Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 496

Sojoji sun yi ikirarin yin sabon juyin mulki a Gabon

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1g3szG8W_wref_Zv6KR5OQS-4reXtKAj4
Wani gungun manyan jami’an sojin kasar Gaban ya bayyana a kafar yada labaran kasar ta Gabon24, inda ya sanar da karfe iko da hannun gwamnatin Ali Bango.
Kafar yada labaran Aljazeera ta ce sojojin da suka ce sun kifar da gwamnatin ta dimukuradiyya a safiyar Larabar nan sun ce matakin nasu ya biyo bayan mummunan magudin zaben da aka tabka a zaben shugaban kasa na makon da ya gabata da ya bai wa Shugaba Bango karin wa’adin mulki bayan kwashe shekaru 14 a kan karagar mulki.
Sojojin sun ce sun rufe iyakokin kasar tare da rusa shugabancin hukumomin gwamnatin ta Gabon.

Nijar ta bukaci jakadanta da ke Faransa ya dawo gida

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1AYPhzTcUVBfWkFQD_fzy9CrA7cnGKj0p
Sojojin mulkin dna Nijar sun bai wa  jakadan kasar a Faransa sa’o’i 48 na ta dawo gida. 

Sojojin sun bayyana hakan ne a cikin wasu takardu daban daban da suka aike ga ma’aikatun harakokin wajen kasashen
A cikin duka takardun dai hukumomin mulkin sojin na Nijar na cewa sun dauki matakin ne sakamakon kin amsa goron gayyatar da sabon ministan harakokin wajen Nijar din ya yi musu a wannan rana juma’a
Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta yi watsi da irin wannan mataki da aka dauka akan jakadan ta inda tace sojojin basu da hurumin yin hakan

Rashin sanin tarihi zai sa ku tabka kuskure irin na magabata – Atiku

0

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jaddada
muhimmancin ilimin tarihi wajen gina kasa. Maitamaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Atikun ya ce Waizrin Adamawa ya ambata hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin ayarin
hukumar editocin jaridar The Sun karkashin babban editan ta Mr. Onuoha Ukeh
yayin da suka kai masa ziyara a gidan sa da ke Abuja a wannan Talata.

 Tsohon mataimakin shugaban kasar Wanda yanzu haka ke
kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa a gaban kotu, kasancewar sa wanda ya
yiwa jam’iyyar PDP takara, ya ce ba tare da la’akari da darrusan da tarihi ya
nuna ba, za a ci gaba da maimaita kura-kuran da aka tafka a baya. Yace wadanda
suke zaune ba tare da sanin abin da ya gabace su ba, akwai yuwuwar su aikata
kura-kuran magabata, inda ya ce ba daidai ba ne a cire darasin tarihi daga
manhajar koyarwar makarantun Nijeriya.

Ruftawar gini ta yi ajalin mutane a sansanin ‘yan gudun hijira na Borno

0

 

Rahotanni daga birnin Maiduguri na cewa mutane 7 sun mutu a sakamakon faduwar gini a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri na jihar Borno.

Jami’an kungiyar Civilian JTF sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa wani aji ne ya fado kan wasu mutane da ke kwana a ciki sanadin ruwan sama a garin Munguno.

Bayanai sun ce ginin ya fado ne da misalin karfe 7 da rabi na safiyar yau, kuma nan take mutane 7 suka ce ga garin ku nan.

Wasu jami’an lafiya sun tabbatarwa manema labarai cewa akwai mutane fiye da 20 yanzu haka da ke kwana a babban asibitin garin Munguno suna karbar magani bayan raunukan da suka gamu da su.

Garin Munguno da ke da nisan kilomita 85 zuwa birnin Maiduguri na da ‘yan gudu hijira fiye da dubu 40 wadanda suka gujewa ta’addancin Boko Haram daga garuruwan su.

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Rabi’u Musa Kwankwaso

0

Jam’iyyar NNPP Ta dakatar da jagoran jam’iyyar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, kan zargin sa da yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Haka kuma jam’iyyar ta dakatar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar baki daya.
Baya ga wannan dakatarwa kwamitin zartawar ya nada Dr. Abgo Major a matsayin mai rikon mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da kuma Mr. Ogini Olaposi a matsayin mai rikon mukamin sakataren jam’iyyar da wasu Karin mukamai 18.
Kamafanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa dakatarwar ta tsahon wata shida ce ko kuma idan aka lura jagora kwankwason ya daidaita sahun sa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Ko a ranar 24 ga watan da muke ciki na Agusta sai da Kwamitin ayyuka na hukumar ya dakatar da wanda ya kirkiri jam’iyyar Dr. Boniface Aniebonam da kuma jami’in yada labaran jam’iyyar na kasa.
A baya dai jam’iyyar ta yi barzanar sallamar kwankwaso matukar bai daina bibiyar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da bibiyar ‘yan jam’iyyar APC ba, duk a kokarin da yake yi na ganin an bashi mukami kamar yadda ta yi zargi, sannan ta shawarce shi kan ya koma jam’iyyar da yake kwadayi salin alin, matukar zai zama cikakken dan jam’iyyar NNPP .

 

Babbar kotun jihar Kano ta haramtawa EFCC da wasu hukumomi bincikar Muhuyi

0

Babbar Kotun jihar Kano ta haramtawa Hukumar EFCC da kuma ta da’ar ma’aikata wato CCB daga kamawa ko kuma bincikar shugaban hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin gado.
A wata takarar dakatar da bincike da kotun ta bayar karkashin jagorancin mai shari’a Farouk Lawan ta ce hukumomin biyu basu bi hanyar da ta dace wajen dakatar da shugaban hukumar daga aikin sa na binciken hukumomi ko dai-daikun mutane ba.
Tun farko dai Antoni Janar na jihar Kano Lwan Musa Abdullahi shine ya shigar da karar yana mai bukatar kotu ta dakatar da EFCC da sauran hukumomi masu biye mata baya wajen bincika ko kuma kama Muhuyi koma dakatar da shi daga wani aiki da yake yi.
Ta cikin takarar da korafin da Antoni Janar din ya aikewa kotun ya yi karin hasken cewa bisa doka matukar wadannan hukumomi na bukatar bincike ko kuma tuhumar wani ma’aikaci ko shugaban wata hukuma a Kano ya zama wajibi su tuntubi Ofishin sa.
Takardar ta kuma kunshi jawabin cewa hukumomin basu yi biyayya ga waccan doka ba, suka yi gaban kansu wajen aikea da Muhuyi takarda, don haka basu da hurumin kama shi ko tuhumar sa, har sai Antoni na jihar Kano ya Amince.
Sai dai alkali Faruk Lawan ya sanya wata rana da yake bukatar jin hanzarin dukannin bangarorin biyu a lokaci guda.

 

APC ta bar ‘yan kasa cikin yunwa – PDP

0

Jam’iyyar adawa ta PDP a tarayyar Nijeriya ta soki lamirin salon mulkin gwamnatin Shugaba Tinubu ta ce sama da mutane milyan 150 a fadin kasar na kwana da yunwa.

Wannan dai ba bakon abu ba ne a siyasar kasar inda ko a lokutan baya lokacin da jam’iyyar APC ke adawa kafin darewa a kan madafun iko ta sha caccakar PDP dangane da salon jagorancinta.

Garin kwaki ya yi ajalin wata budurwa a Kano

0

 

Wata Budurwa mai suna Fiddausi Mahmud da ke garin Rimin Hamza a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ta mutu a sakamakon cin  garin kwaki da ta yi wanda ake zargin ya kulle mata ciki  lokacin da take matsananciyar jin yunwa.

Gidan rediyon Rahama da ke Kano ya ruwaito cewa mahaifin Fiddausi, Malam Mahmud Abdullahi ya ce iyalansa sun kwashe tsawon yini guda ba samu abincin da za su ci ba abin da ya sa ya fita nema kuma ya yi dace ya samo musu garin kwaki. Magidancin ya ce ba ya samun abin da ya wuce Naira 500 a rana guda, lamarin da ya kara jefa rayuwar iyalansa cikin wani mayuwacin hali la’akari da tsadar rayuwar da ake fuskanta a Nijeriya bayan janye tallafin man fetur.

Rahotanni sun ce tuni aka yi janaizar marigayiya Fiddausi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

‘Yan Nijeriya sun yi ”wawa” a wajen rabon kayan tallafi

0

Wasu mutane a jihar Bayelsa da ke Najeriya sun fasa tare da wawushe rumbun tara hatsi da sauran kayan abinci da gwamnatin jihar ta killace a birnin Yenagoa domin raba wa jama’a da zummar rage radadin ibtila’in ambaliyar ruwa tun a 2022. 

RFI Hausa wacce ta ruwaito wannan labarin ta ce gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan abincin sun fara lalacewa. 

An fasa rumbun ne da ke kan babbar hanyar Isaak Boro a Yenagoa saboda irin tashin hankalin da al’umar ke ciki na hauhawar farashn kayayyakin masarufi wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da ya haddasa tsananin tsadar rayuwa. 

Janye tallafin ne ya sa farashin man fetur  ya yi tashin goron-zabi daga N190 zuwa 620 kan kowacce lita wanda hakan ya shafi farashin motocin sufuri da kayan abinci da sauransu.

Sai dai Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Bayelsa ta bayyana cewa wadannan kayayyakin abincin da aka kwashe ba su da ingancin da za a iya aci, domin sun lalace don haka duk wanda ya ci zai fuskanci matsala. 

PUBLICITÉ

Tinubu ya haramtawa wasu mukarraban gwamnati zuwa Amurka

0

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya haramtawa jami’an gwamnati wadanda basu da alaka ta kai tsaye da taron majalisar dinkin duniya zuwa wajen taron.
Shugaba Tinubu ya bada umarnin a dakatar da Shirin karbar Visar da ake yiwa jami’an gwamnatin wadanda babu wata gudumowa da zasu bayar idan sun halarci taron.
Kakakin shugaban Ajuri Ngelale ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce wannan na cikin kokarin da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi na rage kashe kudade baji ba gani da gwamnati ke yi.
Sanarwar ta kuma kara da cewa an dorawa ministoci da manyan shugabannin hukumomin gwamnati da su sanya idanu wajen ganin ma’aikatan su basu tafi Amurka wajen taron ba matukar dai basu da abin yi a wajen.