Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 48

Gwamnatin Nijeriya za ta fara karbar harajin kaso 7.5 ga duk wanda ya yi amfani da banki daga 19 ga Janairun 2026

Gwamnatin Nijeriya ta umurci dukkan bankuna da kamfanonin fintech su fara karɓa da tura harajin VAT kashi 7.5 cikin 100 kan wasu ayyukan banki na zamani daga Litinin, 19 ga Janairu, 2026.

Harajin zai shafi kuɗaɗen hidimar banki irin su cajin tura kuɗi ta waya, USSD, da kuɗin fitar da kati, amma ba zai shafi kuɗin da ake turawa ba, sai cajin hidimar kawai. Misali, idan cajin tura kuɗi N100 ne, VAT zai zama N7.50 kamar yadda bankin Zamani na Moniepoint ya aike da sakonni ga kwastamominsa.

Kamfanin Moniepoint ya ce wannan ba ƙarin farashi ba ne, wajibi ne na doka, kuma ana tura kuɗin kai tsaye zuwa Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS). Ya ƙara da cewa ribar ajiyar kuɗi a asusu ba ta cikin harajin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, matakin na daga cikin shirin gwamnati na daidaita karɓar VAT a harkokin kuɗin dijital da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga, yayin da aka tabbatar wa kwastomomi cewa harajin na VAT za a rika nuna shi a fili a bayanan mu’amala.

Gwamnatin jihar Lagos ta fara gwajin lafiya ga maniyyata aikin hajjin 2026

0

Gwamnatin Jihar Lagos ta fara aikin duba lafiyar dukkan maniyyatan da ke shirin halartar aikin Hajjin shekarar 2026 a kasar Saudiyya. Sakataren Hukumar Jin Dadin Maniyyata Musulmi ta jihar, AbdulHakeem Ajomagberin, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Sanarwar, wadda Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a Taofeek Lawal ya sanya wa hannu, ta ce za a gudanar da aikin duba lafiyar daga Laraba 14 zuwa Asabar 24 ga Janairu, 2026, a cibiyoyi goma da aka tanada a fadin jihar Lagos, karkashin jagorancin Dr. Mazeedat Erinosho.

Ajomagberin ya bayyana cewa an rarraba kananan hukumomi zuwa cibiyoyin gwaji daban-daban domin saukaka wa maniyyata. Ya gargadi cewa duk maniyyacin da ya kasa halartar aikin duba lafiyar ba zai samu bizar shiga Saudiyya ba.

Haka kuma, hukumar ta nada jami’an jadawalin kananan hukumomi domin kula da jin dadin maniyyata kafin tafiya da kuma yayin aikin Hajji. Ajomagberin ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga nasarar aikin Hajji ba, yana mai bukatar jami’an da aka nada su nuna gaskiya da jajircewa.

Gwamnatin Nijeriya ta karfafi tawagar Super Eagles da kalaman kwarin guiwa gabanin wasansu da Morocco a wasan kusa da karshe na AFCON

0

Ministan yada labarai na Nijeriya, Mohammed Idris, ya yi kira ga tawagar Super Eagles da su kasance masu mayar da hankali da kwarin gwiwa yayin da suke shirin fuskantar Morocco a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin Afirka (AFCON) a daren Laraba.

A jawabin da ya wallafa a shafinsa na X, Idris ya yaba da yadda tawagar ta taka leda a gasar, yana mai cewa kowane wasa da suka buga ya nuna ladabi, jarumta, da imani, wanda ke tuna dalilin da yasa Super Eagles ke daga cikin manyan kungiyoyi a Afirka.

Ya kara da cewa, suna dauke da tarihi mai daraja a gasar Afirka. Daga nasarorin baya a AFCON zuwa nasarori kan manyan abokan hamayya, suna daukar tutar Najeriya da alfahari a koyaushe. Idris ya yi kira da su buga wasan cikin hadin kai, kwarin gwiwa, da nufin nasara.

A karshe, ministan ya ce, “Ku fita ku rubuta wani sabon babi mai alfahari a tarihin kwallon kafarmu. Ku buga da zuciya, ku buga da alfahari, ku buga don Nijeriya. Allah ya taimaka muku, Super Eagles. Allah ya taimaki Nijeriya.”

Gwamnatin Nijeriya ta dauki hayar kamfani a Amurka domin kare ta game da zargin cin zarafin Kiristoci kan Dala miliyan 9 – Daily Trust

0

Gwamnatin Nijeriya ta kulla yarjejeniya da wani kamfanin Amurka kan dala miliyan 9 domin bayyana kokarinta na kare Kiristoci da kuma tabbatar da goyon bayan Amurka a yaki da ta’addanci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, takardun Ma’aikatar Shari’a ta Amurka sun nuna cewa kamfanin Aster Legal ya dauki DCI Group a madadin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 17 ga Disamba, 2025.

Yarjejeniyar za ta dauki watanni shida, Nijeriya ta biya dala miliyan 4.5 tun farko, kuma ana biyan dala 750,000 duk wata. Matakin ya zo ne a lokacin da ake samun takaddama tsakanin Nijeriya da Amurka kan zargin cin zarafin Kiristoci, zargin da gwamnatin Nijeriya ta musanta.

Gwamnatin Nijeriya ta karrama sojojin kasar da lambar yabo ta kasa ciki har da Birgediya-Janar Uba da ya rasa ransa a hannun ‘yan ta’adda a Borno

0

Gwamnatin Nijeriya ta bai wa sojoji da tsofaffin hafsoshin Rundunar Sojan Nijeriya lambar yabo ta kasa saboda jajircewa, sadaukarwa, jagoranci da hidima ga kasa, ciki har da Brigediya Janar Musa Uba wanda ‘yan ta’adda suka hallaka a Borno.

An gabatar da lambobin yabon ne a bikin tunawa da ranar sojoji ta 2026 a dakin taro na Banquet na Fadar Gwamnatin Nijeriya a Abuja, inda Shugaban Sojan Kasa, Laftana Janar Waidi Shaibu, ya samu lambar Service and Sacrifice.

Brigediya Janar Uba ya samu Gallantry Award saboda nuna jarumta ta musamman da jagorantar sojoji a gaban fagen fama yayin yaki da ‘yan ta’adda a Borno, yayin da Brigediya Janar Usman Ahmad ya samu Mission Success Award kan rawar da ya taka wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda.

An kuma karrama wasu manyan hafsoshin soja, ciki har da tsohon shugaban sojin kasa, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd.) da tsofaffin sojoji kan gudummawarsu, yayin da Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Ministan labarai da, Mohammed Idris, ya shawarci rundunar soja ta cigaba da kasancewa masu ladabi, aminci da hadin kai wajen kare dimokuradiyya.

Gwamnatin Kano ta dakatar da likitocin da suka manta almakashi a cikin marar lafiyar da ya zama ajalinta

0

Hukumar Gudanar da Asibitoci ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa rashin kulawa ne ya janyo mutuwar Aishatu Umar, mahaifiya mai yara biyar, a Cibiyar Abubakar Imam ta Urology, bayan an bar almakashi a cikin jikinta bayan tiyata.

Hukumar ta dakatar da ma’aikata uku da suka shafi lamarin daga aiki, sannan ta mika batun ga Kwamitin Kula da Ka’idojin Likitoci na Jihar Kano don bincike da hukunci.

Iyalan marigayiyar sun nuna bakin ciki, yayin da mutane da dama a shafukan sada zumunta suka nemi a hukunta wadanda suka yi sakaci da kuma yin gyara a harkar lafiya.

Hukumar ta yi ta’aziyya ga iyalan marigayiya tare da tabbatar wa jama’a cewa irin wannan sakaci ba za a lamunta ba.

Ina fuskantar barazana saboda gyaran dokokin haraji – Taiwo Oyedele

0

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya ce yana fuskantar barazanar halaka sakamakon rawar da yake takawa wajen aiwatar da sabbin tsare-tsaren haraji a Nijeriya.

Oyedele ya bayyana haka ne an Abuja, yana cewa gyaran haraji yana taba muradun wasu mutane, lamarin da ke jawo adawa da barazana.

Ya ce ana kuskuren fahimtar gyaran, inda mutane ke zaton ana kara haraji ne, alhali ana ragewa da daidaita tsofaffi.

Ya bukaci ’yan Nijeriya masu goyon bayan gyaran su fito su yi magana, yana mai cewa sabon tsarin, duk da radadinsa, ita ce hanya daya tilo ta gyara tsarin harajin da ya gaza.

Nijeriya da UAE sun cire haraji kan dubban kayayyaki domin bunkasa kasuwanci

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa Nijeriya ta cire haraji kan kayayyaki 6,243 da ake shigo da su daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da UAE ta cire haraji kan kayayyaki 7,315 daga Nijeriya, a karkashin sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ta Nijeriya ta bayyana hakan ne a ranar Talata, inda ta ce yarjejeniyar Nigeria–UAE Comprehensive Economic Partnership Agreement (CEPA) da aka sanya wa hannu a Janairu 2026 za ta bude kasuwanni ga kayayyakin Nijeriya, da kuma bunkasa fitar da kaya ba tare da dogaro da man fetur ba.

A cewar ma’aikatar, Nijeriya za ta cire haraji nan take kan kaso mafi yawa na kayayyakin UAE, yayin da za a cire sauran cikin shekaru biyar. Haka nan, UAE za ta cire haraji nan take kan dubban kayayyakin noma da masana’antu daga Nijeriya, ciki har da kifi, hatsi, nama, ’ya’yan itatuwa, magunguna da kayayyakin sinadarai.

Gwamnatin Nijeriya ta ce yarjejeniyar za ta samar da karin zuba jari, ayyukan yi musamman ga matasa, tare da bai wa ’yan kasuwar Nijeriya damar shiga kasuwar UAE cikin sauki kuma za ta taimaka wajen karfafa tattalin arzikin Nijeriya a duniya.

Tsagin ADC na zawarcin Jonathan, Saraki da Makinde gabanin zaben 2027

0

Jam’iyyar ADC bangaren Nafi’u Gombe ta kara kaimi wajen fadada karfinta gabanin zaben 2027, inda ta yi kira ga tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, da sauran manyan ’yan siyasa su shiga jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne bayan kaddamar da Kwamitin Taron Yankin Arewa Maso Gabas, wanda ta ce wani muhimmin mataki ne na karfafa tsari a cikin gida da kuma shirya kanta don shugabanci a kasa. Shugaban jam’iyyar na tsagin, Nafiu Gombe, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa bayan taron da aka yi a Jihar Gombe ranar 11 ga Janairu.

A cikin sanarwar, ADC ta ce ta nada Patience Alex a matsayin shugabar Kwamitin Taron Yankin, yayin da Abayomi Adekunle ya zama shugaban Kwamitin Karbar Korafe-korafe. Jam’iyyar ta ce wannan mataki na nuna kudirinta na tabbatar da dimokuradiyya a cikinta da kuma gaskiya a harkokin jam’iyya.

ADC ta ce tana gayyatar manyan shugabanni irinsu Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri, Gwamnan Oyo Seyi Makinde, Gwamnan Abia Alex Otti, da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, tana mai cewa kwarewarsu na da muhimmanci wajen gina Nijeriya mai nagarta, hadin kai da ci-gaba mai dorewa gabanin zaben 2027.

Muna da cikakken bayani kan harin da Amurka ta kai a Jihar Sokoto amma ba za mu bayyana ba – Rundunar ‘yan sandan Nijeriya

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce tana da bayanai kan hare-haren sama da Amurka ta kai kan ’yan ta’adda a Jihar Sakkwato, amma ba za ta fitar da su ga jama’a ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan a ranar Talata, yana mai cewa batun ya shafi harkar tsaro.

Hundeyin ya ce an yi hadin gwiwa da wasu hukumomi, amma ya dace bangaren tsaron soja ne ya yi karin bayani. Ya jaddada cewa rundunar ’yan sanda ba za ta yi tsokaci kan cikakken aikin ba.

Hare-haren sun gudana ne a ranar 25 ga Disamba, 2025, inda Amurka ta ce ta hallaka ’yan ISIS da dama bisa amincewar gwamnatin Nijeriya.

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce Nijeriya ce ta bayar da bayanan sirri, yana mai jaddada cewa hadin gwiwar na cikin yaki da ta’addanci, ba tare da la’akari da addini ba.