Sojoji sun kama tirela makare da makamai za a shigo da ita Nijeriya daga Mali
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa
Dan ‘sumogal’ ya kashe jami’in kwastam a Kebbi
Kotu ta umurci DSS da ta saki Emefiele ko ta kai shi kotu
Ina sane da mawuyacin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki inji shugaban kasa Bola Tinubu
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ya fahimci irin halin kuncin da talakawan kasar suka shiga ta dalilin cire tallafin man fetur, inda ya tabbatar da cewa an dauki matakin ne don kasar ta cigaba da kuma gina kyakkyawar rayuwa ga ‘yan kasa.
Za a samu matan da suka dauki juna biyu ba tare da sun shirya ba kimanin 700,000 cikin shekarar 2023 a Nijeriya
Asusun tallafa wa yawan al’umma na majalisar dinkin duniya UNPF ya ce kalubalen da ake fuskanta wajen shirin tsarin iyali na iya kaiwa ga yawan samun cikin-shege da yawan zubar da cikin.
Ba kowace iyakar Nijeriya muka bude ba – Kwastam
Mukaddashin shugaban hukumar Kwastam Wale Adeniyi ya ce ba dukkanin iyakokin Nijeriya na tudu aka bude ba.
Katsinawa za su san wadanda Dikko zai nada kwamishinoni a makon gobe
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda zai aike da sunayen wadanda zai nada mukamin kwamishinoni a gwamnatinsa ga majalisar dokokin jihar a makon gobe.
Zan samar da tsaron da ko tsakar dare ‘yan Nijeriya za su iya fita harkokinsu inji sabon shugaban sojoji
Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Manjo Janar Taoreeq Lagbaja, ya ce karkashin jagorancinsa, sojoji za su gudanar da aikin samar da tsaron da zai sa al’ummomin dake Neja, Zamfara da sauran jihohin dake fama da matsalolin tsaro za su rika fita harkokinsu ko da karfe biyun dare ne ba tare da sun ji tsoron harin ta’addanci ba.
An kama jirgin da ya shekara 12 yana satar danyen mai a Nijeriya
A Nijeriya kamfanin NNPCL ya sanar da kama wani jirgin ruwa makare da dayen mai da yawansa ya kai kimanin lita 800,000 da ake zargin na sata ne.
