Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 52

Akwai kura-kurai a rahoton kamfanin KPMG kan sabbin dokokin haraji – Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta yi karin haske kan rahoton da kamfanin KPMG ya fitar game da sabbin dokokin haraji, inda ta ce yawancin batutuwan da kamfanin ya kalla a matsayin kura-kurai ko gibi ba daidai ba ne, sai dai rashin fahimta da kuma bambancin ra’ayi kan manufar gyaran tsarin haraji.

A cikin sanarwar da kwamitin sabunta dokokin haraji na fadar shugaban kasa ya fitar, gwamnati ta ce sabbin dokokin haraji sun bi ka’idojin duniya ne don tabbatar da gaskiya, daidaito da hana zamba.

Gwamnatin ta jaddada cewa matakan da ta dauka kamar harajin riba daga hannun jari, takaita amfani da kasuwar bayan fage wajen sayen daloli, da kuma sharadin VAT ga duk harkar da ba a bi doka ba, duk wani yunkuri ne na tsabtace tsarin haraji da karfafa tattalin arziki.

DCL Hausa ta rawaito cewa gwamnati ta ce KPMG ta yi watsi da muhimman sauye-sauyen da sabbin dokokin suka kawo, ciki har da rage harajin kamfanoni daga kashi 30% zuwa 25%, karin fa’idodin VAT ga ‘yan kasuwa, tallafin kananan masana’antu da masu karamin karfi, da kuma kawar da harajin minimum tax.

Gwamnatin ta ce gyaran dokokin haraji babban mataki ne da zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin Nijeriya.
Gwamnati ta bukaci kamfanoni da masana su koma ga tattaunawa mai ma’ana domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da sabbin dokokin haraji.

Wike ya nemi hadin kan ‘yan siyasa a Rivers da su dunkule wuri guda su mara wa Tinubu baya a 2027

0

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya yi kira ga shugabannin siyasa da al’ummomi a jihar Rivers da su ƙara haɗin kai da fahimtar juna domin tabbatar da samun cin ribar dimokuraɗiyya.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin ziyara a karamar hukumar Andoni, wadda ta zama wuri na 20 inda yake ziyartarsu domin gode wa al’ummar kan goyon bayan da suka bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen 2023 tare da neman karin goyon baya a gabanin zaɓen 2027.

Tsohon Gwamnan Rivers ya ce manyan jam’iyyun siyasa a jihar sun haɗu ƙarƙashin inuwa guda inda ya bukaci shugabannin al’umma su ci gaba da aiki tare domin Tinubu ya dawo a karo na 2 a zabe mai zuwa.

Shugaba Trump na Amurka ya amince cewa ba Kiristoci ne kadai ake halakawa a Nijeriya ba

Shugaban Amurka, Donald Trump, a karon farko ya amince cewa ba iya Kiristoci ne matsalar tsaro ta shafa ba, Musulmi ma na daga cikin wadanda suke rasa rayukansu a Nijeriya, duk da cewa ya dade yana nuna cewa Kiristoci ne kawai ake kai wa hari a ƙasar.

Trump ya fadi hakan ne a wata hira da jaridar New York Times, inda ya ce ba addini guda daya ne kawai ke fuskantar matsalar tsaro ba, sai dai duk da haka ya dage cewa Kiristoci ne suka fi shan wahala.

Sai dai ya ce hare-haren da aka kai kan wasu wuraren ‘yan ta’adda a ranar Kirsimeti, Amurka na iya sake kai hare-hare idan ana ci gaba da kashe Kiristoci.

Wasu lauyoyi biyu daga Tanzania sun yi kara a gaban kotu suna kalubalantar zaɓen 2025 da aka gudanar a kasar

0

Wasu lauyoyi biyu a Tanzania, Tito Magoti da Bob Wangwe, sun kai ƙasar Tanzania gaban Kotun Gabashin Afirka kan zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Oktoba, 2025, suna zargin cewa zaɓen bai cika ka’idojin dimokuraɗiyya da dokoki ba.

A ƙarar da suka shigar, lauyoyin sun gurfanar yi karar Antoni Janar na Tanzania da kuma Sakataren Janar na kungiyar kasashen Gabashin Afirka (EAC), inda suka ce zaɓen ya saɓa wa tanade-tanaden yarjejeniyar kungiyar, musamman waɗanda suka shafi dimokuraɗiyya.

Lauyoyin sun jaddada cewa yadda aka gudanar da zaɓen ya tauye waɗannan ka’idoji, lamarin da a cewarsu ya sanya sakamakon ya zama abin tambaya a idon doka da ƙa’idar dimokuraɗiyya a yankin Gabashin Afirka.

Za mu karbi Peter Obi hannu biyu a jam’iyyar LP idan bai samu takara a ADC ba – Datti Baba Ahmed

0

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party LP,Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa Peter Obi zai samu tarba a LP idan har bai samu tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ba a zaɓen 2027.

Datti ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin Channels, inda ya ce ya fi dacewa Obi ya dawo jam’iyyar da suka tsaya takara tare a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Sai dai Datti ya ce yana alfahari da abin da suka yi tare da Obi a baya, yana mai jaddada cewa har yanzu shi jagoran LP ne kuma bai fice daga jam’iyyar ba, sabanin rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Akwai gibi mai tarin yawa da muka gano cikin sabbin dokokin harajin Tinubu a Nijeriya – Kamfanin haraji na KPMG

Kamfanin haraji na KPMG, ya bayyana cewa ya gano manyan kura-kurai, a cikin sabbin dokokin haraji na Nijeriya, duk da burin da gwamnati ke da shi na inganta tattara kuɗaɗen shiga da sauƙaƙa tsarin haraji.

Rahoton KPMG ya fito ne bayan shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokokin a ranar 26 ga Yuni, 2025, inda suka fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.

A wata sanarwa da KPMG ta fitar ta ce duk da cewa dokokin na da damar ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati idan aka aiwatar da su yadda ya kamata, akwai buƙatar gyara cikin gaggawa domin cimma manufar gyaran harajin.

Za a yi zabukan ‘yan majalisar dokoki da kananan hukumomi a Benin

0

Kasar Benin Republic za ta gudanar da zaɓukan ’yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi a ranar Lahadi, wata guda bayan wani yunkurin juyin mulki da ya girgiza ƙasar, zaɓen da ake ganin zai yi tasiri kan zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya yi a watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna cewa jam’iyyun da ke ƙarƙashin hadakar shugaban ƙasa, Patrice Talon, na dab da ƙarfafa ikonsu, musamman ganin yadda babbar jam’iyyar adawa ta Democrats ba za ta shiga zaɓukan ƙananan hukumomi ba, kuma an hana ta shiga zaɓen shugaban ƙasa saboda rashin cika sharudda.

A halin yanzu, jam’iyyar Democrats za ta shiga zaɓen majalisa, amma ana fargabar za ta rasa kujeru da dama, kasancewar hadakar jam’iyyar Talon na rike da kujeru 81 cikin 109 na majalisar ƙasar.

Zaɓen na zuwa ne a daidai lokacin da Benin ke fuskantar matsin lamba bayan yunkurin juyin mulki na ranar 7 ga Disamba, wanda sojoji suka dakile cikin sa’o’i tare da taimakon Nijeriya da Faransa.

‘Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da aikata assha da diyarsa a jihar Bauchi

Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekaru 28 bisa zargin lalata da ’yarsa ta cikinsa ’yar shekara takwas, lamarin da ya faru a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Alhamis, an ce wanda ake zargin ya kira yarinyar zuwa bandaki, inda ake zargin ya aikata laifin a kanta ba tare da amincewarta ba.

An ce an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda ranar 31 ga Disamba, 2025,bayan karɓar rahoton, tawagar bincike ƙarƙashin jagorancin CSP Kadiri Danjuma, DPO na Alkaleri, ta gaggauta zuwa wurin, ta kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta, sannan ta kama wanda ake zargin.

Shugaba Tinubu na hasashen samun saukin hauhawar farashi a Nijeriya cikin 2026

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar zai sauka kasa da kashi 10 cikin 100 a shekarar 2026, lamarin da ya ce zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan kasa da kuma kara habakar tattalin arziki (GDP).

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, 9 ga Janairu 2026, yayin da Shugaba Tinubu ke yaba wa kamfanonin Nijeriya da masu ruwa da tsaki a kasuwar zuba hannun jari bisa samun Naira tiriliyan 100.

Shugaban ya ce cimma wannan matsayi alamar tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da farfadowa ne, inda ya bukaci ‘yan kasa da ‘yan kasuwa su kara zuba jari a Nijeriya, yana mai tabbatar da cewa shekarar 2026 za ta fi alfanu ga masu zuba jari sakamakon ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatinsa.

Shugaba Trump ya yi sabuwar barazanar kara kawo sabbin hare-hare a Nijeriya

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin barazanar sake kai hare-haren a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci, duk da musanta wa da gwamnatin Nijeriya.

Trump, ya bayyana cewa Amurka na iya kara kai hare-haren soji a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci a kasar, kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito a wata hira da aka wallafa ranar Alhamis, 8 ga Janairu 2026.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters,ya rawaito cewa Trump ya yi wannan jawabi ne yayin da ake tambayarsa kan harin soji da Amurka ta kai Nijeriya a ranar Kirsimeti, inda sojojin Amurka suka ce sun kai harin ne kan ‘yan kungiyar IS a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya bisa bukatar gwamnatin Nijeriya.

Trump ya kara da cewa duk da cewa Musulmi ma ana kashe su a Nijeriya, a cewarsa Kiristoci ne suka fi fuskantar hare-hare, ra’ayin da gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da shi, tana mai jaddada cewa ‘yan ta’adda na kashe Musulmi da Kiristoci baki daya, ba tare da nuna wariya ta addini ba.