Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 473

Ba zamu amince da kasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba-NLC

0

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta mayarwa da shugaban kasar martani kan
alkawarin sa na sabuwar shekara game da shirin yiwa ma’aikatan kasar karin albashi.

Kungiyar karkashin jagorancin Joe Ajero ta ce babu wani dalili da zai sa
ta amince gwamnatin tarayya ta yi gaban kanta wajen Karin albashi, a wannan
karo ya zama wajibi a tattauna da su kafin karin albashin.

Shekarar 2018 ce shekara
ta karshe da gwamnatin tarayya ta tattauna da kungiyar kwadago kafin kara albashi.

Kungiyar ta ce gwamnati ta
jima tana yi mata dadin baki game da karin albashi, sai dai a wannan karon ya
zama wajibi ta dauki mataki, don shiga yarjejeniya da gwamnatin tarayya a watan
Afrilu mai zuwa.

Sai dai babban abinda ya
fi daukar hankali a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar shine, yadda ta ce ba
zata amince da kasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Al’ummar Najeriya sun fada
cikin halin masti tun bayan da gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur da
yadda darajar naira ke kara sulalewa, yayin da kayan masarufi ke kara tsada
dalili kenan da ya sa kungiyar kwadagon ke ganin bai kamata ma’aikata su rika
karbar kasa da naira dubu 200 a matsayin albashi ba.

 

 

Jirgin yakin soji a Nijar ya yi hatsari

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar ne janar Salifou Mody ya sanar da faduwar jirgin mai saukar angulu na dakarun kasar a yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga wani aikin sintirin hadin gwiwa da askarawan Burkina Faso
Sanarwar ministan ta ce da misalin karfe 12 na ranar Juma’ar nan ce 5 ga watan Janairu ne hatsarin jirgin ya auku sakamakon matsalar na’ura a daidai lokacin da yake shirin sauka a filin jirgin sojoji na Kantchari
Babu wanda ya rasa rai dai a wannan hatsari amma sai karamin rauni da mutum daya ya samu kamar yadda sanarwar ta ambato

Matakin gwamnati kan digiri ‘dan Kwatano’ ya shafi daliban Nijeriya 15,000

0

Ƙungiyar ɗaliban Najeriya (NANS) a jamhuriyar Benin ta bayyana cewa sama da dalibai 15,000 ne suka shiga halin kaka-ni-kayi, sakamakon haramta wasu jami’o’i da gwamnatin Nijeriya ta yi a kasar.

Shugaban ƙungiyar a Jamhuriyar Benin, Ugochukwu Favor, ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels.

A yayin tattaunawa Favor ya yi kira da a sassauta wannan mataki musamman a kasashe Benin da Togo.

Hakan dai na zuwa ne bayan da wani ɗan jarida mai binciken kwakwaf ya fallasa yadda ake samun takardar shaidar kammala makarantun a kasashen.

Shugaban kungiyar daliban ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi bincike mai zurfi don gano wadanda ke da hannu a badakalar kuma a hukunta su.

Ministan tsaro Matawalle ya gabatar da jiragen ruwa marasa matuki ga Tinubu

 

Ministan kasa a Ma’ikatar Tsaron Nijeriya Mohammed Bello Matawalle, ya gabatar ma Shugaban kasa Bola Tinubu jiragen ruwa marasa matuki guda biyu a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai Henshaw Ogubike ya fitar a Abuja.

Sanarwar ta ce Ministan ya shaida wa shugaban kasa cewa, Jiragen biyu za su taimaka wajen yaki da ta’addanci a bakin gabar ruwa.

Matawalle ya sanar da Tinubu cewa wadannan jirage na da nufin inganta sabbin fasahohin da za su kara wa sojojin Najeriya kwarin gwiwa wajen tunkarar kalubalen tsaro.

EFCC ta kai samame a ofishin Dangote

0
Jami’an hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC sun kai wani samame a babban ofishin kamfanin Dangote a jihar Legas.
Jaridar Premium Times ta ruwaito, jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan canjin kudin da aka ware wa kamfanin a zamanin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele.
Jami’an na EFCC sun bukaci takardun da ke dauke da bayanan kudaden ketare da bankin CBN ya ba kamfanin a cikin shekaru goma da suka gabata.
Idan dai baku manta ba a watan Disamba na shekarar da ta gabata wani mai binciken kwakwaf ya bankado wasu asusun banki guda 593 da ke a kasashen waje.

Hisbah na fatar takaita barace-barace a Katsina

Hukumar Hisba a jihar Katsina ta ja kunnen iyaye akan su kula da yaransu, kuma su ja kunnensu kafin su fara kai samame a gidajen baɗala a jihar.

Kwamandan hukumar Sheikh Aminu Usman Abu-Ammar ne ya faɗi hakan a cikin wani faifan bidiyo yana mai cewa duk mahaifin da ya san ɗansa yana tattara daba a cikin unguwanni, to su kuka da kansu.

Abu-ammar ya ce duk ɗan da ya kuskura ko mahaifin da ya sake ya shigo hannun hukumar zai fuskanci fushin hukuma.

“Zamu shiga lungu da sako domin mu tsawatar, ayi dai-dai”

“Aikin hukumar Hisba ne umarnin da kyakkyawa da kuma hani da mummuna, wannan shi ne jigon aikin hukumar’

Ya kara da cewa “Manufar hukumar shi ne a taimake ka ɗan ka ya zama ingantacce, saboda nauyi ne na hukuma ta yi aikin da za ta inganta al’ummar da take jagoranta.”

Kwamandan ya kara da cewa hukumar za ta yi kokari wajen taƙaita barace-batace a bisa titunan jihar.

‘Yan ta’adda sun bude wuta kan motoci sama da 20 a Katsina, sun kashe mutane akalla 6

‘Yan ta’adda sun bude wuta kan motoci sama da 20 a Katsina, sun kashe mutane akalla 6
‘Yan ta’adda sun bude wuta kan motocin da suka fito daga garin Mai Dabino zuwa ‘Yantumaki a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’ar nan, a daidai lokacin da mutanen suka baro garin Mai Dabino kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a Yantumaki.
Majiyar ta sanar cewa dama duk mako sai sun yi ayari sannan jami’an tsaro su raka su zuwa cin kasuwa a garin ‘Yantumaki da kasuwar ke ci duk Juma’a.
Wani direban mota da DCL Hausa ta zanta da shi ya shaida cewa an kona wasu daga cikin motocin da suke tafe da su. Sannan mafiyawan wadanda suka tagayyara ta dalilin bude wutar su ne mata da kananan yara.
Direban ya sanar cewa akwai ma wani babban soja daga cikin wadanda suka rako su da ya samu harbin bindiga har an garzaya da shi asibiti.

Kamfanin da ke aikin titin Abuja-Kano na son karin kudi N1.35tn, inji Minista

0

 

Hanya

Ministan ayyuka a Nijeriya Sen. David Umahi, ya ce kamfanin Julius Berger na neman karin Naira Tiriliyan N1.35tr domin kammala aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano.

Ministan ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manyan Daraktocin ma’aikatar ayyukan jawabi a ranar Alhamis. 

Aikin dai na daya daga cikin ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu ta gada daga tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari.

An kai kudirin neman majalisa ta amince ‘yan Nijeriya su rika kare kansu daga ta’addanci

0
Majalisa

Majalisar dattawan Nijeriya za ta tattauna kan kudirin da zai ba ‘yan kasa damar mallakar makamai domin kare kansu.

Jaridar Leadership ta ruwaito sanata mai wakiltar Delta ta Arewa a majalisar Prince Ned Nwoko ne ya gabatar da kudirin dokar, domin yin gyara a dokar da ake da ita ta mallakar makami ga farar hula.

Ya kara da cewa barazanar tsaro da ‘yan kasa ke fuskanta ya sa mutane da yawa cikin halin kunci da rashin kwanciyar hankali inda ya kara da cewa kudirin nasa zai baiwa fararen hula damar mallakar makamai da za su kare kansu.

Daga karshe Sanatan ya yi fatar abokan aikin nasa za su goyi bayan kudirin.

Sadiya Umar Faruq ta fadi dalilin da ya sa ba ta je ofishin EFCC ba

Tsohuwar ministar jin kai a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, Sadiya Umar Faruq ta ce rashin lafiya ne babban dalilin da ya hana ta girmama gayyatar hukumar EFCC.
Punch ta rawaito cewa, Sadiya Umar Faruq ta rubuta wa EFCC a hukumance neman alfarmar a kara mata wa’adi kan gayyatar da hukumar ke yi mata.
Ana dai tuhumar Sadiya Umar Faruq kan wasu kudi da suka kai Naira bilyan 37 da ake zargin sun yi batan-dabo a ma’aikatar a lokacin da take matsayin minista hadin baki da wani dan kwangila mai suna James Okwete.
Jaridu dai sun buga labarin cewa jami’an EFCC na can na neman takardar iznin kamo tsohuwar ministar Sadiya Umar Faruq tun da ta ki mutunta gayyatarsu.