin a yau din ma sune da nasara kamar yadda suka samu a baya saboda hujjoji masu karfi da suka rika.

To amma da yake mayar da martani , a lokacin da wannan kafar yada labarai ta tuntube shi lauyan jam’iyyar NNPP ta Abba Gida-Gida Barista Bashir Tudunwuzurci ya ce yana da yakinin cewa Kotun Koli za ta yi watsi da wannan kara, la’akari da hukunce-hukunce makamantan wannan da ta yanke a baya.


Ga wasu abubuwa 6 masu muhimmanci kan wannan shari’a 

1-Wannan ba shi ne karon farko da kotun koli ke yanke hukunce-hukunce da ke da alaka da zaben gwamna ba.

2-Kotun kolin ta sha yin watsi da kararrakin da suka shafi rashin katin zama dan jam’iyya ga dan takara, wanda tace wannan abu ne na cikin gida, ma’ana dai ba ta da hurumi.

3-To sai dai wannan kuma ba zai zame wa jam’iyyar NNPP sandar duka ba, ganin cewa kotun daukaka kara ma ta sha yanke irin wannan hukunci amma a kan tasu karar ta sauya matsaya.

4-Hukumar INEC tana cikin wadanda suka daukaka kara, amma daga baya ta janye, shin me hakan ke nufi ga makomar NNPP a kotu? Kotun Koli za ta bayar da wannan amsa. 

5- Kotun Koli ta sha sauke wasu gwamnoni masu ci a baya. Amma babu tabbas a wannan karan ko Engr. Abba Kabir Yusuf zai iya tsallake wannan siradin.

6-Dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ba ya cikin wadanda suka shigar da kara, amma kuma yana cikin masu murnar jiran karbar shugabanci.

Sa’o’i kalilan suka rage kotun koli ta rufe babin ja-in-jar da jam’iyyun biyu ke yi, yayin da jama’ar Kano ke cike da zullumin me zai je ya dawo game da hukuncin mai cike da sarkakiya.

Shari’a dai mace ce da ciki, ba a san me za ta haifa ba.