Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 475

Tinubu zai kashe N100bn don ciyar da ‘yan makaranta

0
Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 100 domin ciyar da makarantu, a cikin kasafin kudin shekarar 2024.

Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake rattaba hannu a kan kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ya ce tanadin zai kara karfafa yan makaranta su cigaba da halartar makarantun su da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

“Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin kudirin dokar da aka amince da su kwanan nan shi ne ware Naira biliyan 100 don ciyar da yara ‘yan makaranta. Na yi imanin wannan zai zama abin ƙarfafawa ga shiga makarantu da kuma taimakawa wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ɗalibai.

‘Yan sanda sun kama barayin motoci a Zariya

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane uku da ake zargin barayin mota ne tare da kwato wasu motoci da aka sace a Zariya. 
Bayanin hakna na kunshe a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya raba wa manema labarai.
Sanarwa ta ce jami’an rundunar ‘yan sandan birnin Zariya ne suka yi wannan nasara bayan da suka yi aiki da sahihan bayanai suka kama barayin da ake zargi a Agoro da ke Tudun Wada Zaria.

Lantarkin Nijeriya za ta kara inganta a shekarar 2024 – Minista

 

Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin ma’aikatarsa na ba da fifiko ga samar da wutar lantarki a kasar a cikin shekarar 2024.

Ya ce hakan ya yi dai-dai da tsarin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na sauya wutar lantarki a sakonsa na sabuwar shekara.

Mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, Mista Bolaji Tunji, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja jiya Litinin.

Yace “Saboda fahimtar muhimmiyar rawar da wutar lantarki ke takawa wajen bunkasar tattalin arziki, watanni ukun farko da na hau ofis na mayar da hankali kan bincike, tuntubar masu ruwa da tsaki, da kuma tsara dabaru.

“Tare da ingantaccen tsarin aiwatarwa, yanzu lokaci ya yi da za a ɗauki kwakkwaran mataki.

“Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shine haɓakawa da rarrabawa da kayan aikin watsawa don rage asarar da ake samu ta kasuwanci” in ji shi.

Lantarkin Nijeriya za ta kara inganta a shekarar 2024 – Minista

Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin ma’aikatarsa na ba da fifiko ga samar da wutar lantarki a kasar a cikin shekarar 2024.
Ya ce hakan ya yi dai-dai da tsarin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na sauya wutar lantarki a sakonsa na sabuwar shekara.
Mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, Mista Bolaji Tunji, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja jiya Litinin.
Yace “Saboda fahimtar muhimmiyar rawar da wutar lantarki ke takawa wajen bunkasar tattalin arziki, watanni ukun farko da na hau ofis na mayar da hankali kan bincike, tuntubar masu ruwa da tsaki, da kuma tsara dabaru.
“Tare da ingantaccen tsarin aiwatarwa, yanzu lokaci ya yi da za a ɗauki kwakkwaran mataki.
“Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shine haɓakawa da rarrabawa da kayan aikin watsawa don rage asarar da ake samu ta kasuwanci” in ji shi.

Sanata Ike Ikweremadu ya share watanni 9 cikin daurin shekaru 9 da kotu ta yi masa a Ingila

A cikin watan Mayun shekarar 2023 ne dai wata kotu a kasar Ingila ta yanke hukuncin daurin shekaru 9 ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Ike Ikweremadu.
Kotun dai ta kuma yanke wa mai dakin Sanata Ike da karin wani mutum daya hukunci duk bayan an same su da laifin safarar wani matashi don harkallar kodar da za a sanya wa diyarsu.
Sanata Ike Ikweremadu mai shekaru 60 da matarsa Beatrice mai shekaru 56, sun dade suna fafutukar yadda za su samar wa diyarsu Sonia mai shekaru 25 koda.
Kotun ta same su da laifin safarar sassan jikin bil’adama.
Beatrice, matar Ikweremadu ta samu hukuncin daurin shekaru 4 a yayin da mutumin da zai ba da kodar aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10.
Sanata Ike Ikweremadu dai da ya fito daga jihar Enugu, ya fara zuwa majalisar dattawan Nijeriya daga shekarar 2003. Dan jam’iyyar PDP, Ike ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya sau uku a jere a majalisa ta 6,7 da 8.

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin bana

0

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin bana jim kadan bayan komawar
sa Abuja daga jihar Lagos inda ya gudanar da hutun kirismeti.


Ko da yake jawabi jim
kadan bayan rattaba hannu kan kasafin kudin, shugaba Tinubu ya tabbatarwa da ‘yan
Najeriya cewa ba za’a ja kafa ba wajen fara aikwatar da kasafin kudin.

Ya kuma baiwa
dukannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati umarnin fara shirin amfani da kasafin
kudin na bana ba tare da bata lokaci ba.

Manyan bangarorin da ke gaba a kasafin kudin na bana
sun hadar da Tsaro, samar da ayyukan yi, inganta tattalin arziki, alkinta
muhalli, gina dan adam, da kuma yaki da talauci.

Kasafin kudin na bana ya kama Naira Triliyan 28.7

 

 

 

Dan majalisa a Kano ya dauki nauyin yi wa yara kanana kaciya

Dan majalisar wakilai da daga karamar hukumar Fagge a jihar Kano Mohammed Bello Shehu ya dauki nauyin yi wa yara kanana kaciya a mazabar da yake wakilta.
Wannan yunkuri dai ya sa masu ruwa da tsaki na yankin Fagge da kewaye a jihar ta Kano suka sa kafa suka shure, su na ganin cewa kamar ba wannan al’umma ke bukata ba.
A al’adance dai, al’ummar Hausawa na yi wa ‘ya’yansu kaciya a zamanin sanyi.
Dan majalisar da yake a jam’iyyar NNPP ya bugi kirjin daukar nauyin yara sama da 1,000 da za a yi musu kaciya a mazabu 11 da yake wakilta.
Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa har ma an kaddamar da wannan aiki a ranar Asabar a cibiyar kiwon lafiya ta Ofishin Galadima da ke mazabar Fagge B.
Wannan lamari dai ya sa ana ta ce-ce-kuce har wasu na ganin kamar dan majalisar ba zai iya cika alkawarin da ya dauka ba a zamanin yakin neman zabe.

Har yanzu ba’a fara bamu albashin watanni hudu da gwamnati ta rike mana ba-ASUU

0

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta ce har yanzu ba a
fara sakin Albashin watanni 4 da shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci a biya su.

Kimanin watanni biyu cif-cif tun bayan da
shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da a saki albashin watanni
hudu da aka hana malaman jami’o’in Nijeriya sakamaon yajin aikin da suka
tsunduma, kungiyar malaman jami’o’i ta (ASUU) ta ce har yanzu mambobinta ba su
karbi albashin ba.

Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce har
yanzu gwamnati ba ta  aiwatar da mafi
yawan bukatun da suka yi jarjejeniyar za a biya wa ya’yanta.

Wannan na zuwa ne bayan da yan kungiyar ta ASUU suka rika
korafi kan yadda kudaden tafiyar da majalisun dokokin kasar biyu ya zarta wanda
aka ware musu cikin kasafin kudin bana.

 

Kungiyar matan ‘yan sanda ta rabawa zawarawa awaki kusan 150 don inganta rayuwar su

0

Kungiyar
matan jami’an ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta raba awaki 137 ga
matan da mazajensu suka mutu da kuma marasa galihu, domin bunkasa rayuwarsu

Hakan
dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan
sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano.

Shugabar ƙungiyar
Aisha Gumel wacce kuma ita ce uwargidan kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta ce
matakin wani aiki ne na yau da kullun na tallafawa iyalan ma’aikatan da suka
mutu da waɗanda sukai ritaya da sauran marasa galihu a cikin al’umma.

Aisha
ta gabatar da takardar shaidar koyon sana’o’i ga ‘yan kungiyar sama da 100 da
suka samu horo tare da daukar nauyin fara sana’o’i daban-daban daga kungiyar.

 

Gwamnatin Filato ta ware kwanaki 7 don alhinin mutanen da ‘yan bindiga suka kashe

0

Gwamnan jihar Fulato
Celeb Mutfwang ya ayyana kwanaki 7 a matsayin ranakun da za’a gudanar da
alhinin mutanen da suka mutu sama da 150 a sakamakon wani mummunan hari da wasu
mutane suka kai musu.

Yayin jawabinsa na Sabuwar
shekara, gwamnan yace za’a fara wannan alhini ne daga ranar 1-7 ga watan Janairun
da muke ciki.

Bayan wannan sanarwa gwamnan ya kuma yiwa wasu daurarrun gidan
yari uku afuwa ta hanyar rage musu yawan shekaru da aka yanke musu, ciki har da
wani Musa Danladi da aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Ya ce ba shakka jihar ta karkare shekarar 2023 cikin tsananin
bakinciki da alhini, don haka wadannan mutane sun chanchanci a ware ranakun don
karrama su.

A tsakanin watan
Aprilu zuwa Yuni masu dauke da makamai sun kashe mutane sama da 400 a jihar
kadai, sai dai na baya-bayan nan shine mafi muni.

Bayanai sun nuna cewa ranar 24 ga watan Disamban da ya gabata ‘yan
bindiga sun kai hari kauyukan Ndun, Ngyong, Murfet, Makundary, Tamiso, Chiang,
Tahore, Gawarba, Dares, Meyenga, Darwat, and Butura Kampani duk a kananan
hukumomin, Barkin Ladi da Bokkos.