Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 62

An yanke wa daurarru sama da 27,000 hukunci a Nijeriya cikin shekarar 2025

0

Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Nijeriya ta bayyana cewa akalla daurarru 27,416 ne aka yanke wa hukunci a fadin kasar cikin shekarar 2025.

 

Ta kuma ce a halin yanzu akwai mutane 50,703 da ke jiran shari’a a daidai lokacin da ake bankwana da 2025.

 

Wannan dai na cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar, wanda ke nuna irin kalubalen cinkoso da ake samu a gidajen yarin da ke fadin kasar, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

 

A hannu guda, hukumar ta NCoS ta nuna damuwa da cewa yawan wadanda ke zaman jiran shari’ar na kasancewa wani nauyi ga gwamnati, musamman ta bangaren kudaden da ake kashewa wajen kula da su.

Akpabio ya ba mata kyautar kwale-kwalen kamun kifi a matsayin barka da Kirsimeti

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio ya bayar da kyautar kwale-kwalen kamun kifi masu amfani da inji guda 10 ga mata a mazabarsa ta Akwa Ibom ta Kudu.

 

Cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na Sanatan ya fitar, Akpabio ya bayar da kyautar ne a garinsa na Ukana, karamar hukumar Essien Udim da ke jihar, a matsayin kyautar barka da ranar Kirsimeti.

 

Sanarwar ta ce an zabo wadanda aka bai wa kyautar ne daga yankunan da suke da koguna, inda ake yawan gudanar da sana’ar kamun kifi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ku kasance cikin shirin ko-ta-kwana – CDS Olufemi ga sojojin Nijeriya

0

Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Olufemi Oluyede ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar wajen ci gaba da yakar ayyukan ta’addanci, yana mai kira ga jami’an sojin su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a kowane lokaci.

 

Olufemi wanda ya samu wakilcin babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi wannan Jan hankali ne yayin bikin ranar Kirsimeti da suka gudanar da runduna ta 8, sashe na 2 na Operation Fansan Yamma a jihar Sokoto.

 

Jaridar Punch ta ruwaito shi yana gargadin cewa ‘yan ta’adda na iya amfani da lokacin bukukuwa wajen kaddamar da hare-hare kan al’umma.

 

Kazalika ya yabawa jami’an sojin musamman wadanda ke bakin daga, yana mai bayyana su a matsayin wani bangon kariya ga ‘yan Nijeriya.

Babu fashi kan aiwatar da dokar haraji a watan Janairun 2026 – Gwamnatin Nijeriya

1

Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen aiwatar da Dokar Haraji ta kasa daga 1 ga Janairu, 2026, duk da ce-ce-ku-cen da ke gudana kan zargin an yi sauye-sauye a cikin dokokin da aka wallafa.

 

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Kudi da Sauye-sauyen Haraji, Mr Taiwo Oyedele, ya bayyana wannan matsaya bayan ya yi wa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu bayani a Legas.

 

Ya ce an tsara wadannan sauye-sauyen ne domin rage wa ‘yan Nijeriya radadi da nauyin rayuwa, ba wai don tara kudaden shiga cikin gaggawa ba.

SGF George Akume ya angwance da tsohuwar matar Ooni na Ife Gimbiya Zainab

0

Sakataren Gwamnatin Nijeriya (SGF), Sanata George Akume, ya auri Sarauniya Zaynab Ngohemba, tsohuwar matar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

 

Jaridar Punch ta ce an bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta hannun wani mamba na iyalan Dajoh, Abraham Double-d Dajoh, ta shafin Facebook.

 

Iyalan Dajoh sun tabbatar da auren tare da tarbar Sarauniya Zaynab a hukumance zuwa gidan iyali da ke Mbakor, Jihar Benue, a wannan watan Disamba.

Jirgin yakin Nijeriya da aka tsare a Burkina Faso ya isa Portugal

0

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta tabbatar da cewa jirgin ta kirar C-130 mai lamba NAF 913 ya isa cibiyar gyara jirage ta OGMA da ke Lisbon lafiya a Portugal a ranar 26 Disamba, 2025.

 

Wannan na zuwa ne bayan da Burkina Faso ta tsare jirgin da ma’aikatansa a baya bisa zargin keta sararin samaniyarta a ranar 8 ga watan Disamba.

 

Rundunar ta ce jirgin ya kammala tafiyar ferry flight bisa sabon tsarin tashi da ka’idojin tsaron jiragen sama, inda ya bi ta Banjul da Casablanca ba tare da wata matsala ba.

 

Kakakin rundunar sojin sama ta Nijeriya Air Commodore Ehimen Ejodame ya bayyana cewa dukkan ma’aikatan suna cikin koshin lafiya, tare da gode wa hukumomin kasashen da aka bi ta cikinsu bisa hadin kai da goyon baya.

An shiga ruɗani bayan fashewar wasu abubuwa a jihar Kwara

0

Al’ummar yankin Offa a jihar Kwara sun shiga fargaba a daren Alhamis bayan jerin fashewar abubuwa masu ƙarfi da suka girgiza wasu sassan garin, lamarin da ya lalata gidaje da shaguna a yankunan Yidi da Adeleke.

 

Jaridar Daily Trust ta ambato shaidu sun ce fashewar ta faru ne da tsakar dare, inda ta bazu har zuwa al’ummomin da ke makwabtaka saidai ba a tabbatar da asarar rai ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

 

An gano wasu abubuwan fashewa da ba su tashi ba, abin da ya ƙara tayar da shakku kan yiwuwar alaƙa da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa na Amurka.

 

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara ta ce ana ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin lamarin.

PDP ta soki gwamnatin Tinubu kan kin sanarwa ‘yan Nijeriya farmakin Amurka

0

Jam’iyyar PDP ta soki Gwamnatin Nijeriya kan yadda ba ta sanar da ’yan kasar game da farmakin saman da Amurka ta kai a Arewa maso Yamma ba sai bayan shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa labarin.

 

Kakakin PDP, Ini Ememobong, ya ce ya dace gwamnati ta fara wayar da kan jama’a game da lamarin, maimakon jiran tabbatar da abin da ya riga ya yadu a kafafen yada labaran ketare.

 

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito PDP na cewa tsarin sadarwar da ke barin ƙasashen waje su fara sanar da ayyukan tsaro a Najeriya na da matuƙar damuwa.

 

Sai dai Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa farmakin hadin gwiwa ne, inda Najeriya ta amince da shi tare da bayar da bayanan sirri, kuma Shugaba Bola Tinubu ya amince da harin.

Sheikh gumi ya soki farmakin da Amurka ta kai ta sama a Najeriya

0

Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya soki farmakin saman da Amurka ta kai kan sansanonin ’yan ta’adda a arewa maso Yammacin Najeriya, yana cewa hakan na iya ƙara rarraba al’umma tare da tauye ikon ƙasar.

 

Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa sojojin Amurka sun kai hare-hare masu tsanani, yayin da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da haɗin gwiwar tsaro da musayar bayanan sirri da Amurka.

 

A wani rubutu da ya wallafa a Facebook, ya nemi gwamnati ta dakatar da haɗin gwiwar soji da Amurka, ta nemi taimakon ƙasashen China, Turkiyya da Pakistan.

 

Ya kuma ce jefa bama-bamai kaɗai ba zai magance ta’addanci ba, yana mai cewa Najeriya na da isassun sojoji don gudanar da ayyukan ƙasarta, tare da zargin cewa hare-haren a Sokoto na iya ƙara tayar da hankali da rarrabuwar kai a ƙasar.

Tinubu ne ya sahale wa Amurka kai hari bayan Nijeriya ta ba da bayanan sirri – Gwamnati

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya amince a kai hare-haren sama da Amurka ta yi kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

 

Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya ce hare-haren hadin gwiwa ne tsakanin kasashen biyu, inda Najeriya ta bayar da muhimman bayanan sirri kuma an aiwatar da su ne bayan samun cikakkiyar amincewar shugaban kasa.

 

Tuggar ya jaddada cewa aikin bai sabawa ikon kasa ba kuma ba ya da nasaba da addini.

 

Gidan talabijin na Channels ya ambato shi ya ce Najeriya kasa ce mai addinai da dama kuma ta na hada gwiwa da abokan hulda irinsu Amurka ne domin yaki da ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

 

A cewar Amurka, an kashe ‘yan ISIS da dama a hare-haren, yayin da AFRICOM ta tabbatar da cewa an yi su ne tare da cikakken hadin kai da hukumomin Najeriya.