Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 497

Uganda ta zartas da hukuncin kisa kan matashin da aka samu da auren jinsi

0

Mahukuntan kasar Uganda sun yankewa mutum na farko hukuncin kisa a tarihin kasar, bayan kama shi da laifin take dokokin da suka haramta auren jinsi.

Wannan shi ne karo na farko da kasar ta zartas da hukuncin da take ikirarin dauka duk da yadda kasashen yammacin duniya suka yi watsi da wannan mataki.

Dokar dai ta tanadi daurin rai da rai idan aka kama mutane biyu da laifin auren jinsi, sannan ta tanadi hukuncin kisa kai tsaye idan aka sake kama su a karo na biyu, ko kuma suka yiwa wani irin wannan dabi’a ta dole har ya kamu da cuta, ko kuma tilastawa karamin yaro ko tsoho ko masu bukata ta musamman.

Rahotanni sun ce tuni aka zartas da hukuncin kisan kan matashin mai shekaru 20, bayan an same shi da laifin maimaita luwadin bayan kamun da aka yi masa na farko da wani mutum mai shekaru 41.

Tuni dai shugaban kasar dama ‘yan majalisa suka fara shan suka, kan wannan mataki da suka dauka, wanda ake ganin yana da matukar tsauri.

 

Malamar da ta umarci dalibanta su mari abokin karantu saboda kasancewar sa musulmi ta shiga hannu

0

Mahukuntan jihar Uttar Pradesh ta India sun rufe wata makaranta mai zaman kanta, bayan da aka sami rahoton wata Malama da ta umarci daliban ta su mari abokin karantu su, kawai saboda kasancewar sa musulmi.

Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta ce bayan bullar Labarin dalibin da aka mara, bincike ya tabbatar da cewa makarantar mai suna Neha bata cika ka’idojin koyo da koyarwa ba.

Bayanai sun ce tuni aka fara kokarin rarraba daliban a tsakanin marantun gwamnatin da ke yankin. 

Tun farko malamar mai suna Tripta Tyagi ta umarci daliban ta su bi layi su kuma yi ta dallawa wa dalibin dan ajin su mari kawai saboda kasancewar sa musulmi.

Sai dai a ganawar Malamar da kafar yada labarai ta NDTV ta ce bata dana sanin abinda ta aikata, sai dai ta musanta cewa ta yi hakan ne don addinin dalibin, sai don bai yi aikin gida da ta bashi ba.

To amma ba tun yau ba iyayen yaron sun sha yin korafin cewa yaron yana yawan gaya musu malamar tana dukan sa da kuma aibata addinin sa.

A Wani gajeran Faifan bidiyo da ya rika yawo a karshen mako ya nuna yadda Malamar ta Umarci daliban su bi layi tare da marin abokin karatun nasu dan shekaru 7, kuma an jiyo lokacin da take musu tsawa cewa “Me yasa kuke marin sa a hankali? Ku mare shi da karfi”

Haka kuma an jiyo lokacin da take cewa “ku dake shi a baya yanzu fuskarsa ta yi ja” yayin da yaron ke tsaye yana kuka.

 

Faransa ta haramtawa mata musulmai sanya Hijabi a cikin makarantu

0

Gwamnatin kasar Faransa ta haramtawa mata Musulmai amfani da Hijabi, abaya ko kuma rufe kan su a cikin makarantu.

Tuni dai wannan sabuwar doka ta fara cin karo da suka daga kungiyoyin kare hakkin addinai da dai-daikun mutane, duk da cewa gwamnatin kasar ta ce ta yi haka ne don kare mata Musulman.

Wannan na zuwa ne bayan da cin zarafi da kuma kyamar mata musulmai ke kara ta’azzara a kasar da  ta yi kaurin suna wajen kyamatar addinin musulunci

Ta cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce mata musulmai a kasar na fuskantar kyara, tsokana da kuma cin zarafi musamman a tsakanin abokan karatun su da malamai a cikin makaratu, a don haka hana su sanya Hijabi ko kuma rufe gashin su ne kadai hanyar da zai sa su saje da sauran dalibai da nufin gujewa cin zarafi.

Sanarwar ta kuma kara da cewa bai kamata a ce da zarar malami ya shiga aji ya gane daliba musulma da wadda ba musulma ba.

Tun ba yanzu ba, malamai a kasar sun sha yin korafin cewa gane banbanci tsakanin daliban su musulmai da wadanda ba musulmai ba, yana hana su gudanar da aikin su yadda ya dace saboda irin ba banbancin mu’amala da ke tsakanin mabanbantan addinan.

Shugaba Tinubu ya karbi goron gayyatar tattaunawa da Joe Biden na Amurka

0

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya amince da tayín ganawar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, a gafen taron majalisar dinkin duniya.

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada Labarai, Aguri Ngelale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, jim kadan bayan kammala ganawar shugaban na Najeriya da babbar jami’ar diplomasiyyar Amurka kan nahiyar Africa Molly Phee.

Sanarwar ta kunshi cewa shugaba Tinubu ya kuma jadadda cewa ya zama wajibi Najeriya ta yi zarra a bangaren kasuwanci da jayo masu zuba jari a karkashin mulkin sa.

Bayan amsa tayin ganawar da shugaban Biden, Tinubu ya kuma bukaci Amurka ta taimakawa Najeriya ta hanyar  habbaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

A nata bangaren jami’ar ta Amurka kan Hulda da nahiyar Africa Uwargida Phee  ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin alaka ta kyautatu a tsakanin Najeriya da kasar Amurka.

 

Faransa ta bukaci jakadanta ya zauna a Nijar duk da korarsa da Janar Chiani ya yi

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1uDa9Cuy6B-zGQPYlTPa9wLSoRD3gvLBq
Jakadan Faransa a Nijar Sylvain Itte zai ci gaba da zama a kasar duk da cikar wa’adin kwana biyu da sojojin Nijar suka ba shi. 
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya sanar da haka a wannan Litinin a yayin ganawa ta intanet da ya yi da jakadan Faransa da ke sassan duniya.

Sojin Nijar sun yanke wa sojojin Faransa ruwa da lantarki a Yamai

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1Vg90jqgkYLpik-nyZdUj2n4ZsY0ZxeAx
Gwamnatin Janar Abdourahmane Chiani ta yanke wa sojojin Faransa da ke Nijar ruwa da wutar lantarki.
Rahotanni sun ce masu juyin mulkin sun katse kai wa sojojin wadannan abubuwa a kananan ofisoshin jakadancin Faransa da ke Damagaram, Tera, Oualam, Ayorou, Dosso, Niamey da Filingue.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan da sojojin na Nijar suka janye jakadan kasar da ke Faransa. 

EFCC na son binciken Muhyi Magaji kan zargin da ke da alaka da bidiyon dalar Ganduje

0

Hukumar dake yaki da cin hanci da
rashawa ta EFCC da hukumar kula da da’ar ma’aikata, sun fara binciken shugaban
hukumar hana cin hanci da karbar Korafe-korafe na jihar Kano Muhuyi Magaji
Rimin Gado kan zargin amfani da karfin gwamnatin tarayya wajen bincken cikin
gida.

 

Muhuyi Magaji Rimin Gado shine jami‘in
da ke tsaye kai da fata wajen tabbatar da zargin cin hanci da Karbar daloli
daga ‚yan kwangila da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Kano Abudllahi Umar Ganduje.

 

Hukumomin biyu ta cikin wasu mabanbantan
wasiku da suka iakewa hukumar, sun shaida cewa tuni suka  fara binciken shugaban ta, kan zargin amfani
da karfin da ya wuce wanda doka ta bashi a kan aikin sa, na binciken tsohon gwamna Ganduje game da bidiyon dala.

Tuni dai wannan sabon bincike ya fara haifar
da ce-ce ku-ce musamman a tsakanin Kanawa wadanda ke ganin Abullahi Ganduje yayi
amfani da sabon mukamin sa na shugaban jam’iyyar APC na kasa wajen shirya wa
muhuyi kulalliya.

 

Jaridar Premium Times ta ruwato cewa, ko
a lokacin da Gwamna Ganduje ke jagorantar jihar, yayi iya kokarin sa wajen ganin
binciken zargin bidiyon dala da ake yi masa bai yi nasara ba, ta hanyar amfani
da majalisar jihar.

 

Idan dai za’a iya
tunawa Sabuwar Gwamnatin Abba Gida-Gida ce ta mayar da Muhuyi Magaji Rimin Gado
kan mukamin sa, bayan da gwammnatin Ganduje ta dakatar da shi saboda zargin
wasa da aiki, kuma kememe ta ki mayar da shi duk da umarnin kotu.

 

Mutuwar fuju’a ta firgita dalibai a Enugu

0

 Ana ci gaba da zaman dar-dar yayin da
rudani ya mamaye zukatan dalibai da mazauna kewayen jami’ar kimiyya da Fasaha ta
jihar Enugu bayan da wasu dalibai har 13 suka mutu sakamakon wata cuta da ba’a
santa ba cikin ‘yan makonni.

 

Wasu daga cikin daliban jami’ar sun
shaidawa jaridar Premium Times cewa abokan karatun su 13 ne suka mutu
cikin kasa da makonni 2 sakamakon wata cuta mai ban tsoro da basu santa ba.

A cewar daliban cikin 13 da suka mutu
guda daya ce kadai aka yi gaggawar kaita asibitin koyarwa na jihar Enugu, inda
ta cika a can, kuma har yanzu ba’a gaya musu dalilin mutuwar ta ba.

Daliban sun kuma kara da cewa da zarar
dalibi ya fara nuna alamun rashin lafiya zai mutu nan take ba tare da bata lokaci
ba, abinda ke kara jefa su cikin razani.

Ko da ta ke karin haske kungiyar dalibai
ta NANS reshen kudu maso gabashin Najeriya ta bukaci mahukuntan makarantar su
yi gaggawar rufe ta don ceto rayukan sauran dalibai.

Ta cikin wata sanarwa da shugaban
kungiyar na shiyyar Kudu maso gabas Chidi Nzekwe ya fitar, ya ce kungiyar ta
damu matuka da irin wannan mutuwa mai ban mamaki, don haka akwai bukatar
mahukunta su yi gaggawar daukar mataki don gano dalili.

Sai dai kuma a wani martanin gaggawa da
shugaban sashen kula da dalibai na jami’ar Jude Udenta ya yi ta cikin sanarwar
da ya fitar, ya yi watsi da bukatar kungiyar dalibai na rufe makarantar.

Ta cikin sanarwar, Mr Udenta
ya musanta labarin cewa dalibai 13 ne suka mutu, yana mai cewa dalibai 5 ne
kachal suka mutu, yayin da yace guda daga cikin su ya mutu ne a sakamakon
hadarin mashin, kuma shi kadai ne ya mutu a cikin makaranta.

“Mu kan mu muna cikin rudani, kuma muna
mamakin irin wannan mutuwa, amma batun mutane 13 sun mutu ba haka bane, tun
farko mu bamu so maganar ta fita bainar jama’a ba, saboda a ganin mu bai dace ana
yamadidi da mutuwar daliban mu ababen kaunar mu a duniya ba” in ji Mr Udenta.

Mr Udenta ya kuma kara da cewa sauran dalibai hudun da
suka mutu sun mutu ne a wajen jami’ar, don haka babu tabbas game da dalilin
mutuwar su, ikirarin da tuni daliban suka musanta, bayan da suka tabbatarwa
manema labarai cewa dukannin dalibai 13 sun mutu a dakunan kwanan dalibai wasu
kuma a cikin aji.

Wannan labari mai cike da sarkakiya dai
tuni ya tilastawa gwamnatin Jihar kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin
sakataren gwamnatin Jihar Chidiebere Oniya.

Yayin ziyarar
da kwamitin ya kai jami’ar Mr Oniya ya ce, baya ga binciken, gwamnatin jihar ta
kuma umarci kwamishinan harkokin lafiya Emmanuel Obi da ya gudanar da nasa
binciken daban kan yanayin tsafta, lafiya da ma yanayin da karamin asibitin
shaka ka tafi na jami’ar ke ciki, saboda irin muhimmancin da daliban jami’ar ke
da shi ga jihar.

Har yanzu ban gamsu da shaidar karatun Tinubu ba- Atiku

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1U5du2TWkMzuecgUrugMfbQ7Cqp2GaEkC
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya ce shugaba Tinubu ya gaza gamsar da cikin yan Najeriya yadda ya samu shaidar kammala karatun jami’a a jihar Chicago ta Amurka.
Atiku a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter a wannan Lahadi ya ce bayanan karatun Tinubu na nuna tamkar bai yi karatun furamare da sakandare ba , jami’a kawai ya yi.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Atikun ke jiran sakamakon da kotun sauraran korafin zabe za ta yanke kan zargin da yake cewa Shugaba Tinubu ya murde masa nasarar da ya samu a zaben da ya gabata.

Son Nijeriya ne ya sa muke son dawo da Bazoum a Nijar – Tinubu

https://drive.google.com/uc?export=view&id=11NV5sySC5phE0Zv-H9-LqJQE7ZbFOO6p
Shugaban Nijeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS Bola Tinubu ya ce shi da kansa ya gamsu yaki da kasar Nijar ka iya haifar da matsaloli ga yunkurinsa na samar kofofin arziki ga ‘Yan Nijeriya. Amma a cewarsa, kokarin da ECOWAS ke yi na dawo da Nijar cikin hayyacinta, yunkuri ne na kare muradu da martabar Nijeriya.
Tinubu ya fadi haka ne a yayin wata ganawa da ya yi a ranar Jumma’a da jakadan Amurka a Nijeriya. Shugaban na ECOWAS ya ce yana da matukar muhimmanci ECOWAS ta yi amfani da hanyoyin da suka wajaba wajen dawo da dimukuradiyya da hana sojojin tsawaita zamansu a Nijar .