Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 61

Tinubu ne Malamina a siyasa – Shugaban APC na Nijeriya

0

Shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa yana koyon siyasa ne a wajen shugaba Tinubu.

Nentawe ya fadi hakan ne yayin da yake karbar sarautar gargajiya ta “Kaeh-rit” a jihar Plateau.

A cewar sa, shugaba Tinubu gogaggen dan siyasa ne wanda ya kasance cikin wadanda ya kamata a yi koyi da su a fagen siyasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Haka kuma ya jingina duk wata nasara da zai iya samu a tafiyarsa ta siyasa do horon da ya samu daga Tinubu.

‘Yansanda sun dakile yunkurin ‘yan bindiga na tare wata babbar hanya a Zamfara

Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar dakile wani yunkuri daga ‘yan bindiga na tare wata babbar hanya.

 

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar na jihar DSP Yazid Abubakar ya fitar, ta bayyana cewa a ranar 21 ga watan Disamban 2025, jami’an sashen hana garkuwa da mutane na rundunar karkashin jagorancin ASP Aliyu Bilyaminu Koko, ta samu bayanan sirri kan cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar Tsafe zuwa Yanwarin Daji.

 

Hakan ya sa suka kai dauki wajen, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da yayi sanadiyyar jikkatar wasu da dama da suka tsere, aka kuma kama mutum guda mai suna Umar Alhaji Bukar da aka fi sani da Bingil wanda ya mika wuya.

 

Rundunar ta jinjinawa jami’an tare da al’umma wadanda suka taimaka wajen bayar da bayanan sirrin kan yunkurin ‘yan bindigar.

Ni ne dan siyasa na biyu da aka fi ci wa zarafi a Nijeriya – Nyesom Wike

2

Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa shi ne dan siyasa na biyu da aka fi ci wa zarafi a Nijeriya bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Wike ya bayyana haka ne a garinsa na Ochiba da ke karamar hukumar Ahoada ta gabas a jihar Rivers, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wike dai ya jaddada ci gaba da goyawa shugaba Tinubu baya a kowane lokaci, tare da cewa daga watan Janairun 2026, za a sake komawa siyasa a jihar Rivers a hukumance.

Kwankwaso ya umurci a ba ’ya’yan ’yan majalisar Kano da suka rasu tikitin takarar maye gurbinsu

0

Jagoran darikar Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya umarci a bai wa ‘ya’yan ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu da suka rasu damar tsayawa takara a karkashin jam’iyyar NNPP domin maye gurbin iyayensu.

 

Cikin wata tattaunawa da DCL Hausa ta yi da shugaban jam’iyyar NNPP na Kano Dr Hashim Sulaiman Dungurawa, ya tabbatar da cewa an cimma matsayar ne bayan da Kwankwaso ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kuma iyalan mamatan a gidansa da ke Kano.

 

A cewar sa, amince musu su tsaya takarar don wakiltar kananan hukumomin Ungoggo da Municipal a zauren majalisar dokokin Kano, ya zo ne duba da irin gudunmawar da iyayensu suka bayar wajen hidimtawa al’umma.

 

Dungurawa ya ce suna kyautata zato tare da sa ran cewa Sa’ad Aminu Sa’ad, da kuma Nabil Aliyu Daneji za su kwatanta irin rawar da iyayensu suka taka a fagen siyasa da kuma aikin hidimtawa al’umma.

Jam’iyyar ADC ta soki gwamnatin Tinubu kan harin Amurka a Nijeriya

0

Jam’iyyar ADC mai hamayya a Nijeriya, ta soki gwamnatin shugaba Tinubu kan damar da ta bai wa Amurka wajen kaddamar da hari kan ‘yan ta’adda a jihar Sokoto.

 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta a Nijeriya Bolaji Abdullahi ya fitar a shafinsa na X, ya ce ya zama wajibi Nijeriya ta dauki alkalin kare kanta da kuma samar da tsaro cikin gida ba tare da sa hannu daga waje ba.

 

Haka kuma, ya ce hakan na nuni da yadda Tinubu wanda ke da alhakin jan ragamar shugabanci ya koma baya, lamarin da ta ce abin tambaya ne, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Jam’iyyar dai, ta ce kamata yayi irin wannan mataki ya zama na karshe da za a iya dauka idan har an rasa duk wata damar kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya.

Jam’iyyar EFF ta Afirka ta Kudu ta yi tir da amincewar Nijeriya kan harin Amurka

0

Jam’iyyar Afirka ta Kudu ta dan gwagwarmayar adawa da Turawa Julius Malema (EFF) ta yi Allawadai da yadda Nijeriya ta amince da harin Amurka a cikin kasar kan ‘yan ta’adda.

 

A cikin wata sanarwa, EFF ta nuna damuwa cewa Najeriya ba ta kalubalanci matakin na Amurka ba, tana gargadin cewa irin wannan yarda na iya zama wani abu mai haɗari da ka jaddada cewa gwamnatocin Afirka ba sa iya kare kansu daga matsin lambar ƙasashen waje.

 

Haka kuma EFF ta dage kan cewa wannan mataki na gwamnati na iya buɗe ƙofa ga tsoma bakin ƙasashen waje a nahiyar Afirka nan gaba.

 

Sai dai gwamnatin Najeriya ta kare kanta, tana mai cewa an amince da kaddamar da harin ne bayan tattara bayanai na sirri da kuma tsara dabarun aiki.

Mun nemi taimakon Turkiyya wajen yakar matsalar tsaro a Nijeriya – Shugaba Tinubu

0

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta nemi taimakon kasar Turkiyya wajen yakar matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Nijeriya.

 

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin tattaunawa da wata tawagar kungiyar Kiristoci ta Nijeriya a gidansa da ke jihar Legas.

 

Sanarwar da hadiminsa Bayo Onanuga ya fitar, ta ce ya bukaci samun hadin kai daga kungiyar, musamman wajen hakuri da kuma fahimtar irin matakan da gwamnatinsa ke dauka.

 

Kazalika ya jaddada kudurin kafa ‘yansandan jihohi, a daidai lokacin da gwamnati ke kan aikin hadin gwiwa da kasar Amurka wajen yakar matsalar tsaro, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

An mayar da ‘yan Nijeriya masu gudun hijira 26,000 gida cikin shekarar 2025 – Rahoto

0

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa ‘yan Nijeriya masu gudun hijira sama da 26,000 ne aka mayar gida daga kasashe daban daban.

 

Bayanan rahoton da aka fitar a watan Nuwamban 2025, sun nuna cewa an dawo da su ne daga kasashen Nijar, Chadi da kuma Kamaru da kuma Sudan.

 

Haka kuma, hukumomi sun tabbatar da cewa a halin yanzu akwai ‘yan Nijeriya fiye da dubu 408 da ke zaune a kasashen waje, a yanayi na gudun hijira.

 

Hukumomin sun jingina yawaitar samun hakan da samun rikice-rikice daga ayyukan ta’addanci a sassa daban daban na kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

An yanke wa daurarru sama da 27,000 hukunci a Nijeriya cikin shekarar 2025

0

Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Nijeriya ta bayyana cewa akalla daurarru 27,416 ne aka yanke wa hukunci a fadin kasar cikin shekarar 2025.

 

Ta kuma ce a halin yanzu akwai mutane 50,703 da ke jiran shari’a a daidai lokacin da ake bankwana da 2025.

 

Wannan dai na cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar, wanda ke nuna irin kalubalen cinkoso da ake samu a gidajen yarin da ke fadin kasar, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

 

A hannu guda, hukumar ta NCoS ta nuna damuwa da cewa yawan wadanda ke zaman jiran shari’ar na kasancewa wani nauyi ga gwamnati, musamman ta bangaren kudaden da ake kashewa wajen kula da su.

Akpabio ya ba mata kyautar kwale-kwalen kamun kifi a matsayin barka da Kirsimeti

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio ya bayar da kyautar kwale-kwalen kamun kifi masu amfani da inji guda 10 ga mata a mazabarsa ta Akwa Ibom ta Kudu.

 

Cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na Sanatan ya fitar, Akpabio ya bayar da kyautar ne a garinsa na Ukana, karamar hukumar Essien Udim da ke jihar, a matsayin kyautar barka da ranar Kirsimeti.

 

Sanarwar ta ce an zabo wadanda aka bai wa kyautar ne daga yankunan da suke da koguna, inda ake yawan gudanar da sana’ar kamun kifi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.