Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 495

AU ta dakatar da Gabon daga cikin mambobinta

Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, ta sanar da dakatar da kasar Gabon daga cikin jerin mambobin kungiyar sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasar da ke tsakiyar Afirka.
Kwamitin zaman lafiya da samar da tsaro na kungiyar taAU ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Alhamis.
Kafin daukar matakin kwamitin ya kuma yi kakkausar suka kan kwace mulki da sojoji suka yi a kasar ta Gabon, juyin mulkin wanda ya yi sanadiyar hambarar da gwamnatin shugaba Ali Bongo.
AU ta ce dakatarwar za ta haramta wa Gabon shiga dukkanin sabgogi da ayyukanta har sai an dawo da tsarin mulkin farar hula a kasar.

JIBWIS ta tara Naira milyan 90 daga kudin fatun layya a bana

Kungiyar JIBWIS ta ce a bana ta tara kudin fatun layya da resitai da jimillar kudaden suka kai kimanin Naira miliyan casa’in, da dubu dari takwas da hamsin da biyar, da dari biyar da arba’in da biyu kacal  (90,855,542.00) a wannan shekara ta 2023.
Shugaban kungiyar IZALA a Nijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya sanar da hakan bayan ya karbi rahoton kwamitin wanda shugaban kwamitin Sheikh Habibu Yahaya kaura ya ba da a garin Rano da ke jihar kano a ranar alhamis din nan.
Sheikh Bala Lau ya yaba wa ‘ya’yan kungiyar da suka yi hobbasa wajen ganin sun mika fatun layyansu ga kungiyar ta IZALA, ya kuma sha alwashin ci gaba da ayyukan raya addini kamar yadda aka Saba da kudaden a baya, ta yadda ko da wanda ya ba da ya koma ga Allah, zai ci gaba da samun lada mai gudana daga Allah Insha Allah.
A bana jihar kaduna ce ta zo ta farko, inda ta samar da:
N11,127,650.00.
Jihar Sokoto ita ta zo na biyu inda ta tara:
N10,967,080.00
Sai jihar Kebbi ita tazo na uku inda ta tara:
N9,185,397.00
Jihar Katsina ita ce ta hudu inda ta tara:
N6,284,930.00
Jihar Niger ta zo ta biyar inda ta tara:
N5,529,665.00
Juhar Zamfara ita ke biye da su inda ta yi na shida ta tara 
N5,042,380.00
Jihar Adamawa ita tayi na bakwai inda ta tara:
N4,736,820.00
Jihar Bauchi ita ta yi na takwas inda ta tara:
N4,567,600.00
Jihar Nasarawa ita ta yi na tara inda ta tara:
N4,477,550.00
Abuja FCT ita ta yi na goma inda ta tara:
N4,078,530.00

Mata ta kai mijinta kara kotu saboda ya shekara 2 ba su yi saduwar aure ba

Wata matar aure mai kimanin shekaru 25 mai suna Ruqayya Mukhtar a ranar Alhamis din nan ta shaida wa wata kotun shari’a da ke zamanta a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna cewa mijinta ya shafe shekara biyu bai kwanta da ita ba.
Matar wadda ta shigar da kara ta roki kotu da ta raba aurenta da mijinta mai suna Naziru Hamza, ta kuma koka kan yadda mijin ke cin zarafinta.
Sai da mijin ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa inda ya ce yana yin iya bakin kokarinsa wajen ganin ya gamsar da matarsa a yayin saduwa.

Mahaukacin kare ya hallaka jaririya ‘yar watanni biyar tana goye bayan mahaifiyarta

Wani mahaukacin kare a birnin Osogbo na jihar Osun  ya yi sanadiyyar mutuwar wata jaririya ‘yar watanni biyar da haihuwa.
Mahaifiyar jinjirar Nafisat Muideen ta ce lokacin da lamarin ya faru a cikin rukunin gidajen Hallelujah babu wadanda za su kai mata daukin gaggawa.
Mahaifiyar jinjirar ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:45 na rana a lokacin da take kan hanyar zuwa shago don sayo wa diyar magani.
Ta ce tana cikin tafiya ta ji haushin kare a bayanta, juyawarta ke da wuya, karen ya yi tsalle ya cimma yarinyar da ke goye a bayanta.

Za mu tabbatar an daina kasa kayan sana’a a bisa titunan jihar Katsina – Kwamandan KASSAROTA

Sabon Kwamandan hukumar kula da ababen hawa da tabbatar da dokar tuki ta jihar Katsina KASSAROTA Comr Amiru Tsiga ya sanar cewa za su yi aiki tukuru don tabbatar da mutane sun daina baza baza sana’o’i a bisa titunan da aka ware don mutane da ababen hawa su wuce.
Comr Amiru Tsiga na magana ne a lokacin da shiga ofis a matsayin sabon Kwamandan hukumar a Katsina.
A ranar 21 ga watan Agusta, 2023 ne dai Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Manjo Yahaya Rimi mai ritaya a matsayin Darakta Janar da Amiru Tsiga a matsayin Kwamandan hukumar ta KASSAROTA.
Hukumar KASSAROTA dai ce ke da alhakin kula da ababen hawa da yanayin tuki da kuma tabbatar da ba a zuba kayan kasuwa a kan titunan da mutane ke amfani da su ba da sauran ayyukan tsaftace harkar tuki.
Amiru Tsiga ya ce batun kasa kayan sana’a a bisa titi ya dade yana ci masa tuwo a kwarya tun kafin a bashi wannan mukami. Don haka ne ya ce zai ba da tashi gudunmuwa sosai don ganin an rika amfani da titi yadda ya dace.
Kwamandan ya ce ayyukan hukumar KASSAROTA ya shafi har ma wanda bai da wani abin hawa, madamar dai zai yi amfani da titin da aka tanadar don al’umma su bi, ko a kafa ko a keke.
“Ni gaskiyar magana, yana daya daga cikin abin da ke min tuwo a kwarya, tun kafin Allah Ya kawo ni wannan matsayin. Kuma ina kira ga su masu ababen hawa, hukumar KASSAROTA ba wuri bane na cutar da al’umma a jihar nan. Mutane ne kamar kowa, illa kiran da zan yi, al’ummar jihar Katsina su bi doka da oda”.
Ya yi godiya ga Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda da ya ba shi damar hidimta wa al’ummar jihar ta hanyar nada shi wannan mukami da ya ce zai yi amfani da shi domin al’ummar jihar su amfana.

Sojojin Nijar za su fitar da jakadan Faransa daga kasar da karfin tuwo

 

Sojojin Nijar sun umurci ‘yan sandan kasar su fitar da jakadan Faransa da ke cikin kasar da karfin tuwo ta hanyar tasa keyarsa.

Gidan rediyon DW Hausa ya ruwaito ma’aikatar harkokin wajen Nijar a cikin wata sanarwa na cewa gwamnati ta bai wa ‘yan sandan kasar umurnin fitar da jakadan Faransa daga kasar ta hanyar tisa keyarsa. Kazalika ma’aikatar harkokin wajen ta sanar da soke takardar visa da sauran takardun diflomasiyya na jakadan kasar ta Nijar da iyalinsa.

Tinubu nake yi wa aiki ba APC ba kuma har yanzu ina PDP – Nyesom Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya ce shi fa shugaba Tinubu yake yi wa aiki ba wai jam’iyyar APC ba.
Tsohon Gwamnan na jihar Rivers ya ce yana yi wa shugaban kasar aiki ne don ya aminta da shi har ya damka masa amana. Wike ya fadi haka ne a lokacin da ya halarci shirin siyasa na gidan talabijin na Channels.
Ya ce ban yi nadamar cewa ina PDP na yi wa shugaba aikin da ya ci zabe ba.
‘Yan Nijeriya na ta tofa albarkacin bakinsu game da yiwuwar kasancewar Wike a jam’iyyar PDP ganin yadda aka nada shi minista kuma sunansa ya fito a jerin mambobin kwamitin yakin neman zaben Gwamna a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi a zaben da zai gudana a Nuwambar 2023.

Gwamnati ta kashe Naira bilyan 81 wajen dasa itatuwa a arewacin Nijeriya

Kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilan Nijeriya da ke bincike kan yadda aka alkinta kudaden kula da muhalli ya sa kafa ya shure batun da hukumar kula da muhalli ta kasa ta yi na cewa ta kashe Naira bilyan 81 wajen sayowa tare da dasa itatuwa milyan 21 a jihohin da ke fama da matsalar zaizayar kasa a arewacin Nijeriya.
Jihohin su ne na Kebbi, Katsina, Sokoto Zamfara, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Yobe da Borno.
Darakta Janar na hukumar Yusuf Maina Bukar ya fada wa ‘yan kwamitin cewa hukumar ta kuma kashe kudi Naira milyan 697.71 wajen gyaran ofisoshi da Naira bilyan 11.28 wajen gudanar da manyan ayyuka.
Shugaban kwamitin Isma’ila Haruna Dabo, ya sanar da cewa hukumar ta kashe kudi kawai ba tare da an ga alfanun hakan ba. Kazalika, kwamitin ya ce wannan hukuma ta kauce daga irin tsarin aikin da aka kafa ta.

Duk sojan da ba zai yi wa Tinubu biyayya ba, ya ajiye aikin – Janar Takuti

0
Babban Kwamandan rundunar soji ta 81 Manjo Janar Muhammad Takuti Usman ya bukaci jami’an soji a Nijeriya da su ci gaba da yi wa shugaba Bola Tinubu da duk wanda kundin tsarin mulkin kasa ya umurce su biyayya.
Janar Takuti Usman na magana ne a lokacin da ya ziyarci rumbun adana makamai na 35 Artillery Brigade da ke Alamala, Abeokuta jihar Ogun.
Kwamandan sojin ya bukaci sauran sojojin da su kasance masu biyayya tun daga sama har kasa. Kalaman nasa dai na zuwa ne a lokacin juyin mulki ke ta kara fadada a Nahiyar Afrika, a yayin da aka hambarar da gwamnatin Ali Bango na kasar Gabon.
Janar Takuti ya ce rundunar sojin Nijeriya ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin da’a ba daga jami’anta ko ma wani daga waje, inda ya ce akwai ‘yan matsaloli nan da can, amma dai ba a wannan sashen adana makamai ba.

Gwamnatin Kano ta sayo gadajen Aurar da zawarawa 1,800

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki na ma’aurata 1,800 a karkashin shirinta na aurar da zawarawa a fadin jihar.
Babban kwamandan hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da wasu daga cikin kayayyakin auren a ranar Laraba a Kano.
Ya ce gwamnati jihar ta ware kudi sama da Naira miliyan 800 don siyan kayan daki da kayan abinci da kayan sawa da sauran kayan bukatu na bikin auren na zawarawa da za ta kaddamar.