Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 476

Ƙungiyar matan ‘yan sanda sun raba awaki ga zawarawa a Kano

Kungiyar matan jami’an ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta raba awaki 137 ga matan da mazajensu suka mutu da kuma marasa galihu a jiya Lahadi, domin bunkasa rayuwarsu
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano.
Shugabar ƙungiyar Aisha Gumel wacce kuma ita ce uwargidan kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta ce matakin wani aiki ne na yau da kullun na tallafawa iyalan ma’aikatan da suka mutu da waɗanda sukai ritaya da sauran marasa galihu a cikin al’umma.
Aisha ta gabatar da takardar shaidar koyon sana’o’i ga ‘yan kungiyar sama da 100 da suka samu horo tare da daukar nauyin fara sana’o’i daban-daban daga kungiyar.

Gwamnatinmu ta dauki hanyar kawo karshen matsalar tsaro- Bola Tinubu

0

 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da cewa gwamnatin sa ta
taka rawar gani wajen takaita matsalolin tsaro duk kuwa da hare-haren da ake ci
gaba da kaiwa sassan kasar.

Shugaba Tinubu na
wadannan kalamai ne kasa da makkonni biyu bayan da yan bindiga suka kai wani
mummunan hari jihar Plateau da ke tsakiyar kasar.

Yayin jawabin sa na
sabuwar shekara, Shugaban kasa yace tun bayan da ya karbi office gwamnatin ta
yi iya bakin kokarin ta wajen ganin irin saukin da aka samu a sassan kasar da
hare-hare suka yi kamari.

Tinubu ya ce
hare-hare da ake samu nan da can shine dalilin da ya sa gwamnatin ba zata yi
ikirarin kakkabe ta’addanci kai tsaye ba, amma tabbas an sami ci gaba.

Inganta fannin tsaro na cikin manyan
manufofin shugaban kasar takwas da ya sha alwashin ganin ya sharewa ‘yan
Najeriya hawayen su a kai.

Manufofin
shugaban 8 sun hadar da tabbatar da tsaron kan iyakoki, tsaron cikin gida,
samar da ayyukan yi, habbaka tattalin arziki, gina dan adam, alkinta muhalli
yaki da talauci da tsare hakkin al’umma.

An jarabtu da tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya a shekarar 2023, inji Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce shekarar 2023 ita ce shekarar da ta jawo wahala da tashin hankali a fadin kasashe.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bayyana hakan a wani sako na bidiyo da aka fitar a jajibirin shekarar 2024.
A cewarsa “bil’adama na cikin zafi. Duniyarmu tana cikin babban matsala. 2023 ita ce shekarar da ta fi zafi a tarihi. mutane na mutuwa ta hanyar karuwar talauci da yunwa. Yaƙe-yaƙe da tashin hankali suna ƙaruwa da yawa Kuma amana ta yi karanci.
“Amma nuna wa juna yatsa da zuwa yaƙe-yaƙe ba za su kawo mafita ba”.
Gutteres ya yi kira da a hada kai cikin gaggawa da kuma hada karfi domin shawo kan kalubalen da ke gabansu. “Dole ne 2024 ta zama shekarar gina amana da maido da zaman lafiya.
“Dole ne mu hada gwiwa domin kawo mafitar wannan rigimar.
“Tare, zamu tashi tsaye wajen yakar wariya da kiyayya da ke haifar da guba game da dangantakar dake tsakanin kasashe da al’ummomi.
“Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da hada kan duniya don samar da zaman lafiya, ci gaba mai dorewa da kare hakkin dan Adam.
“Mu tabbatar da cewa shekarar 2024 ta zama shekarar gina amana kuma muna fatan zaman lafiya.
A halin yanzu, Guterres ya bayyana damuwarsa kan karuwar talauci da yunwa. Yana mai bayyana wadannan kalubalen da ke ci gaba da zama barazana ga rayuwar jama’a a duniya.

Ran majalisar dinkin duniya ya baci kan kisan mutane 190 a Plateau

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna bacin ran ta game da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan jihar Filato a karshen shekarar nan. 
Shugaban kula da hakkin bil adama a majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya sanar da haka ne a wani jawabi da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.
Mista Volker Turk ya nuna akwai matukar bukatar ayi gaggawar kawo karshen wannan kashe-kashen.
A cewarsa “Ina mai matukar damuwa da jeringiyar hare-haren ‘yan bindiga a kauyuka da-dama da ke jihar Filato.” 
“Ina kira ga hukumomin Najeriya su binciki wannan lamari da wuri kuma da kyau, bisa doron dokokin kare hakkin Bil Adama, kuma ayi adalci wajen hukunta wadanda aka samu da laifi a kotu.”
 “Dole a gaggauta kawo karshen wannan zalunci da yake yawon aukuwa. Sannan gwamnati ta dauki matakan kwarai wajen shawo kan asalin matsalolin tare da tabbatar da rikicin ba zai sake faruwa ba.” In ji Mista Turk. 
A halin yanzu, MDD ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hana sake faruwar irin wannan ta’adi.

Shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun maka Abba Gida-gida a kotu

Shuwagabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun maka gwamnatin jihar kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan matakin da ta dauka na gina sabbin gadojin sama guda biyu a Tal’udu da Danagundi duk a cikin birni.
Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da kashi 70 cikin 100 na kudaden kananan hukumomi domin gina wadannan sabbin gadoji.
Sai dai Gwamnan a yayin da yake aza harsashin ginin gadar sama da maraicen Juma’a ya yi magana kan hanyoyin samar da kudaden ayyukan inda ya ce al’ada ce da ta faro tun daga magabata na samar da irin wadannan manyan ayyuka ta hanyar yin amfani da asusun hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke gudanarwa.

Bankin Duniya ya sake hasashen samun karuwar ayyukan ta’addanci da matsin tattalin arziki a Katsina da Kaduna

Bankin Duniya ya sake hasashen cewa za a cigaba da samun karuwar ayyukan ta’addanci da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a wasu kananan jihohi 6 na Nijeriya.
Jihohin kamar yadda hasashen bankin duniyar ya nuna su ne na Katsina, Borno, Sokoto, Yobe, Kaduna da Zamfara kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Hasashen na bankin duniya ya ta’allaka ne kan yadda mafiyawan alummomin wadannan yankuna ke gaza zuwa gonakinsu don gudanar da harkokin noma.
Rahoton bankin ya ce kasashen Nijeriya, Chad, Nijar da Mali ne wadannan matsaloli za su iya shafa.

Mutane 70 ke takarar shugabancin Senegal a zaben 2024

‘Yan takara 70 ne za su fafata a neman hawa kujerar shugabancin kasar Sénégal a zaben shekara mai kamawa ta 2024.
Daga ciki ‘yan takarar hada fitaccen madugun ‘yan adawar nan na kasar Ousmane Sonko.
Kudi milyan 30 ne na CFA ne kowane dan takara zai zuba a matsayin kudin tsayawa takarar.
Ya jerin sunayen wadanda suke takarar.
1. Amadou Ba
2. 2. Papa Eugène Barbier
3. Boubacar Camara
4. Ibrahima Cissokho
5. Ada Coundoul
6. Bougane Gueye Dany
7. Hamidou Dème
8. Mamadou Lamine Diallo
9. Mame Boye Diao
10. Aminata Assome Diatta
11. Cheikh Dieng
12. Cheikh Bamba DIEYE
13. Cheikh Tidiane Dièye
14. Mamadou Dièye
15. Boun Abdallah Dionne
16. Babacar Diop
17. Mouhamed Ben Diop
18. Moussa Diop
19. Mamadou Diop Decroix
20. Abdourahmane Diouf
21. Elhadj Diouf
22. Jean Batiste Diouf
23. Dethié Fall
24. Pape Djibril Fall
25. Adama Faye
26. Bassirou Diomaye Faye
27. Cheikh Tidiane Gadio
28. Malick Gakou
29. Malick Gueye
30. Assane Kâ
31. Amadou Aly Kane
32. Mouhamadou Madana Kane
33. Mouhamadou Fadilou Koné
34. Ndiack Lakh
35. Amadou Ly « Akilé »
36. Aliou Mamadou Dia
37. Birima Mangara
38. Bara Doly Mbacké
39. Abdoul Mbaye
40. Aida Mbodj
41. Serigne Mboup
42. Momar Ndao
43. Aly Ngouille Ndiaye
44. Babacar Ndiaye
45. Daouda Ndiaye
46. Samba Ndiaye
47. Souleymane Ndéné Ndiaye
48. Anta Babacar Ngom
49. Mary Teuw Niane
50. Al Hassane Niang
51. Thione Niang
52. Abdou Khadre Sall
53. Ibrahima Sall
54. Khalifa Ababacar Sall
55. Thierno Alassane Sall
56. Alioune Sarr
57. Amadou Seck
58. Idrissa Seck
59. Amsatou Sow Sidibé
60. Ousmane Sonko
61. Haguibou Soumaré
62. Habib Sy
63. Abdoulaye Sylla
64. Alpha Thiam
65. Hamidou Thiaw
66. Abdoulaye Tine
67. Aminata Touré
68. Karim Wade
69. Rose Wardini
70. Mamadou Yatassaye

Kasar Bénin ta sanar da dage matakin daina karbar hajojin Nijar a tashar jirgin ruwan ta

A cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun babban daraktan tashar jirgin ruwan Cotonou Bart Jozef Johan VAN EENDO kasar Benin ta sanar da dage matakin nata na daina karbar hajojin Nijar a tashar tata
Kasar ta Bénin dai ta dauki matakin dakatar da karbar hajojin na ‘yan Nijar a tashar ruwan tata tun a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata
Wannan mataki na hukumomin Bénin din na zuwa ne ‘yan kwana kadan bayan da aka jiyo shugaba Patrice Talon yana bukatar kawo karshen tsamin dangantakar daga tsakanin kasar tasa da kasashen da ke karkashin mulkin soja da ke cikin yankin kungiyar ECOWAS

Ban taba sani ko jin sunan dan kwangilar da ake alakantawa da ni ba kan badakalar kudi – Sadiya Umar Faruq

Tsohuwar ministar jin kai a Nijeriya Sadiya Umar Faruq, ta nesanta kanta daga wasu rahotanni da ke alakanta ta da wani dan kwangila James Okwete da aka ce ya yi zargin tana da hannu a wata badakalar kudi a ma’aikatar jin kai ta Nijeriya.
Sadiya Umar Faruq a cikin wata sanarwa da ta wallafa a sahihin shafinta na Facebook, ta ce kwata-kwata ba ta ma san mai wannan sunan ba, bare ma a ce wata alaka ta taba hada su.
Jaridar Punch ta rawaito cewa akwai wani dan kwangila mai suna James Okwete da hukumar EFCC ta kama, yake ba ta bahasin cewa tsohuwar ministar Sadiya na da hannu a wata badakalar kudi Naira bilyan 37 tare da wasu daraktocin da suka yi aiki a ma’aikatar a lokacin tana minista.
Har ma hukumar ta ce da yiwuwar a kama ita tsohuwar ministar da wadancan daraktoci da wannan dan kwangila ya ayyana.
A cikin sanarwar Sadiya Umar Faruq,vta ce har yanzu tana mai matukar farinciki da bugun kirjin yadda ta yi aikinta na minista cikin tsanaki da tsafta ta hidimta wa kasar ta ba tare da wani son rai ya shigo ba.
Ta ce ta tuntubi tawagar lauyoyinta don bullo ma lamarin ta hanyar da ta dace.

EFCC ta kama dan kwangilar ma’aikatar jin kai da Sadiya Umar Faruq ta jagoranta

Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce ta kama dan kwangila James Okwete da hakan ke da nasaba da zargin wata badakalar kudi Naira bilyan 37 da ake zargin ministar jin kai a zamanin mulkin Buhari, Sadiya Umar Faruq.
Wani babban jami’in hukumar EFCC da ya sanar da jaridar Punch, ya ce dan kwangilar ya yi bayani gamsasshe a kan tsohuwar ministar da ma wasu tsoffin daraktoci a ma’aikatar.
Wannan batu dai ya zo daidai da lokacin da ake binciken wasu ministocin gwamnatin Buhari guda uku kan zargin wata badakalar kudin da aka kiyasta sun kai Naira milyan 150.
Majiyar daga hukumar EFCC ta ce da yiwuwar a kama Sadiya da sauran daraktocin da suka yi aiki a zamanin tana minista.
Yanzu haka dai bayanai sun ce ana tsare da dan kwangila Okwete a hedikwatar hukumar EFCC da ke Jabi, Abuja.