Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 477

Ba Faransa ce ke ingiza ECOWAS daukar matakai kan Nijar ba – Ministan Tinubu

Ministan harkokin kasashen waje na Nijeriya Amb Yusuf Tuggar ya sanar cewa babu kanshin gaskiya a zargin da wasu ke yi cewa kasar Faransa ce ke ingiza kungiyar ECOWAS ta dauki matakan kakaba takunkumai ga kasar Nijar tun bayan juyin mulkin soji.
Kungiyar ECOWAS sai ta sanya wasu takunkumai ga kasar Nijar tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed a farko-farkon wannan shekara.
Daga cikin takunkuman akwai na rufe kan iyakar Nijeriya da Nijar da yanke wutar lantarki da katse huldar jakadanci da sauransu.
Ministan ya yi wannan furucin ne a wata zantawa da gidan talabijin na Trust Tv.

‘Yan majalisa sun kori kwamishinan kasafin kudin daga zauren majalisar dokokin jihar Zamfara

‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun bukaci da kwamishinan kudi na jihar Abdulmalik Gajam da ya fita daga zauren majalisar a lokacin da Gwamna Dauda ya gabatar musu da daftarin kasafin kudin 2024.
‘Yan majalisar dai sun ce sun dauki wannan matakin ne biyo bayan kin mutunta gayyatar majalisar da suka ce kwamishinan ya yi, na ya je gabansu don kare kasafin kudin shekarar 2024.
Bayan tattaunawa, majalisar ta amince cewa takardar tabbatarwar da ta ba kwamishinan tun da farko, ta janye.
Kamar yadda suka ce, sun gayyaci kwamishinan sau uku don ya je majalisar ya kare kasafin kudin shekarar 2024 na ma’aikatarsa, amma ya ki zuwa, kuma bai bayar da wata hujja mai kwari ba.
Bayan kammala bayyana wadannan dalilai na su, ‘yan majalisar sun bukaci kwamishinan da ya fita daga zauren majalisar.

Kotu ta haramta wa minista a gwamnatin Buhari rike duk wani mukamin gwamnati

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta dakatar da tsohuwar ministar harkokin mata a gwamnatin Buhari, Ms Pauline Tallen da karbar duk wani mukamin da ya danganci gwamnati.
A cikin hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta nuna rashin jin dadinta kan kalaman Pauline Tallen bayan da aka yanke hukuncin da ya danganci jihar Adamawa a shekarar bara.
A baran dai ne kotun ta yanke hukuncin cewa Aisha Binani ta APC ba ta cancanci tsayawa takarar Gwamna ba.
Daga cikin kalaman Pauline Tallen a wancan lokacin, ta ce wannan hukuncin kotu ya yi kama da hukuncin kama-karya.
Shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Yakubu MaiKyau a lokacin ya nemi Pauline Tallen da ta nemi afuwar ta kuma janye kalamanta, idan ba haka ba, zai maka ta kotu, amma ta kiya, dalilin da ya sa hakan ya kai su kotu.

Katsina da Yobe ne jihohin da ba su iya rayuwa idan babu kudin FAAC na FG – Rahoto

Rahoton shekara-shekara na karfin hanyoyin samar da kudaden shiga na jihohi a Nijeriya ya nuna cewa akwai jihohin da idan babu daunin gwamnatin tarayya, ba za su iya tsayawa da kafafunsu ba.
Jihohin kamar yadda rahoton ya ce su ne Katsina, Kebbi, Bayelsa, Akwa Ibom, Taraba da Yobe.
Rahoton da aka fitar a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ya nuna cewa jihohin 6 sun gaza samar da kaso 10% na kudaden shiga daga cikin gida IGR a shekarar 2022.
Kudaden shigar jihohi 36 na Nijeriya a shekarar 2022 sun kai Naira Tiriliyan 1.8, inda suka zarta na shekarar 2021 da aka samu Naira Tiriliyan 1.7.
Jihar Lagos dau ce kan gaba wajen tattara kudaden shiga a cikin gida da Naira bilyan 651 sai jihar Ogun ta biyu sai jihar Rivers ta uku.

An damfari ‘yan Nijeriya sama da 1,000 da sunan za a ba su aiki a Ingila – IOM

Hukumar da ke kula da masu gudun hijira ta majalisar dinkin duniya IOM ta ce akwai ‘yan Nijeriya sama da dubu daya da aka damfara da sunan za a samar musu aiki a kasar Ingila.
Babban jami’in hukumar a Nijeriya Laurent De Boeck ya sanar da hakan a Abuja a lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Mr Boeck ya ce kusan kowanensu ya yi asarar kudin da suka kai darajar Dala dubu 10,000 ta dalilin neman aikin, amma ba a yi kwado da yaro ba kuma ba a bashi gayansa ba.
Mr Laurent ya ce idan suka je ma’aikatun suka gabatar da takardun kama aikin da aka damfare su aka ba su, sai ma’aikatun su ce wannan takarda ba daga gare su take ba.
Ya ce da yawansu suna can sun yi tsuru-tsuru a Ingila ba su da kudin komowa Nijeriya, a yayin da wasu kuma ke kunyar dawowa su tunkari iyalansu.

An sake zaben Abdel-fatah Al-sisi a matsayin shugaban kasar Egypt karo na uku

Hukumar zaben kasar Masar ta sanar cewa shugaba Abdel-fatah Al-sisi ya sake yin nasara karo na uku bayan zaben da aka gudanar makon jiya.
Al-sisi ya zamo shugaban kasar Masar a shekarar 2014, aka sake zabensa a shekarar 2018, sai yanzu da zai ci gaba da jagorantar kasar har zuwa 2029 da kundin mulkin kasar ya ce nan ne magaryar tukewa.
Hukumar zaben dai ta ce Abdel-fatah Al-sisi ya lashe zaben ne da kaso 90% na yawan kuri’un da aka kada.

JAMB ta kara farashin kudin rajista

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta Nijeriya JAMB ta sanar da kara kudin rajistar jarabawar da za a zauna a shekarar 2024.
A cikin wata sanarwa daga hukumar, ta ce yanzu za a rika biyan kudin rajistar Naira dubu 7,700 da kuma Naira 6,200 kudin neman share fagen zauna jarabawar ta Mock.
Kafin wannan karin dai, ana sayar da fom din JAMB kan kudi Naira5,700, sai take kamawa 6,700 hada jarabawar Mock.
Hukumar ta ce daliban kasashen ketare da ke da aniyar zuwa Nijeriya su zauna jarabawar za su sayi fom din Dala 30.

An gano manyan dalilan da suka sanya albasa ta yi tsada a wasu jihohin Nijeriya

Jaridar Daily Trust ta gano cewa yawan amfani da ake da albasar da karancin da ta yi a kasuwanni ne ya sa albasar ta yi tsada.
Binciken ya gano cewa ana sayar da buhun albasar kan kudi Naira dubu 120,000. Sai dai bincike ya gano cewa farashin ya fara sauka bayan da aka fara shigo da ‘yar waje daga Gada ta Jamhuriyar Nijar.

Yunkurin ofishin Mai Ba Shugaban kasa Shawara kan harkokin tsaro ne ya sa aka sako daliban jami’ar FUDMA – VC

An sako dalibai mata na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsinma kwanaki 74 bayan sace su da ‘yan bindiga suka yi.

An dai sace daliban su biyar ne a ranar 03 ga watan Oktoba, 2023. Sai dai daya daga cikinsu ta kubuta kwanaki kadan bayan sace su.
Shugaban jami’ar Prof Armaya’u Hamisu Bichi ya ce tabbatar ko an biya kudin fansa ko a’a, kawai dai ya ce yunkuri da kokarin Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro NSA Malam Nuhu Ribadu ne ya sa aka sako daliban.

An sallami daraktoci 33 daga aiki a ma’aikatar sufurin sama

Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo ya kori daraktoci 33 da ke aiki a karkashin ma’aikatar da yake jagoranta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito karkashin ma’aikatar sufurin jiragen sama mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Odutayo Oluseyi da ya fita a ranar Alhamis. 
Korar na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da shugaban kasa, Bola Tinubu ya kori Manajan Daraktan FAAN, Kabir Mohammed; NAMA, Toyib Odunowo; Babban Daraktan NiMet, Farfesa Mansur Matazu; Babban Daraktan Hukumar NSIB, Engr. Akin Olateru da kuma dakatar da babban darakta na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu.
Sanarwar ta kara da cewa an yi korar ne domin a kara inganta ma’aikatar ta yadda za a rika gudanar da aiki a cikin tsari mai tsafta.