Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 480

Kotu ta ci tarar Gwamna Abba N25m game da shari’ar Alhassan Doguwa

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ci tarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Naira miliyan 25 kan haddasa rudani da damuwa ga dan majalisar tarayya mai wakilta Kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Hon Alhassan Ado Doguwa.
Hakazalika, kotun ta kuma soke umurnin da gwamnan ya ba Atoni-Janar na jihar na sake duba shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisa.
A zaman kotun na ranar Juma’a, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya umurci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da kada ya sake taba ’yancin dan’Adam na mai kara Alhassan Ado Doguwa ko kuma tsoma baki a abin da ya shafe shi.

Cutar AIDs ta rage yawan kashe mutane inji Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, an samu raguwar mace-mace sakamakon cutar kanjamau (AIDS) da kashi 70 a faɗin duniya tun 2004.
Majalisar ta ce duk da wannan matsayi da aka cimma, har yau AIDS na kashe mutum guda a cikin duk minti guda.
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ne ya bayyana haka cikin saƙon da ya fitar albarkacin Ranar Yaƙi da AIDS ta Duniya ta 2023.
António Guterres ya ce, “ya zama wajibi mu ga bayan AIDS a matsayin ƙalubale ga lafiyar al’ummar duniya ya zuwa 2030.”
Ya ƙara da cewa, domin kawar da AIDS dole ne a maida hankali kan ƙauyuka wajen ba su kulawar da ta dace game da kiwon lafiya da dai sauran tallafi.
Haka nan, ya ce don cimma nasarar yaƙi da HIV ya zama dole a tafi tare da shugabanni al’ummomin karkara wajen gudanar da harkokin yaƙi da cutar.
Ya ce ana buƙatar sama da Dala biliyan takwas duk shekara wajen yaƙi da wannan cuta a ƙasashe masu samun ƙarami da matsakaicin kuɗin shiga.
“Lallai kawar da AIDS abu ne mai yiwuwa. Mu ƙarasa aikin kawar da cutar ta hanyar tallafa wa ‘yan karkara wajen yaƙi da wannan cuta,” in ji António Guterres.

Alamun dumamar yanayi ne ya sa aka samu ruwan saman ba-zata a wasu jihohin arewacin Nijeriya – NiMet

Hukumar ta bayyana hakan ne a wajen wani taron kara wa juna sani da ta shirya wa ‘yan jarida tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniy na, wajen tunatar da ‘yan jarida kan dumamar yanayi ta yadda za su fadakar da al’ummar kasar nan.
Taron ya gudana ne a Otel din Rock Biew da ke Abuja, inda ta ce wannan wani sharar fage ne kan babban taron da aka fara a kasar Dubai daga ranar 30 ga Nuwamba zuwa 12 ga Disamba.
Hukumar NiMet ta yi nemi ‘yan jarida su kara kaimin fadakar da al’ummar Nijeriya kan illar dumamar yanayi a bangaren lafiya da tattalin arziki da kuma yadda za a magance matsalolin ta hanyar da ta dace.
A cewarta, ta dauki nauyin bayar da horo ga ‘yan jarida ne kan dumamar yanayi, saboda ayyukan ‘yan jarida ba zai iya misultuwa ba wajen fadakar da al’umma illarsa da kuma hanyoyin magance lamari.
Da yake jawabi a wurin taron, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Mattias Schmale, ya ce dukkan kasashen duniya na fama da matsalar dumamar yanayi, amma kasashen da suka ci gaba sun dauki matakin rage matsalolin wanda hakan ya sa suke kokarin bayar da tallafi ga kasashe masu tasowa irinsu Nijeriya, domin a gudu tare a tsira tare.
Ya ce kididdiga ta nuna cewa kasashen Nahiyar Afirka su suka fi fuskantar barazanar kamuwa da illolin dumamar yanayi, wanda hakan  ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da hankali wajen taimaka musu.
Wakilin ya kara da cewa a 2023, an samu sauye-sauyen canjin yanayi ba ma a Nijeriya ba har da duniya baki daya, wanda akwai bukatar hada kannu da karfe wajen taimaka wa kasashe domin a tsira daga illar lamarin.
A tattaunawarsa da manema labarai, wakilin Kungiyar Masu Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) a yankin yammaci da Afirika ta tsakiya, Mista Biyarnada Edward Gomez, ya bayyana cewa, an shirya taron ne don zaburar da ‘yan jarida da dukkan masu ruwa da tsaki wajen tattaunawa tare da bayar da rahotannin da suka shafi dumamar yanayi da yadda take addabar al’ummar sassan duniya da kuma irin gudunmwar da kowa zai bayar don rage irin matsalolin da ake fuskanta.
Ya ce, wannan yana da muhimmanci musamman da yake ana gudanar da babban taron ne da majalisar Dinkin Duniya ta shirya a kan dumamar yanayi a Hadaddiyar Daular Larabawa, taron shi ne na 28 tun da aka fara gabatarwa duk shekara.
“Muna zama ne a kan dumamar yanayi. Ana yin zaman saboda dumamar yanayi na addabar kowa a duniya. Kowa da kowa. Daga Nijeriya zuwa nahiyar Turai da Asiya da Amurka. Kuma babban abin da yake haddasa dumamar yanayi shi sinadarin CO2 din da suke fita wanda ni da kai duk muna taimakawa wajen gurbata muhalli. Idan kana tukin mota, motarka tana shan mai. 
Mai kuma yana fitar da sinadarin ‘Carbon Diodide’ cikin sararin samaniya idan kana amfani da ‘Air conditioner’ shi ma yana fitar da iskar. idan ka kunna wutar lantarki shi ma yana fitar da gurbatacciyar iska. Toh dukkanmu muna taimakawa wajen fitar da shi. Amma akwai kasashen da suka fi yi fiye da wasu, kasashen da suke da manyan kamfanoni, sun fi haifar da dumamar yanayi fiye da kananan kasashe”.
Mr Gomez ya kuma kara da cewa, “Dumamar yanayi na faruwa, me za mu yi a kai? Dole mu nemo hanyoyin da za mu saba. 
Misali, idan ana samun ruwa sosai da yake janyo ambaliya me za mu yi? Dole mu nemo hanyar da za mu saba. Ko kuma dalilin wannan zaman shi ne domin zaburar da ‘yan jarida domin su samu karfin gwiwa da ra’ayi a kan wadannan labarun, za su iya rubuta labarai a kan abubuwan da ke faruwa kuma su taimaka wajen sabawa da kuma shirya wa manyan dumamar yanayi, kuma muna kira gare ku ‘yan jarida ku sa ra’ayinku a kai, saboda wannan zai shafe ka kuma zai shafe shi kuma zai shafe ni, ya shafi dukkan al’umma.
Ya kara da cewa, “lallai mun yi sa’a, Nijeriya ba ma cikin manyan garuruwan da illolin dumamar yanayi yake shafa, idan ka samu kanka a garin da ake ambaliya sosai za ka iya rasa rayuwarka, zan iya rasa rayuwata. Saboda haka dukkanmu ya kamata mu maida hankali a kan abin da yake tafiya kuma mu fitar da labarun da za su tsawatar wa mutane don su dauki mataki a kan lokaci. Kuma a shirye muke mu ci gaba da ba ku wasu labarai da suka shafi dumamar yanayi don watsawa ga al’ummar yankunan karkara.”
Taron ya samu halartar masana daga cibiyoyin bincike, malaman jami’o’i da ‘yan jarida daga kafafen watsa labarai na jihohin Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Jami’ar FUDMA za ta karrama Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero da digirin girmamawa

Jami’ar FUDMA da ke Dutsinma jihar Katsina ta sanar cewa za ta karrama manyan mutane uku da digirin girmamawa na ‘Honorary Doctorates’ da suka haɗa da Sarkin Daura Umar Faruq Umar, Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero da tsohon Jihar Katsina Barr Ibrahim Shema.
Kazalika, jami’ar ta sanar cewa daga yanzu duk mai son a dauke shi aikin malanta, sai ya yi digiri na biyu sannan.
Shugaban jami’ar Prof Armaya’u Hamisu Bichi ya sanar da hakan a taron manema labarai, a shirye-shiryen bikin yaye dalibai da jami’ar za ta gudanar.
Ya yi nuni da cewa digirin farko, bai isa a ba mutum aikin malanta a jami’ar ba a halin yanzu, inda ya kara da cewa can baya jami’ar tana ba daliban da suka kammala digirin farko da sakamako mai kyau na first class, saboda a baya jami’ar na kokarin tasowa ne.
Prof Bichi yace jami’ar za ta yaye daliban digirin farko 4,365 da wadanda suka kammala manyan digirori na Post Graduate.

Jami’ar FUDMA ta daina daukar masu digirin farko aikin koyarwa – VC

Jami’ar gwamnatin tarayya ta FUDMA da ke Dutsinma jihar Katsina, ta sanar da cewa daga yanzu duk mai son a dauke shi aikin malanta, sai ya yi digiri na biyu sannan.
Shugaban jami’ar Prof Armaya’u Hamisu Bichi ya sanar da hakan a taron manema labarai, a shirye-shiryen bikin yaye dalibai da jami’ar za ta gudanar.
Ya yi nuni da cewa digirin farko, bai isa a ba mutum aikin malanta a jami’ar ba a halin yanzu, inda ya kara da cewa can baya jami’ar tana ba daliban da suka kammala digirin farko da sakamako mai kyau na first class, saboda a baya jami’ar na kokarin tasowa ne.
Prof Bichi yace jami’ar za ta yaye daliban digirin farko 4,365 da wadanda suka kammala manyan digirori na Post Graduate.
Sannan ya sanar cewa jami’ar za ta karrama manyan mutane uku da digirin girmamawa na ‘Honorary Doctorates’ da suka haɗa da Sarkin Daura Umar Faruq Umar, Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero da tsohon Jihar Katsina Barr Ibrahim Shema.

Mata na cin zarafin maza a ‘yan kwanakin nan – NAPTIP

Hukumar da ke yaki da safarar bil’adama ta Nijeriya NAPTIP ta ce ta gano yadda ake samun yawaitar cin zarafin maza ta hanyar tursasa su wajen saduwa a ‘yan kwanakin nan.
Shugabar hukumar ta kasa Fatima Waziri Aza ta sanar da hakan a taron bitar da aka shirya a Abuja.
Mrs Fatima ta ce daga cikin matsalolin da mazan ke fuskanta sun hada da raba ‘ya’ya da mahaifinsu, korar mazan daga gidan da suke zaune da iyalansu da kuma cusguna musu.
Ta tabbatar wa da mazan da ke cikin wannan kunci da cewa su kwantar da hankulansu, akwai dokar da ta tsare mutuncinsu, inda ta ce sun samu korafe-korafe 15 a cikin wannan shekara da ke nuna yadda aka ci zalin din maza.

Tinubu ya gaza wajen yaki da cin zarafin dan adam-Amnesty International

0

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International
ta zargi shuga Tinubu da kau da idanu game da yadda ake amfani da karfi wajen
cin zarafin jama’a a Najeriya.

 

A wata makala da
kungiyar ta fitar mai taken tsarin yaki da cin zarafi a Najeriya, ta ce cikin watanni
shidan da Tinubu ya yi a Office bai tsinana komai ba, game da yaki da cin
zarafin jama’a.

Makalar da kungiyar
ta gabatar a Abuja, ta kunshi misalai game da yadda aka ci zarafin jama’a amma
gwamnati ta yi shiru.

Amnesty
International ta kuma ce abin takaici ne yadda kundin sabbin tsare-tsare da
gwamnati ta bijiro da su basu kunshi irin yadda za’a yaki cin zarafin jama’a
ba.

Sai dai kuma kungiyar ta ce har yanzu lokaci bai kurewa Tinubu
ba, don kuwa yana da damar da zai kawo karshen wannan matsala.

Shawara ta farko da hukumar ta baiwa Shugaba Tinubu shine ya yi kokari
wajen tabbatar da ganin an hukunta masu aikata wannan laifi.

 

 

Kwace mulki daga hannun Abba gida-gida ka iya tayar da rikicin da zai mamaye Africa- NNPP

 Shugabancin jam’iyyar
NNPP ya yi gargadin cewa amfani da karfin iko wajen kwace nasarar da Abba Kabir
Yusuf ya samu a jihar Kano, ka iya tayar da hankali, wanda zai iya mamaye
Najeriya har ma ya tsallaka zuwa wasu kasashen Africa.

 

Ta cikin wata
sanarwa da mai rikon kwaryar shugabancin jam’iyyar Abba Kawu Ali ya sanyawa hannu
aka kuma rabawa Kungiyar kasashen yammacin Africa, da ofishin jakadancin
Kungiyar tarayyar turai da na kasar Amurka da Burtaniya, ta ce akwai manyan
alamu da ke nuna cewa jam’iyyar APC ta lashi takobin yin duk mai yiwuwa wajen
kawace mulkin duk da bata yi nasara ba.

Sanarwar ta ce idan
aka lura da yadda jihar Kano ke ciki, ana zaman dar-dar ne, saboda yadda jama’ar
da suka fita kwan su da kwarkwata suka zabi Abba, amma ake shirin kwace wa,
wanda matukar hakan ta tabbata shakka babu zasu iya tayar da rikici.

Sanarwar ta kuma kara
da cewa akwai hasashen cewa jama’ar Kano ba zasu yi hakuri irin wanda suka yi a
2019 ba lokacin da aka yi amfani da wasu dokoki wajen kwace mulki kiri-kiri.

Abba Kawu Ali, ya
kuma ce akwai bukatar wadannan hukumomi da kasashen duniya su sanya idanu kan
wannan shari’a su kuma tabbatar an yi gaskiya, matukar ba haka ba kuma akwai
yiwuwar jama’a su dauki doka a hannun su.

Tinubu ya ware wa bangaren tsaro kaso mai tsoka a kasafin kudin 2024

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ware kaso mai tsoka a daftarin kasafin kudin shekarar badi, 2024.
A Larabar makon nan dai ne shugaban kasar ya gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan 27.5 a gaban Majalisar dokokin kasar.
Bangaren tsaro dai na da Naira Tiriliyan 3.25, kusan kaso 12% na daukacin kasafin kudin.
Daga tsaro, sai bangaren ilmi da aka ware wa Naira Tiriliyan 2.2, kusan kaso 9%. Sai kuma bangaren kiwon lafiya mai Naira Tiriliyan 1.4.