Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 478

An fara rusa ginin majalisar dokokin jihar Rivers

Rikicin siyasa ya sa yanzu haka an rusa ginin majalisar dokokin jihar Rivers.
Da sanyin safiyar Larabar nan dai, jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an ga motoci samfurin bulldozer da ke rusa gini a bakin harabar majalisar.
A ranar Litinin din makon nan dai ‘yan majalisar 27 cikin 32 suka bar jam’iyyar PDP inda Gwamnan ya ke suka koma APC ta shugaba Tinubu.

Kwastam sun fara binciken jami’ar su da ake zargi da karbar na-goro a filin jirgin Lagos

Wani faifan bidiyo ya bayyana yadda wata jami’ar hukumar kwastam a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, tana so ala-tilas sai an ba ta na-goro Naira 5,000.
Wani fasinja dai ne, aka gano bidiyon matar da ke sanye da uniform da mukamin anini daya take umurtarsa dole sai ya ba ta kudi kafin ya wuce da kayansa.
Sai dai mutumin ya hakikance cewa ba zai biya N5,000 ba, shi N1,000 zai biya.
Mai magana da yawun hukumar Abubakar Maiwada a cikin wata sanarwa, ya ce ana nan an kaddamar da bincike kan lamarin.
Maiwada ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa wanda aka nema ya ba da cin hancin ne ya nadi bidiyon.

Wata kungiya ta dauki nauyin lauyoyi 300 da za su taimaka wa Matawalle a kotun koli kyauta

Wata kungiyar ‘yan kishin kasa (Association Of Concerned Citizens) ta yi alkawarin hada kan lauyoyi masu zaman kansu akalla 300 domin bayyana ra’ayinsu na kare dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Bello Mattawale, a kotun koli.
Wannan lamari dai ya biyo bayan matakin da Gwamna Dauda Lawal da jam’iyyar sa ta PDP suka dauka na zuwa kotun koli bayan umarnin kotu ya sa a sake yin zabe a kananan hukumomi uku: Maradun, Birnin-Magaji, da Bukkuyum a jihar.
Da suke jawabi a taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Shugaban kungiyar Comr Ekemini Bassey, ya bayyana cewa sun dauki matakin na hada kan kwararrun lauyoyi 300 domin kare martabar dimokuradiyyar Nijeriya da kuma abin da mutane suka zaba, inda suke zargin a zaben na jihar Zamfara akwai magudin zabe da kuma masu yunkurin tsoratar da bangaren shari’a.
Kwamared Bassey, ya jaddada cewa dole ne kotun koli ta tabbatar da adalci domin kare martabarta, tare da kawo karshen girman kan wadanda suke ganin su ne ke rike da jihar Zamfara.
“Mun tattaro gungun lauyoyi da ‘yan gwagwarmaya masu fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci, kuma zamu tsaya tsayin daka har sai kotu na mana adalci kamar yadda muka san dama kotun adalai ne, muna kuma kara jaddada hada kai da neman adalci ga Gwamna Bello Matawalle mai jiran gado a karo na biyu”. inji shi. 
Ekemini ya bukaci kotun ta koli da ta yanke hukuncin ba tare da tsoro ba domin tabbatar da adalci ga alummar jihar Zamfara akan abunda suka zaba. 
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankulan jama’a, tare da nuna kwarin guiwar cewa za a yi adalci, yana mai cewa, “Bello Mattawalle zai dawo kan kujerarsa domin shine mai tausayin al’ummah, kuma wannan kungiya za ta tsaya masa tun daga farko har karshe, domin mun riga munyi bincike mun san wanene Bello Matawalle da kuma irin fadi tashin da yakeyi domin cigaban jihar zamfara ne a gabanshi.

Sanatocin Nijeriya sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen kauyen Tudun Biri

Sanatoci 109 na Nijeriya sun ba da kyautar albashinsu na watan Disamba ga iyalan da bam ya shafa a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna

Sanatocin sun sanar da hakan a ranar Lahadi, lokacin da suka kai ziyarar ta’aziyya da jajanta wa ga iyalai da gwamnatin jihar Kaduna.
Sanata Barau Jibrin da ya jagoranci tawagar ya ce kudin da suka ba da gudunmuwa sun kai Naira milyan 109.

An kama mijin da ya yi yunkuri kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinta a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama wani magidanci mai shekaru 35 da haihuwa da ake zargi da yunkuri hallaka matarsa da tabarya.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce mutumin ya sanar da su cewa ya yi yunkurin aikata hakan ne don ya samu damar sayar da talabijin dinta don ya kara jarin kasuwanci a shagonsa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ahmad Wakili.
‘Yan sandan dai sun ce mijin ya yi kuruwar cewa barayi sun shiga gidansa, ya ruga ya shiga dakin matarsa ya sanar da ita ta gaggauta rufe fuskarta. Daga nan ya fita, shi ma ya rufe fuskarsa, ya dawo cikin dakin da tabarya, ya fara jibga ma matar tabarya.
‘Yan sanda suka ce wanda ake zargin ya amsa laifin cewa ya yi niyyar kashe matar ne don ya samu damar sayar da talabijin da suke kallo a gidan, ya samu kudin da zai kara jarin kasuwanci a shagonsa.

Tsadar rayuwa ta sa ‘yan Nijeriya na jin haushin jami’an gwamnati – Kasshim Shettima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce yanzu haka ‘yan Nijeriya na jin haushin jami’an gwamnati da sauran ‘yan boko ganin irin halin matsin rayuwa da hauhawar farashi ta haddasa a kasar.
Mataimakin shugaban kasar na magana ne a Abuja a wajen taron da cibiyar nazarin tsaro ta shirya.
Jaridar Punch dai ta rawaito cewa wannan ne karon farko da aka ji wani jami’in gwamnati ya amsa cewa ana cikin yanayi na matsin rayuwa a Nijeriya tun bayan da Bola Tinubu ya karbi ragamar tafiyar da kasar a Mayun 2023.
Kasshim Shettima ya ce akwai ‘yan Nijeriya masu karamin karfi da ke jin haushin wadanda suke ganin sun samu rufin asiri. Har ya buga misali da cewa a Maiduguri, idan mutum ya sayo sabuwar mota, mutane na mayar da gidansa kamar wani wajen neman gafara ta yadda mutane ke yawan zuwa ziyara.

Nijeriya ce mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika

DW Africa ta rawaito cewa ya zuwa yanzu dai, Nijeriya ta sha gaban Egypt da Afrika ta Kudu.
Kamar yadda rahoton asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sanar, sauran kasashen Nahiyar Afrika da ke da karfin tattalin arziki su ne Ghana, Kenya, Tanzania, Angola, Morocco, Algeria da Ethiopia

An gano inda ake hada-hadar cinikin kodar bil’adama a Abuja

Wani zurfaffen bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano inda ake sayar da kodar bil’adama a babban birnin tarayya Abuja.
Binciken ya gano cewa a kasuwar ta bayan fage, ana sayar da duk koda daya kan kudi Naira milyan daya.
Kazalika, an gano yadda ake yaudarar mutane musamman masu karamin karfi ta yadda za a ja ra’ayinsu, su sayar da kodar su.
An dai gano cewa wannan sana’a ta jima ana gudanar da ita, musamman a yankin Mararaba da ke kusa da birnin tarayya, amma garin ya ke a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.

Za a kashe Naira milyan 173 don samar da lantarki ta hasken rana a asibitin Dutse, jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da a fitar da kudi Naira milyan 173 don aikin samar da lantarki ta hasken rana a babban asibitin da ke Dutse, babban birnin jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Sagir Musa ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya ce majalisar zartarwar jihar ce ta amince da hakan bayan taron da ta gudanar a ranar Alhamis.
Kwamishinan ya ce wannan matakin ya biyo bayan kudirin Gwamnan jihar Umaru Namadi na kyautata babban asibitin jihar don samar da kiwon lafiya mai inganci ga al’ummar jihar.

Sarkin Katsina ya sanar da korar shirin AGILE bisa saba ka’idojin Musulunci

 
Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya sanar da korar shirin inganta ilmin ‘ya’ya mata na AGILE daga jihar Katsina.
Mai Martaba Sarkin ya ayyana korar ne ga manema labarai a fadarsa, a lokacin da ya ke wasu nade-naden sarautu a karshen mako.
Jaridar yanar gizo ta Mobile Media Crew ta rawaito Sarkin na cewa, korar shirin ya biyo bayan keta wasu ka’idoji addinin Musulunci da shirin ke kokarin yi a jihar da kuma zargin kokarin bata tarbiyar ‘ya’ya mata da ke karatu a makarantu
Ya ci gaba da cewa shirin na kokarin wuce gona da iri wanda a matsayinsu na iyayen kasa, ba za su lamuncewa hakan a cikin kasa ba.