Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 498

ECOWAS: Sojojin Nijar sun umurci dakarunsu su daura damarar kare kansu

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1Vysv8_z8ewmYbzFdOWkH5y6KznuZlH5a
Sojojin da suka yi juyin mulkin Nijar sun bukaci dakarunsu su kasance cikin shirin kare kansu daga hare-haren da suke fargabar za su fuskanta. 
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce umurnin na kunshe a cikin wata takarda da majalisar koli ta mulkin sojin Nijar ta fitar a ranar Jumma’a. Sai dai kungiyar ECOWAS ta ce ba ta da niyyar afka wa Nijar, illa dai kokari take na mayar da Nijar din tafarkin dimukuradiyy ta hanyar diflomasiyya.

‘Yan ta’adda sun sace jigon APC a Kaduna

‘Yan ta’adda sun sace Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, a jihar Kaduna Hon Kawu Ibrahim Yakasai a gidansa da ke kauyen Yakasai na karamar hukumar Soba ta jihar a daren Juma’a.
Daily Trust ta rawaito cewa ‘yan ta’addar sun kutsa kai gidan mutumin da misalin karfe 10 na daren Juma’a, inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani wurin da har yanzu ba a kai ga sani ba.
Hon Kawu Ibrahim Yakasai dai tsohon shugaban karamar hukumar Soba ne ta jihar Kaduna.
Lawal Shehu, mai magana da yawun Gwamnan jihar Kaduna ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Gwamna Uba Sani ya umurci jami’an tsaro da su durfafi ‘yan ta’addar nan su kuma tabbatar sun kubutar da Hon Yakasai.

“Za mu kara albashin ma’aikatan Shari’a don yaki da rashawa” – Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi alkawari cewa gwamnatinsa za ta yi wa ma’aikatan Shari’a karin albashi da ma sanya masu alawus-alawus ta yadda za a magance matsalolin cin hanci da rashawa a fannin Shari’a.
Shugaba Tinubu ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar sanarwar shugqban ya ce sun lura cewa ya zama tilas gwamnati ta yi yaki da cin hanci da rashawa don haka za su yi nazari sosai kan albashi da alawus-alawus na jami’an shari’a”.
Tawagar NBA ta samu jagorancin shugaban kungiyar, Yakubu Maikyau, babban lauyan Nijeriya (SAN), mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale.

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da lokacin da matatun man kasar za su dawo aiki

Karamin ministan man fetur Heineken Lokpobiri ya ce matatar man fetur ta Port Harcourt za ta dawo aiki a cikin watan Disambar bana.
Ministan ya ba da wannan tabbacin ne a yayin wani rangadin duba ci gaba da aikin gyaran da ake yi a matatar man ta garin Fatakwal na jihar Ribas a ranar Juma’ar nan.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta fara gyaran matatar Warri a watannin uku farko na shekara mai zuwa, sannan kuma za a gyara ta Kaduna cikin karshen shekara mai zuwa.

Ba Turawan Yamma ke ingiza mu daukar mataki kan Nijar ba – ECOWAS

Kungiyar ECOWAS ya musanta rade-radin da ake yi cewa Turawan Yamma ne ke juya akalarta game da rikicin juyin mulkin Nijar.
Shugaban hukumar kungiyar ta ECOWAS Omar Aleiu Touray ne ya sanar da hakan a Abuja a lokacin da ya kira taron manema labarai.
A ranar 26 ga Julin 2023 ne dai sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum a Nijar, inda sojojin suka nada Janar Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaba na riko.
Kungiyar ECOWAS dai ta sha sukar lamirin sojojin da suka yi wannan juyin mulkin, inda suka saka wa Nijar dokoki daban-daban da zummar sojojin su ji matsi su mayar da gwamnatin farar hula a kasar.

‘Yan bindiga sun hallaka jami’an kwastam a jihar Kebbi

Hukumar kwastam ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda biyu bayan wata musayar wuta tsakanin jami’an nata da wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne kan titin Bunza-Dakingari-Koko a jihar Kebbi.
A cikin wata sanarwa daga Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta kwastam a jihar Kebbi Mubarak Mustapha da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an ke aikin binciken ababen hawa, ‘yan bindigar a cikin wata mota samfurin Toyota Corolla suka far musu, su kuma suka mayar da biki, aka ci gaba da musayar wuta, har aka samu wannan asarar rayuka.
Sanarwar ta ce jami’an da suka rasu sun hada da Alhaji Kabiru Shehu mai mukamin ‘Insfekta’ da Abdullahi Muhammad mai mukamin ‘Custom Assistant’ da sanarwar ta ce tuni an rigaya an yi musu sutura.
Yanzu haka dai hukumar kwastam din ta kaddamar da farautar wadanda suka yi wannan aika-aika da zummar kama su don girbar abin da suka shuka.
Kwantarolan hukumar a jihar Kebbi Ben Oramalugo ya yi ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da roko ga al’umma da su rika kwastam bayanan sirri ingantattu da za su taimaka a dakile safarar kaya ba bisa ka’ida ba da sauran masu aikata assha a cikin al’umma. 

Ana karancin naman shanu da na tumaki da dabino a Nijeriya bayan rufe bodar Nijar

Safarar shanu, tumaki, dabino da sauran kayan bukata da ake shigowa da su Nijeriya daga Jamhuriyar Nijar ta samu tangarda bayan rufe iyakar kasashen biyu.
Nijeriya dai ta sanar da rufe iyakarta da Nijar bayan da soji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum a watan 26 gaJuli, 2023.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa kaso mai tsoka na naman shanu da ragunan da ake ci a sassan Nijeriya daban-daban na zuwa ne daga Jamhuriyar Nijar.
Kusan jihohi 6 dai ne suka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da suka hada da Katsina, Jigawa, Yobe, Sokoto, Borno da Kebbi.
‘Yan kasuwa da sauran masu safara na kokawa cewa wannan mataki na gwamnatin Tinubu ya tsayar da harkokinsu cik, inda suka yi roko da gwamnati ta sake duba na tsanaki game da matakin.

An yi jana’izar sojoji 20 da aka kashe a Neja

Yanzu an gudanar da jana’izar sojoji 20 da harin ‘yan ta’adda ya rutsa da su a jihar Neja.
A makon jiya dai ne hukumomi daga bangaren sojin Nijeriya suka sanar da mutuwar jami’ansu 36, bayan da ‘yan ta’adda suka yi musu kwanton-bauna a hanyar  Zungeru-Tegina na jihar Neja a lokacin da suke bisa jirgi.
Daily Trust ta ba da labarin cewa ministocin tsaro Muhammad Badaru da Bello Matawalle da shugaban sojin Nijeriya CG Musa duk sun halarci jana’izar.
Karin wadanda suka halarci jana’izar, sun hada da mataimakin Gwamnan jihar Neja Yakubu Garba da shugaban sojin kasa Taoreeq Lagbaja da sauransu.
Daga cikin wadanda aka yi jana’izarsu akwai Habib Aliyu da ya shiga aikin soji a shekarar 2020 da Nura Muhammad da ya shiga aikin a shekarar 2016 da sauransu.

Wike ya umurci a kama wanda ya mallaki benen da ya rufta a Abuja

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayar da umurnin a jami’an tsaro su cafke mutumin da ya mallaki benen nan mai hawa biyu da ya ruguje a daren Laraba a unguwar Garki, Abuja.
Wike ya ba da umurnin a lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a ranar Alhamis.
ya kuma bukaci babban sakatare na hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, Adesola Olusade, da ya biya kudaden jinyar wadanda ke kwance a asibiti.

Cece-kuce kan zargin raba gurbatacciyar masara da gwamnati ta yi a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da jama’a cewa masara da sauran kayan abinci da ake ta yamadidi cewa an raba a wasu sassan jihar gurbatacci ne, to ba daga gwamnatin jiha bane, daga kananan hukumomin jihar ne.
Kwamishinan yada labaran jihar Malam Bala Salisu Zango ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai a Katsina.
Kazalika, kwamishinan yada labaran ya ce kudin da ake cewa gwamnatin tarayya ta ba jihohi Naira bilyan biyar-biyar, to jihar Katsina Naira bilyan 2 kacal ta samu daga gwamnatin tarayya.
Ya ce “an jawo hankalin gwamnatin jihar Katsina game da wani labari da ke yawo a kafafen yada labarai cewa gwamnatin tarayya ta ba jihohi kudi Naira bilyan biyar-biyar domin samar da ababen saukaka rayuwa. Ina mai farincikin sanar da ku cewa Naira bilyan 2 kacal gwamnatin jihar Katsina ta samu daga gwamnatin tarayya domin sayo hatsin da za a rarraba wa al’ummar jihar.”
Ya ci gaba yana cewa “akwai alfanu a fayyace cewa, gwamnatin tarayya ta shirya kashe Naira bilyan 5 domin sayo masara, shinkafa da taki don raba wa ga jihohi, amma sai gwamnoni suka nace cewa sai dai a ba jihohi kudinsu kai tsaye domin su sayo wadannan kayan abinci da taki, domin farfado da tattalin arzikin kananan ‘yan kasuwa da saukaka hanyoyin rabon kayan da sauran hanyoyin duk da za a bi don samun sauki wajen aiwatar da shirin. A haka, gwamnatin tarayya ta ba da wadannan kudade ga jihohi.”
Babu ko shakka, gwamnatin tarayya ta umurci babban bankin kasa na CBN da ya ba da kudin ga jihohi a matsayin bashi mai saukin ‘ruwa’, wanda gwamnatin tarayya za ta biya kaso 52% sai jihohi su biya kaso 48% a cikin watanni 12.”
Ya ce ya zama wajibi, a nan, a fayyace cewa, gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda PhD ta karbi wannan Naira bilyan 2, har ma ta yi abin da ya dace da ita, ta sayo buhunan shinkafa 40,000 da za a rarraba a runfunan zaben da ke jihar.
Bugu da kari, a kwana-kwanan nan, kwamishinan ya ce, Gwamna Radda ya umurci kananan hukumomi a jihar Katsina da su sayo tare da rarraba masara ga al’umma kyauta a kananan hukumominsu. Ya cigaba yana cewa Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin a saukaka tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta bayan cire tallafin man fetur.
“An rigaya an sayo wadannan kayan abinci, kuma an rarraba ga al’umma a dukkanin runfunan zaben da ke jihar Katsina.”
Kan haka ne, ake kira ga al’ummar jihar Katsina da su kara nutsuwa cike da tabbacin cewa da zarar gwamnatin tarayya ta kara kawo daukin wasu kudin, gwamnatin jihar Katsina za ta kara sayo wasu kayan abincin domin raba wa ga jama’ar yadda ya dace.”
Sai dai ya ce wannan masarar marar kyau da ake zargin an raba, kuma ake alakantata da gwamnatin jiha, to ba daga gwamnatin jihar take ba, sai dai daga kananan hukumomi.