Da N800 muke ciyar da duk kare daya da muke aiki da shi, yayin da muke ciyar da fursuna da N750 a kowace rana – Gwamnatin Nijerya
Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasa Halliru Nababa ya ce hukumar na kashe kudi masu yawa don ciyar da karnukan da ake aiki da su, fiye da yadda ake kashe wa mutanen da ke tsare a gidan yari.
Halliru Nababa ya sanar da hakan ne a gaban kwamitin majalisar dokokin Nijeriya da ke kula da harkokin cikin gida son kare kasafin kudin shekarar badi, 2024.
Ya ce hukumar ta rubuta wa ministan harkokin cikin gida, inda take neman da a kara yawan kudin da ake ciyar da ‘yan gidan yari daga Naira 750 zuwa 3,000 a rana.
Shugaban hukumar ya ce har yanzu su na jiran amincewar ma’aikatar harkokin cikin gida kan wannan bukata ta su, inda ya bukaci majalisa ta sa baki don a amince musu su yi wannan karin.
Halliru Nababa ya ce a shekarar 2023, Nijeriya na da mutane 81,354 da ake tsare da su a gidajen ysrin kasar.
Hukumar ta sanar cewa tana ciyar da duk kare daya da ake aiki da shi a hukumar kan kudi Naira 800 duk rana.
Kotu ta yi hukunci ga mutumin da ya kashe abokinsa saboda Naira 100 a Zamfara
Babbar kotun jihar Zamfara ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum mai suna Anas Dahiru bisa samunsa da laifin kashe abokinsa saboda takaddamar kudi N100.
A shekarar 2017 ne dai aka gabatar da Anas a gaban kotun, inda ake zarginsa da kisan abokinsa Shamu Ibrahim kan Naira 100, inda ya daba masa wuka.
Da ya ke karanta hukuncin, Alkalin kotun Mai Shari’a Mukhtar Yusha’u, ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru da ke a unguwar Dallatu da ke cikin birnin Gusau ya caka wa abokinsa Shamu wuka a lokacin da suke takaddamar kudi Naira 100.
Shugaba Tinubu bai saka aikin samar da lantarkin Mambila cikin kasafin kudin 2024 ba
Jaridar Daily Trust ta gano cewa a cikin daftarin kasafin kudin shekarar badi, 2024 d shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa, babu kason aikin samar da lantarki a Mambila da ke Gembu jihar Taraba.
Sai dai an ware wa ma’aikatar makamashi da ke kula da sha’anin lantarki kudi Naira milyan 400 don shirya taruka a cikin shekarar ta 2024.
Aikin samar da lantarki na Mambila dai ya haddasa ce-ce-kuce a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, da ake kyautata zaton idan an yi shi zai samar da megawatts 3,050 ga Nijeriya.
A shekarar 2017, majalisar zartarwar Nijeriya ta amince da fitar da kudi Dalar Amurka 5.729 kwatankwacin Naira Tiriliyan 1.140 don gudanar da aikin.
Kotu ta umurci tsohon Gwamnan Zamfara Matawalle ya dawo da motocin gidan gwamnati
Babbar kotu da ke zamanta a Sokoto ta yi watsi da bukatar tsohon Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan hakkin mallakar motocin gidan gwamnati da ya tafi da su bayan ya sauka daga Gwamna a watan Mayun, 2023.
A watan Juni, ‘yan sanda sun shiga gidajen Matawalle suka kwaso motocin da ke ciki kamar yadda kotu ta umurta.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara Sulaiman Bala Idris ya sanar cewa kotu ta yi watsi da bukatar Matawalle a kan wadannan motoci.
Sulaiman Bala Idris ya ce tsohon Gwamnan na jihar Zamfara wanda yanzu haka shi ne karamin ministan tsaro a Nijeriya, shi da wasu jiga-jigan gwamnatinsa, sun kwashi motocin da aka ware wa ofisoshinsu suka bar gwamnatin Dauda Lawan babu motocin da za su yi amfani da su.
Sanarwar ta tunaso cewa duk a cikin watan Juni, gwamnatin Dauda ta ba Matawalle da saura mukarrabansa wa’adin kwanaki biyar na su maido da wadannan motoci. Ya ce bayan kin bin wannan urni ne ya sa gwamnati ta nemi iznin kotu ta je ta kwaso wadannan motoci.
Bayanai sun ce a baya, akwai kotun da ke zama a Gusau babban birnin jihar Zamfara, ta umurci da a maida wa Matawalle motocin, inda Matawalle ya sake shigar da wata kara yake neman kotun ta halasta masa wadannan motoci.
A haka ne, gwamnatin Dauda ta nemi a mayar da shari’ar a babbar kotu.
Nijar ta kulla yarjejeniyar tsaro da Rasha
Hukumomin mulkin sojan Nijar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karfafa huldar tsaro da kasar Rasha.
A yayin wata ziyara ce da wata babbar tawagar kasar Rashar ta kawo Nijar ne karkashin jagorancin karamin ministan tsaron kasar manjo kanal Evkurouv Lunus-Bek aka kulla wannan wannan yarjejeniya tare da ministan tsaron Nijar janar Salifou Mody.
Daga bisani tawagar ta samu ganawa da shugaban gwamnatin mulkin sojan birgediya janar ABDOURAHAMANE Tiana a fadar sa.




