Dakatattar ministar jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ta isa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), bisa zarginta da hannu a badakalar naira miliyan 585.
Idan dai za’a iya tunawa, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Dr Betta Edu akan mukaminta bisa wata badakalar kudin da suka kai Naira milyan 585.
An dai zargi ministan da tura wasu kudade a wani asusun banki na wani mutum, wanda hakan ya saba dokar kasa.
Dr Betta Edu, ta zama minista ta farko da aka dakatar daga aiki tun bayan rantsar da mambobin majalisar zartarwar ta tarayya a watan Agustan shekarar da ta gabata.
Fadar Elysée ce ta kasar Faransar ta sanar da hakan inda ta ce Elisabeth din ta mika wannan takarda ce ta murabus din tata da ta gwamnatin ta baki daya a ranar jiya litinin din nan 8 ga Janairu ga shugaban kasar Emmanuel Macron
A sakon da ya aike a shafinsa na X, shugaba Macron ya gode wa shugabar gwamnatin tasa mai barin gado dangane da aikin da ya ce ta yi ga kasar abin misali. Mrs Elisabeth dai da sauran membobin gwamnatin ta za su cigaba da wasu ayyukan yau da gobe har zuwa lokacin da za a nada sabuwar gwamnati.
Elisabeth Borne da aka nada a wannan mukami tun a watan Mayun 2022 ita ce mace ta biyu da ta rike wannan matsayi bayan Édith Cresson.
Tsohon shugaban Majalisar Dokokin tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Mamman Abubakar Danmusa ya bayar da shawarar kafa cibiyoyin koyar da sana’oi domin kawo karshen yawan kaura da matasa sukeyi zuwa wasu garuruwa.
Alhaji Mamman Abubakar Danmusa na magana ne a lokacin bikin kaddamarwa da hannanta cibiyar koyar da sana’oi mai azuzuwa biyar da ofisoshin malamai 2 da ya gina a garin Danmusa ga gwamnatin jahar katsina
Tsohon shugaban majalisar Dokokin ya bayyana cewa ya hananta cibiyar ne ga gwamnatin jiha don samar da kayan aiki da ake bukata ga cibiyar wanda zasu taimaka ma matasa marassa aikin yi koyon Sana’oi hannu.
Alhaji Mamman Abubakar Danmusa wanda ya samu wakilcin babban Dan’sa Nuradden Mamman Danmusa yace ya yanke shawarar kafa cibiyar horar da sana’oi ne don tallafawa matasa su zamo masu amfani acikin al’umma.
Daga nan sai ya bukaci masu hannu da shuni dasu rika kafa irin wadannan cibiyoyin don karfafama matasa gwaiwa wadanda sune kashin bayan al’umma.
Alhaji Mamman Abubakar Danmusa wanda ya taba zama mataimakin shugaban majalisar dattawa a jamhuriyya ta biyu ya bukaci matasa da su amfani da cibiyar domin dogaro da kai.
A jawabinshi bayan karbar makullin cibiyar amadadin shugabar hukumar bunkasa Sana’oi Aisha Aminu malumfashi, Daraktan shiyya na hukumar Alhaji kabir Abdullahi kofar soro ya yabama hangen nesan Mamman Danmusa bisa kafar cibiyar da yayi hadi da rawar da yake takawa don ciyar da yan’kin dama jiha baki bdaya.
Ya kuma bayyana kafa cibiyar amatsayin sadakatu jariya ga Mamman Abubakar Danmusa, inda ya jaddada cewa cibiyar zata samarwa matasa a bubuwa a yan’kin.
A jawabin godiya magajin malam Hakimin Danmusa Alhaji Darda’u muaazu Abubakar Danmusa wanda ya samu wakilcin wakili Gurza Alh Darda’u Gambo Danmusa ya yabama da irin gudumuwar da yake bayar wa ga cigaban yankin.
A jawabansu daban daban Sarkin kasuwa Bishir yusufa da murtala Amadu mai shanu da kuma Nura Abdu sun yaba da gudumuwar da mamman Abubakar Danmusa yake tallafama Al’ummar yankin, tare da rokon Allah ya sakama shi da mafificin allhairi.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu nan take.
Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.
Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.
Wasu yan Najeriya sun yi ta kiraye-kiraye ga gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta nata domin a gudanar da cikakken bincike game da zarge-zargen da ake mata.
Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa wani asusun banki da babban akanta janar na ƙasa yaki amincewa da shi.
Shugaba Tinubu a sanarwar da ta fito daga fadar sa ya umurci shugaban hukumar EFCC ya gudanar da bincike sosai kan zargin da ake wa Beta Edun.
Gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar ta sanar da hallaka fararen hula a ‘yan kasar bisa kuskure a lokacin da dakarun kasar ke kokarin maida martani ta sama da jiragen yaki daga wani harin ta’addanci da wasu mahara suka kai musu a yankin karamar hukumar Gothèye da ke cikin jihar Tillaberi
Ministan tsaron kasar ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar wacce a cikin ta ya ce lamarin ya faru ne a dare Juma’a wayewar Asabar din nan ta 6 ga watan Janairu
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta sanar da kama wata mata mai suna Bilkisu Sulaiman da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan ta’adda a jihar Katsina.
Kamar yadda sanarwar da ta fito daga kakakin hukumar na kasa Femi Baba Femi, ta ce an kama matar mai shekaru 28 na safarar makaman ne kan titin Zaria-Kano, inda take burin kai makaman a kauyen Kakumi na karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Hukumar ta ce an samu matar da harsasai 249 da aka kulle a cikin bakar leda aka saka cikin karamar jikkar hannu.
Femi ya ce bayan kama matar, an kai ta Ofishin ‘yan sanda na jihar Kaduna don karasa bincike a kanta.
Shekaru 61 da suka gabata aka haifi gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga Janairun 1963 a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano.
Engr Abba Kabir Yusuf ya halarci makarantar firamaren garin Sumaila da makarantar sakandaren Dawakin Tofa da kuma sakandaren Lautai dake Gumel din jihar Jigawa a halin yanzu kuma a can ne ya kammala karatun sakandare a shekarar 1980.
Gwamna Abba ya samu satifiket na diploma a Kwalejin Tarayya da ke Mubi jihar Adamawa a halin yanzu, sai ya yi babbar diploma wato HND a Kaduna Polytechnic.
Kwararren Injiniyan ya kuma kara fadada karatunsa a jami’ar Bayero da ke Kano a inda ya samu shaidar PGD.
Ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da kuri’u 1, 019, 602 Sai dai wannan nasara ta fara girgidi a hannunsa tun lokacin da kotun sauraren kararraki ta tsame kuri’u 165,000 da ce babu hatimin hukumar zabe a jikin su, lamarin da ya sanya kotun ayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara wanda da farko INEC ta ce ya samu kuri’u 890,705.
Duk da yawan mutanen da suka zabe shi, masu adawa da Engr. Abba Kabir Yusuf na zargin mutum ne wanda ba ya iya daukar hukunci na kashin kansa, wato dai kawia dan amshin shata ne ga mai gidan sa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
A yayin da masu goyon bayansa ke cewa hakan ba komai bane sai kwarewa a biyayya, kasancewar sa mutum mai cike da biyayya da kawaici tare da mutunta mutum ba tare da gadara da ake zargin wasu shugabanni da aikatawa ba.
A shekarar 1999 bayan an dawo dimokradiyya, Gwamnan jihar Kano a wancan lokacin Rabi’u Musa Kwankwaso ya nada Abba Gida-Gida mukamin hadimi na musamman wato PA ga Gwamna, Mukamin da Abba ya ci gaba da rikewa har bayan Kwankwason ya zama ministan tsaron Nijeriya a wa’adi na biyu na mulkin Obasanjo daga 2003-2007.
Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran darikar Kwankwasiyya ya nada Abba mulkin kwamishinan ayyuka na jihar Kano, a shekarar 2011 lokacin da ya dawo kan karaga a karo na biyu a matsayin Gwamna.
A shekarar 2018, jam’iyyar PDP ta tsayar da Abba a matsayin dan takarar Gwamnan Kano, Wanda suka Kara da Gwamna a wancan lokacin Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC bayan an raba gari tsakanin Kwankwaso da Ganduje. Sai dai zaben a karshe ya kare da Inconclusive, kuma bayan kamala shi ne hukumar zabe ta ayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.
Sai a shekarar 2022, Abba Kabir Yusuf ya bar PDP ya koma NNPP. Wannan ke-tare da watakila kuskuren da ya yi kamar yadda kotun daukaka kara ta bayyana na rashin karbar katin jam’iyyar NNPP a lokacin da ya sauya sheka na cikin dalilan da suka sanya ita kotun soke nasarar da Abba ya samu a matsayin gwamna.
Tun da farko dai ya yi fafatawa mai zafi da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a zaben na 2023.
A yanzu Abba Gida-Gida da magoya bayansa sun zura ido su ji hukuncin da kotun koli za ta yanke kan rusa nasararsa har sau biyu da lauyoyin jam’iyyar APC suka yi nasarar samu a kotuna biyu.
Abba, shi ne gwamna na 8 da aka zaba a jihar Kano tun daga shekara ta 1960 zuwa yanzu, Kafin shi zuwan Abba, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ne aka fara zaba a shekarar 1979 a jam’iyyar PRP, sai Alhaji Abdu Dawakin Tofasai kuma Alhaji Sabo Bakin Zuwo, dukkaninsu ‘yan jam’iyyar PRP. Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya take musu baya a jam’iyyar NRC. Daga nan sai Rabi’u Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da kuma Abdullahi Umar Ganduje.
Daga cikin jiga-jigan da suka taya Gwamna Abba murnar zagayowar ranar haihuwarsa harda shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya yi wa Abba fatan samun koshin lafiya da tsawon rai a duniyar nan. Sai kuma mai gidansa, wato, Dr Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya ce biyayya ta yi wa Abba Kabir rana musamman ganin yadda ya samu daukaka tun daga karamin dan siyasa har yanzu ga shi a matsayin gwamnan jihar Kano.
Hukumar kula da ayyukan ‘yan
sanda ta kasa ta ce mutane dubu 30 kachal zata dauka aiki, cikin sama da dubu
400 da suka nemi aikin a bana.
Ta cikin wata sanarwa da
shugaban hukumar Solomon Arase ya fitar ta ce sama da mutane dubu 400 ne suka
nemi aikin dan sanda cikin makonni 6 kachal da bayar da sanarwar.
Hukumar ta ce zata fara tantance
wadanda suka nemi aikin don tsamo wadanda suka chanchanta a gobe litinin 8 ga
watan da muke ciki na Janairu.
Arase wanda tsohon Supeton ‘yan
sanda ne ya ce ma’aikatan hukumar zasu zabi ma’aikata ne bisa chanchanta, don
haka ya gargadi masu yunkurin amfani da sanayya wajen samun aikin da su kuka da
kansu matukar aka kama su.
Kungiyar dillalan
man fetur ta IPMAN ta musanta labarin da ke cewa tana shirin kara farashin man
fetur.
Shugaban kungiyar
reshen jihar Enugu Mr Chinedu Anyaso ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa
da manema labarai, yana mai cewa akwai bukatar jama’a su yi watsi da wannan
labari.
Ya ce basu sami wani umarni ko shawarar kara
man fetur daga kamfanin mai na kasa NNPC ba don haka babu wani dalili da zai
sanya su kara farashin man fetur din a halin yanzu.
Bayanin nasa na zuwa ne dai-dai lokacin da jama’a
suka fara sayen man fetur da yawa don adanawa, saboda tsoron karin farashin man
kamar yadda ake yadawa.
Ya ce a maimakon kara farashin man yana da hasashen
cewa za’a sauke farashi ne idan har matatar mai ta dangote ta fara tace man da
ya kai ganga dubu 650 kowacce rana.
Yace
matatar man ta dangote da gyaran matatar mai ta Fatakwal zasu zamewa ‘yan Najeriya
rahama a fannin samun rangwamen tsadar farashin mai.
Hukumar kula da jami’o’I ta kasa ta lissafo jerin
wasu jami’o’in cikin gida mallakar gwamnati da masu zaman kansu da zata fara
bincike akan su sakamakon zargin su da bayar da shaidar kammala karatu ta bogi.
Duk dai wannan na zuwa ne bayan bankado asirin yadda
wasu ‘yan Najeriya ke samo shaidar kammala jami’a cikin wata guda.
Ma’aikatar ilimi ta ce binciken farko-farko da ta
gudanar ya gano yadda ake wannan badakala har a cikin gida, lamarin da ya sa
dole ta magance wannan matsala, saboda inganta makomar kasar.
Jami’o’in sun hadar da:
1. National University of Nigeria, Keffi, jihar
Nasarawa.
2. North Central University, Otukpo, jihar Benue.
3. Christ Alive Christian Seminary da jami’ar jihar Enugu.
3. Richmond Open University, Arochukwu, dake jihar
Abia.
4. West Coast University, Umuahia.
5. Saint Clements University, Iyin Ekiti, a jihar Ekiti.
6. Volta University College, Aba, jihar Abia.
Illegal Satellite Campuses of Ambrose Alli
University.
7. L. I.F.E Leadership University, Benin City, jihar Edo.