Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 60

Kasar Birtaniya ta dakatar da bai wa ‘yan Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo biza

0

Gwamnatin kasar Birtaniya ta sanar da dakatar da tsarin ba ’yan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo biza, lamarin da ake zargin zai shafi matafiya daga ƙasar da dama.

Wannan mataki, kamar yadda hukumomin Birtaniya suka bayyana, ya biyo bayan kin karɓar ’yan ƙasar da suka shiga Birtaniya ba bisa ƙa’ida ba.

Baya ga haka, Birtaniya ta ce manyan jami’an gwamnati da manyan baki daga Congo za su rasa damar shiga kasar kamar yadda suka saba a baya.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin watan Nuwamba, ma’aikatar cikin gida ta Birtaniya ta gargadi DR Congo, Angola da Namibia cewa za su fuskanci takunkumin biza matuƙar ba su karɓi ’yan gudun hijira da kuma ’yan ƙasarsu masu aikata laifuka a kasashen ƙetare ba.

Za a kaddamar da aikin bututun iskar gas na AKK a 2026 – Shugaban NNPCL

0

Kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPC Limited ya bayyana cewa ana sa ran aikin bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano AKK wanda darajarsa ta kai dala biliyan 2.8 zai fara aiki a farkon shekarar 2026.

Shugaban kamfanin NNPCL Bashir Bayo Ojulari ne ya bayyana hakan bayan kammala duba aikin da Ministan harkokin albarkatun man fetur Ekperikpe Ekpo ya jagoranta tare da manyan jami’an NNPCL.

Ojulari ya ce NNPCL ta kammala manyan layukan bututun gas na AKK, wanda ya shafe shekaru da dama ya ana gudana.

Sojoji sun ceto wani mutum da shanu a tsakanin Kano da Katsina

Sojojin rundunar haɗin gwiwa na Joint Task Force sun yi nasarar ceto wani mutum da aka sace tare da kwato wasu shanu da ‘yan bindiga suka kwace, bayan artabu da suka yi da su a iyakar jihohin Kano da Katsina.

Rahotanni daga rundunar sojin sun nuna cewa lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi a yankin Yankwada na jihar Kano, bayan sojoji sun samu bayanan sirri kan motsin wasu ‘yan bindiga da ke shigowa daga yankunan Daurawa da Kira na jihar Katsina zuwa bangaren Kano.

Majiyoyin sojin sun bayyana cewa dakarun sun tare ‘yan bindigar ne a yankin Ungwan Dogo da Ungwan Tudu, inda aka yi musayar wuta mai zafi tsakaninsu.

A yayin artabun, an samu nasarar ceto wani mutum mai suna Rabiu Alhaji Halilu, mai shekaru 38, wanda aka sace,sai dai rahotanni sun ce an harbi Halilu da bindiga a kafa, inda aka gaggauta kai shi asibitin na soji da ke Faruruwa domin samun kulawar likitoci.

Majalisar Dokokin Taraba ta musanta cewa Kakakinta ya raba Naira 1000 a matsayin barka da Kirsimeti

0

Majalisar Dokokin Jihar Taraba tare da Zing Watch Group sun musanta rahotannin da ke yawo cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, John Bonzena, ya raba Naira dubu dai-daya ga al’ummar mazabarsa a matsayin barka da Kirsimeti.

Musantawar ta biyo bayan rahotannin da suka ce wasu mata da matasa daga yankin karamar hukumar Zing sun nuna rashin jin daɗi bayan an ce an gayyaci kusan mutum 37 zuwa gidan Kakakin Majalisar a Jalingo domin karɓar kyautar barka da Kirsimeti.

Rahotannin sun yi ikirarin cewa mutanen, da aka zaɓo daga mazabu daban-daban a Zing, sun je Jalingo ne da fatan samun tallafi mai yawa, amma daga bisani suka zargi cewa Kakakin Majalisar ya ba su N1,000 kacal, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Sai dai a cikin sanarwarsu ta manema labarai daban-daban da aka fitar a ranar Asabar, Majalisar Dokokin Jihar Taraba da Zing Watch Group sun bayyana cewa kyautar ba ta shafi baƙin da suka zo daga Zing ba. Sun ce an tanadi tallafin ne ga yara da matan da ke zaune a unguwar da Kakakin Majalisar ke zaune a Jalingo, ba don baƙin mazabarsa ba.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai yi balaguro zuwa Turai

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Lagos a ranar Lahadi, 28 ga Disamba, domin ci gaba da hutun karshen shekara a Turai, kafin daga bisani ya wuce Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa.

 

An gayyaci Shugaba Tinubu ne don ya halarci taron Abu Dhabi Sustainability Week 2026, wanda ake shirin gudanarwa a farkon watan Janairu, inda manyan shugabanni daga bangaren gwamnati, ‘yan kasuwanci ke tattauna hanyoyin bunkasa ci gaba mai dorewa a duniya.

 

A cikin wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan yada labarai Mr. Bayo Onanuga, ya fitar, ta bayyana cewa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, ne ya gayyaci Shugaba Tinubu domin halartar taron.

 

Sanarwar ta ce shugaban kasar zai dawo Nijeriya da zarar an kammala taron UAE din.

Za a yi fafatawar karshe a gasar kokawar cin takobin Nijar

0

Zakirou Zakari da Noura Hassan ne ‘yan kokawar da za su yi fafatawar karshe a yammacin wannan rana ta Lahadi 28 ga watan Disamban 2025, a gasar takobin Nijar da ke gudana a jihar Tahoua.

 

‘Yan kokowar da dukkanin su suka kasance ‘yan jihar ta Tahoua mai masaukin baki, sun yi nasarar kai wa wannan mataki ne bayan karawar wasan kusa da na karshe da aka yi a safiyar wannan rana, inda Zakirou Zakari ya yi nasarar kada Mati Siley na jihar Maradi yayin da shi kuwa Noura Hassan ya yi nasarar kada Chaibou Ardji na jihar Maradi.

 

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun ‘yan jiha guda sun zo matakin karshe ba, domin kuwa a baya bayan nan jihar Dosso ma ta taba kafa wannan tarihi inda Noura Hassan da Kadai Abdou da aka fi sani da Issaka Issaka suka yi karon karshe.

 

A yanzu dai abin jira a gani shi ne wanda zai yi nasarar lashe wannan gasar ta kokawar cin takobin na kasa karo na 46.

Sojoji sun ceto wani da aka yi garkuwa da shi a kan iyakar jihar Kano da Katsina

0

Sojojin Nijeriya karkashin rundunar hadin gwiwa ta Faruruwa sun samu nasarar kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a kan iyakar jihar Kano da Katsina da safiyar Lahadi.

 

Mai magana da yawun runduna ta 3 da ke Kano Manjo Zubairu Babatunde, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewa an samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a yankunan Daurawa da Kira da ke kan iyakar Katsina da Kano.

 

A cewar sa, bayan dauki ba dadi da ‘yan bindigar, sojojin sun samu nasarar kubutar da mutumin mai suna Rabi’u Alhaji Halilu, wanda ya samu raunin harbi a kafarsa.

 

Rundunar dai ta ce tuni aka mika shi asibiti don samun kulawar gaggawa.

 

Haka kuma ta samu nasarar kwato tarin babura da kuma shanun da ake kyautata zaton na sata ne wadanda ‘yan bindigar suka tsere suka bar su.

Ana fitar da litar Dizal sama da 300,000 a matatar Fatakwal – NMDPRA

0

Hukumar kula da albarkatun man fetur ta Najeriya NMDPRA ta ce matatar mai ta Fatakwal da ke jihar Rivers na samar da dizal duk da cewa an rufe ta.

Cikin wani bayani da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, NMDPRA ta ce har zuwa watan Nuwamban da ya gabata, matatar man na samar da lita 349,000 a kowace rana wanda ake fitarwa zuwa kasuwa.

Tun a ranar 24 ga watan Mayu 2025 ne kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya sanar da rufe matatar man ta Fatakwal domin gudanar da gayara, inda ake cikin wata na bakwai a halin yanzu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ne Malamina a siyasa – Shugaban APC na Nijeriya

0

Shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa yana koyon siyasa ne a wajen shugaba Tinubu.

Nentawe ya fadi hakan ne yayin da yake karbar sarautar gargajiya ta “Kaeh-rit” a jihar Plateau.

A cewar sa, shugaba Tinubu gogaggen dan siyasa ne wanda ya kasance cikin wadanda ya kamata a yi koyi da su a fagen siyasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Haka kuma ya jingina duk wata nasara da zai iya samu a tafiyarsa ta siyasa do horon da ya samu daga Tinubu.

‘Yansanda sun dakile yunkurin ‘yan bindiga na tare wata babbar hanya a Zamfara

Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar dakile wani yunkuri daga ‘yan bindiga na tare wata babbar hanya.

 

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar na jihar DSP Yazid Abubakar ya fitar, ta bayyana cewa a ranar 21 ga watan Disamban 2025, jami’an sashen hana garkuwa da mutane na rundunar karkashin jagorancin ASP Aliyu Bilyaminu Koko, ta samu bayanan sirri kan cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar Tsafe zuwa Yanwarin Daji.

 

Hakan ya sa suka kai dauki wajen, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da yayi sanadiyyar jikkatar wasu da dama da suka tsere, aka kuma kama mutum guda mai suna Umar Alhaji Bukar da aka fi sani da Bingil wanda ya mika wuya.

 

Rundunar ta jinjinawa jami’an tare da al’umma wadanda suka taimaka wajen bayar da bayanan sirrin kan yunkurin ‘yan bindigar.