Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 471

Hukumar Kwastam ta samu Karin kudaden shiga na Tiriliyon N3.206

0

Hukumar Kwastam a Najeriya ta ce ta tattara kudaden shiga na Naira Tiriliyan 3.206 a shekarar data gabata ta 2023, wanda hakan ya nuna cewa an samu karuwar kashi 21.4 a cikin dari daga Naira tiriliyan 2.64 da aka samu a shekarar 2022.

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam, Mista Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, a Abuja jiya Laraba.

Adewale Adeniyi yace hukumar ta samu gagarumin ci gaba ta hanyar tattara kudaden shiga na Naira tiriliyan 3.206, a shekarar 2023, wanda hakan ya nuna cewa an samu karin kashi 21.4% daga jimillar kudaden shiga na shekarar da ta gabata na Naira tiriliyan 2.641.

Sarkin Musulmi ya ce a sa ido dan dubar jinjirin watan Rajab

0

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, ya umurci al’ummar Musulmi su fara duba jinjirin watan Rajab daga Juma’a 12 ga watan Janairu.

Sanarwar duba watan na Rajab ta fito ne daga shugaban Kwamitin Ba da Shawarwari kan Al’amuran Addinin Musulunci, Farfesa Sambo Janaidu.

Yace, idan aka samu labarin jinjirin Watan sai a mika rahoton hakan ga Hakimi ko mai unguwa mafi kusa don sadarwa ga Sarki.

Kotu za ta yanke hukunci kan shari’ar Barr Muhyi a ranar Juma’a

Kotun kula da ma’aikata ta CCB da ke zamanta a Abuja, ta sanar da ranar Juma’a 12 ga watan Janairu, 2024 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar Barr Muhyi Magaji Rimin Gado.
Muhyi Rimin Gado dai shi ne shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano PCACC.
Kotun dai ta ba da wannan matsayar ne a Larabar nan bayan zaman da ta gudanar karkashin jagorancin Mai Shari’a Danladi Umar.
Kamfanin Dillancin labaran Nijeriya NAN ya ba da labarin cewa a ranar 16 ga watan Nuwambar 2023, kotun ta tsare Muhyi Magaji Rimin Gado, inda take tuhumarsa da laifuka 10.
Sai dai Barr Muhyi ya kiya amsa laifin, har ma ya nemi a ba da shi beli, karshe kotun ta ba da shi beli kan kudi Naira milyan 5 da masu tsaya masa guda biyu.

Dan majalisar tarayya ya fara gwangwaje al’ummar mazabarsa da ayyukan ci gaba a Katsina

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon Sani Aliyu DanLami ya ce zuwa karshen watan nan na Janairu, za a fara gudanar da ayyukan hanyoyin da ya sanar cewa za a gudanar a unguwanni daban-daban na karamar hukumar.
Sani Aliyu DanLami na magana da manema labarai dangane da ayyukan samar da ruwan sha da fitilu masu amfani da hasken rana da yake gudanarwa a karamar hukumar.
Ya ce za a gina hanyar da ta tashi daga Kofar Sauri zuwa Lambun Dan Lawal zuwa Yandadi ta wuce zuwa Bye Pass
Haka kuma, ya ce akwai hanyar da ta tashi daga Tashar Rabe zuwa Bye Pass, da wasu hanyoyin da ya ce ya nemo duk za a gudanar da ayyukan su.
Sanı Dan Lami ya ce cikin watanni hudu za a yi aikin a kammala, don haka al’umma su ba da gudunmuwa wajen ganin an yi aiki mai inganci domin ci gaban karamar hukumar da jihar Katsina bakidaya.

Sakataren gwamnatin Kano ya dawo gida bayan ya sha jinya a Saudiyya

0

 

Sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya dawo gida Nijeriya bayan ya shafe wasu kwanaki yana jinya a kasar Saudiyya.

Idan za a tuna ranar 7 ga watan Disamba ta shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta amince da nadin Abdullahi Musa, shugaban ma’aikata na jihar ta nada shi rikon kwarya.

Dawowar Sakataren gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da kotun koli ke shirin yanke hukuncin zaben gwamnan jihar.

Bichi ya sauka a filin jirgin sama na Aminu Kano, ya kuma samu tarba daga ‘yan uwa da abokan arziki.

Tsare wani lauya ba bisa ka’ida ba ya ci kujerar wani DPO a Lagos

0

Rahotanni daga jihar Legas na cewa an dakatar da baturen ‘yan sandan (DPO), na rukunin gidaje na Gowon bisa zarginsa da tsare wani lauya da ke neman adalci ga wanda yake karewa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da dakatar DPOn a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewar Hundeyin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Adegoke Fayoade, ya ba da umarnin dakatar da jami’in da gaggawa daga sashin.

Atiku ya yaba da matakin Tinubu kan su Betta Edu da Sadiya

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa shugaba Tinubu kan dakatar da ministar jin kai Betta Edu da ya yi.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar.

Atiku ya bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa ministar abin a yaba ne ga shugaban kasar.

An dai dakatar da ministar jin ƙan bisa zargir ta da tura Naira miliyan 585 zuwa wani asusu na daban.

Tinubu ya rage yawan kudaden da ake kashewa a tafiye-tafiye

0

 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da rage yawan kudaden da ake kashewa a tafiye-tafiyensa da na mataimakinsa da karin wasu mukarraban gwamnati.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, inda ya ce wannan sabon tsarin zai shafi tafiye-tafiyen shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da ma uwargidan shugaban kasar da sauran manyan jami’an gwamnati.

Yace tafiye-tafiye zuwa kasashen waje shugaban kasar zai tafi da mutane 20 da aka rage daga mutane 50 a baya, yayin da mataimakin shugaban kasa zai kasance da mutum biyar kawai, sannan kuma uwargidan shugaban kasar da mutane biyar.

Tafiye-tafiyen cikin gida kuwa, shugaban kasar zai samu rakiyar mutane 25, sai mataimakin shugaban kasar zai tafi da mutum 15 yayin da uwargidan shugaban kasa za ta tafi da mutane 10.

Sanarwar ta ce shugaban kasar ya rage yawan kudaden tafiye-tafiyen ne da kaso 60%.

INEC ta shirya gudanar da zabukan cike gurbi a Kano

0

Hakan ya fito daga bakin kwamishinan Zabe na Jihar Malam Abdu Zango, yace an shirya yin zaben ne ranar 3 ga watan Fabrairu.

A cewarsa wuraren da za a gudanar da zabukan sune Kunchi da Tsanyawa, Kura da Garun Malam sai Rimin Gado da Tofa.

Kwamishinan ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi da masu ruwa da tsaki a hedikwatarta da ke jihar a yau Talata.

Ya kara da cewa za a yi amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a na Bimodal BIVAS a yayin sake gudanar da zabukan da nufin tabbatar da sahihin zabe.

Ba mu da furofesoshin bogi – BUK

0

Jami’ar BUK da ke Kano ta musanta batun nan da ke cewa tana da furofesoshi na bogi har kusan 20.

Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Sagir Abbas ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba ma manema labarai a Kano.

“Mun ga wasu labarai da ke yawo a kafafen sada zumunta wai akwai wasu farfesoshi na bogi har guda 20 da ke aiki a jami’ar.

Abbas ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan labarin.

Sanarwar ta ƙara da cewa kwanan nan jami’ar ta kasance a matsayi ta 5 mafi inganci a Nijeriya.