Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 56

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa za ta tsunduma sabon yajin aiki

Kungiyar Likitocin masu neman kwarewa NARD ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin, 12 ga Janairu, 2026, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da aka cimma da su.

Shugaban kungiyar, Dakta Mohammad Suleiman, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na X a karshen makonnan, bayan taron gaggawa da aka gudanar a ranar Jumma’a.

Ya ce yajin aikin, zai fara ne idan har gwamnatin tarayya da ma’aikatar Lafiya ba su aiwatar da yarjejeniyar da aka rattaba hannu da ƙungiyar ba.

Tankiya tsakanin Nijer da Benin ta sa kasashen rufe ofisoshin jakadancin juna

Kasashen Benin da Niger sun kori jami’an diflomasiyyar juna a wani mataki na ramuwar gayya, bayan shafe kusan shekara biyu ana takun-saka a tsakaninsu, a cewar majiyoyin diflomasiyya.

Dangantakar kasashen ta tabarbare ne tun bayan da sojoji suka kwace mulki a Niamey a watan Yulin 2023.

Gwamnatin mulkin sojan Niger dai na zargin Benin da yunkurin tayar da hankula, zargi da Cotonou ke musantawa.

Rikicin ya kara tsananta bayan dakile yunkurin juyin mulki a Benin a farkon watan Disambar jiya. Duk da cewa Benin ba ta zargi Niger kai tsaye ba, ana ci gaba da nuna shakku kan rawar da Niamey ka iya takawa.

A ‘yan kwanakin nan, Benin ta kori wani jami’in leken asiri da dan sanda da ke aiki a ofishin jakadancin Niger a Cotonou.

Idan za a tuna, an dakile yunkurin juyin mulkin Benin na 7 ga Disamba ne da taimakon Najeriya da Faransa, yayin da aka samu yaduwar labaran karya a kafafen sada zumunta cewa an kifar da gwamnatin kasar da ke yankin Sahel.

Niger na cikin kawancen AES ta Burkina Faso da Mali, kasashen da suka fice daga ECOWAS, wadanda ke kusantar siyasa da Rasha, tare da sukar kasashen gabar teku na yammacin Afirka da ke da alaka da Faransa, ciki har da Benin da Ivory Coast.

‘Yan bindiga sun yi ajalin mutane fiye da 30 a jihar Neja

Aƙalla mutane 30, ciki har da mata, sun rasu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari Kasuwan Daji da ke ƙauyen Demo, Borgu LGA a Jihar Niger, a ranar Asabar.

Maharan sun shiga kasuwar da misalin 4:30 na yamma, inda suka ƙone kasuwar, suka wawashe kayan abinci da sauran dukiyoyi na daruruwan miliyoyin naira, tare da yin garkuwa da wasu mutane.

Jaridar Daily Trust ta ambato wani mazaunin yankin ya ce maharan sun fito ne daga dajin National Park a Borgu, kuma sun yi ta’addanci ba tare da wani ƙwakkwaran ƙalubale ba daga jami’an tsaro ba.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Niger, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin, yana cewa jami’an tsaro sun ziyarci wurin da safe, inda aka tabbatar da mutuwar sama da 30, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.

Goyon bayan jagororin APC ga takarar Fubara a 2027 ta sake dagula alakarsa da Wike

1

Manyan shugabannin jam’iyyar APC sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, domin neman wa’adi na biyu, duk da rikicin siyasa da ke ƙara tsananta tsakaninsa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Sakataren APC na ƙasa, Ajibola Basiru, ya ce jam’iyyar za ta tsaya tsayin daka wajen kare Fubara a matsayin gwamnan APC, yana mai jaddada cewa yana tafiyar da mulkin jihar yadda ya kamata.

Haka kuma, shugabancin jam’iyyar ya tabbatar da Fubara a matsayin jagoran APC a Rivers.

Sai dai Wike ya ce sauya sheƙar Fubara zuwa APC ba ta ba shi tabbacin tikitin takara kai tsaye ba, yana mai barazanar hana shi dawowa.

Anthony Joshua fitaccen dan damben UFC ya koma Burtaniya

0

Tsohon gwarzon damben duniya Anthony Joshua ya koma Birtaniya bayan hatsarin mota a Najeriya da ya yi sanadin mutuwar Latif Ayodele da Sina Ghami.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ‘Yan sanda sun gurfanar da direban motar, Adeniyi Mobolaji Kayode, kan tuhumar tukin ganganci da ya haddasa rasa rai, inda zai gurfana a kotu ranar 20 ga Janairu.

Hatsarin ya faru ne a hanyar Lagos–Ibadan bayan motar da suke ciki ta buge wata mota da aka aje a gefen hanyar.

Joshua ya samu raunika kaɗan kuma an sallame shi daga asibiti, kuma ya koma Birtaniya ne gabanin jana’izar abokan aikinsa.

sojojin Nijeriya sun yi ajalin ‘yan bindiga uku a jihar Kogi

0

Dakarun 12 Brigade na Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kawo karshen ‘yan bindiga uku tare da kama wanda ake zargin mai samar musu da kayayyaki a yayin wani samame a Kabba Bunu da Yagba West a Jihar Kogi.

Aikin ya gudana ne a ranar Asabar 3 ga Janairu, 2026, bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan bindiga.

Jaridar Punch ta ruwaito Lt. Hassan Abdullahi, na cewa sojojin sun yi musu kwanton-bauna inda aka yi artabu da bayarayin, lamarin da ya tilasta ‘yan bindigar janyewa.

Lauyoyin Bazoum sun ce rabon su da magana da shi tun watan Oktoban 2023 da aka kwace wayar sa

1

Barista Reed Brody ne daya daga cikin lauyoyin hambararren shugaban ya bayyana haka kamar yadda Wadata Radio ta ruwaito yana mai cewa shekaru biyu kenan yanzu rabon su da magana da wanda suke karewar

Wannan korafi na lauyoyin hambararre shugaban kasar na Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da ake gamgamin saka hannu kan wata takarda ta neman a saki Bazoum inda tuni wadansu fitattun mutane da suka hada da wadansu tsoffin ministoci da masu ci da wadansu kasashe suka hannu

Sojojin da suka yi wa Bazoum juyin mulki a ranar 26 ga watan Yulin 2023 ne dai ke tsare da shi da mai dakinsa a wani bangare na fadar shugaban kasar tun bayan da suka hambare shin

Kwankwaso ba shi kadai ya ƙirƙiri Kwankwasiyya ba – Dr Adamu Dangwani

Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa tafiyar Kwankwasiyya Dakta Adamu Dangwani ya ƙaryata zargin da ake yi cewa wasu tsoffin abokan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun ci amanar tafiyar Kwankwasiyya.

Ya baiyana cewa waɗanda ke yin irin wannan zargi ba su fahimci ma’anar cin amana ba.

Dr. Dangwani yayin wata tattaunawa da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta intanet a Kano ya jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya ba mallakin mutum ɗaya ba ce tare da cewa ƙungiyar an samar da ita ne tare kuma an ba ta suna ne ta hannun ƙananan ’yan siyasa da masu ilimi ba wai Sanata Kwankwaso kaɗai ya ƙirƙire ta ba.

Ya ce kalmar Kwankwasiyya da kafuwar ƙungiyar tun asali ra’ayi ne na mutane shida, ciki har da Alhaji Salisu Buhari, Farfesa Hafiz Abubakar, wani tsohon minista da aka sani da Borodo, Farfesa Umar Farouk, Alhaji Rabiu Suleiman Bichi da shi kansa.

Ya jaddada cewa siyasa ra’ayi ce kuma sabanin ra’ayi ba cin amana ba ne, sa’annan rabuwa a siyasa abu ne na al’ada kamar yadda hakan ke faruwa ko a cikin iyali.

Dr. Dangwani ya ƙara da cewa hanyoyinsu da Sanata Kwankwaso sun bambanta ne lokacin da tsohon gwamnan Kano ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP ba tare da tuntubar wasu daga cikin makusantansa ba.

Kotu za ta yanke hukunci kan belin Abubakar Malami a ranar 7 ga Janairu

Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta sanya 7 ga Janairu domin yanke hukunci kan bukatar beli da Abubakar Malami, tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, ya gabatar bisa zargin safarar kudi.

A halin yanzu, Malami na tsare a gidan gyara hali na Kuje tare da dansa, Abdulaziz Malami, da daya daga cikin matansa, Bashir Asabe, wadanda ke fuskantar shari’a a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 a kansu, tana zarginsu da safarar kudade har Naira biliyan 8.7. Dukkaninsu sun musanta zargin lokacin da aka gurfanar da su a ranar 29 ga Disambar 2025.

EFCC ta yi watsi da zargin Gwamna Bala Mohammed na tsangwamar jami’an gwamnatinsa

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati a Nijeriya ta yi watsi da ikirarin da Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Bauchi, ya yi na cewa ana amfani da hukumar wajen tsangwamar sa da jami’an gwamnatinsa ta fuskar siyasa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, EFCC ta bayyana zargin a matsayin “karya” tana jaddada cewa hukumar na gudanar da ayyukanta ne cikin ‘yanci ba tare da katsalandan na siyasa ba.

Hukumar na mayar da martani ne ga kalaman Gwamna Bala Mohammed, inda ya yi zargin cewa wasu masu ruwa da tsaki na siyasa na amfani da EFCC wajen muzanta shi da makusantansa, musamman Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya.

EFCC ta ce ayyukanta na bin doka da oda ne kawai, tare da tabbatar da cewa ba ta aiki bisa umarnin kowace jam’iyya ko mutum, illa bin ka’idojin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.