Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 65

Hukumar EFCC ta ki bin umurnin kotu inda ta ci-gaba da tsare Malami

0

Ofishin Abubakar Malami, SAN, ya yi tir da yadda EFCC ta ki bin umarnin kotun FCT Abuja na a saki Malami bayan ya cika sharuddan da aka tsara a ranar 23 Disamba, 2025.

A cikin wata sanarwar da ofishin ya fitar, ta ce EFCC ta cigaba da tsare shi fiye da kwanaki 14 ba tare da gurfanar da shi a kotu ba, yayin da take amfani da kafafen watsa labarai wajen yada labarai don lalata masa suna.

Ofishin ya yi kira ga kotu da hukumomin sa ido da su ɗauki mataki cikin gaggawa, sannan ya jaddada cewa babu wata hukuma da ta fi karfin doka.

Ba da jimawa ba kwamitin majalisar wakilan Nijeriya zai kammala binciken dokokin harajin da ake zargin an sauya

0

Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken bambance-bambancen da ake zargi a cikin sabbin dokokin sauya haraji ya yanke shawarar kammala aikinsa da gabatar da rahotonsa ga majalisa cikin gaggawa.

An kafa kwamitin karkashin jagorancin Muktar Aliyu Betara (Borno, APC) bayan ɗan majalisa Abdulsammad Dasuki ya ɗaga batun kan rashin daidaito tsakanin dokokin da majalisar ta amince da su da kuma waɗanda aka wallafa a jaridar hukuma.

Kwamitin ya yi alkawarin gudanar da bincike cikin gaskiya da tsanaki, inda za a gabatar da sakamakon da shawarwari ga majalisar cikin dan lokaci bayan kammala binciken.

Dokokin da ake bincike a kansu sun haɗa da: Dokar Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa, Dokar Hukumar Hada-hadar Haraji ta Ƙasa, Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, da kuma Dokar Haraji ta Nijeriya, waɗanda aka amince da su a majalisar a watan Maris kuma Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kansu a watan Yuni.

Sanata Ndume ya bukaci bincike da dakatar da dokokin haraji saboda zargin sauyin da ke ciki

0

Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da aiwatar da sabbin dokokin sauya haraji da aka tsara fara aiki a watan Janairu, sakamakon ce-ce-ku-ce kan yadda aka tsara dokokin bayan amincewar Majalisar Tarayya.

Ndume ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ja hankalin gwamnati kan rahotannin da ke nuna cewa an canza wasu sassa na dokokin bayan amincewa da su.

Hakazalika ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya kafa kwamitin bincike na musamman domin tantance gaskiyar dokokin da kuma gano sahihancin zargin canje-canjen kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sanatan ya gargadi cewa fara aiwatar da dokokin ba tare da warware zarge-zargen ba zai iya haifar da matsalar inganci da rage amincewar jama’a ga dokokin gwamnati.

Mawaki Davido ya koma jam’iyyar Accord Party, inda kawunsa Gwamnan Osun Adeleke ya koma

0

Mawaki Davido, ya sanar da shirin sa na shiga jam’iyyar Accord, inda zai bi sawun kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke na Osun.

Mawakin ya ce zai kasance a Osogbo a ranar Laraba domin karɓar katin zama mamba na jam’iyyar.

Wannan lamari ya biyo bayan Gwamna Adeleke da ya sanar da barin PDP zuwa jam’iyyar Accord kafin zaɓen gwamna na 2026.

Shirin Davido ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda ake lura da yadda shahararrun mutane ke shiga harkokin siyasa a Nijeriya.

Shugaba Tinubu ya nuna jarumta wajen aiwatar da tsare-tsare masu wahala a 2025 – Jam’iyyar APC

0

Jam’iyyar APC ta ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna jarumtaka ta musamman da jajircewa wajen tafiyar da Nijeriya cikin sauye-sauyen tattalin arziki da na gwamnati masu wahala amma suka zama dole a shekarar 2025.

A cikin rahoton ƙarshe na shekara kan halin ƙasa, wanda Seye Oladejo, Sakataren Yada Labarai na APC na Jihar Legas ya sanya hannu, jam’iyyar ta ce 2025 ta kasance lokacin da ake buƙatar shugabanci mai ƙarfin hali da yanke shawara mai wuya.

Jam’iyyar ta yi suka ga wasu ’yan siyasa da suka yi amfani da wahalhalun sauye-sauyen don nuna Nijeriya a matsayin ƙasa mai gazawa domin cin moriyar siyasa, inda ta ce wannan adawa babu kishin ƙasa sai dai manufar cutar da ƙasa.

Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan zargin kin bin umurnin kotun koli na ba kananan hukumomi kudadensu kai tsaye

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jinkirta aiwatar da hukuncin Kotun Koli da ya umurci Gwamnatin Tarayya ta raba kudaden FAAC kai tsaye ga kananan hukumomi.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook, Atiku ya ce jinkirin ba kawai rashin kulawa bane, har ma yana nuni da nuna kin bin doka domin siyasa. Ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya tana amfani da aiwatar da kundin tsarin mulki a matsayin hanyar tilasta gwamnonin adawa shiga jam’iyyar APC da tabbatar da cewa gwamnonin APC suna ƙarƙashin ikon ta.

Ya kara da cewa, “Hukuncin Kotun Koli ƙarshe ne, ba zaɓi ba. Rashin aiwatarwa kai tsaye karan tsaye ne ga kundin tsarin mulki kuma cin zarafi ne ga alkawarin da Shugaba ya ɗauka ga ’yan Nijeriya.”

Atiku ya jaddada cewa wannan mataki yana jefa kananan hukumomi cikin matsala, yana hana ci-gaban yankuna, da ƙara talauci a matakin ƙasa, inda hanyoyi suka lalace, cibiyoyin lafiya ba sa aiki, kuma albashin ma’aikata bai biya ba.

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya ya bukaci Shugaba Tinubu da ya umarci Lauyan Gwamnatin Tarayya nan da nan ya aiwatar da hukuncin, yana mai cewa rashin yin hakan na nuna cewa mulkin jam’iyya ya fi adalcin tattalin arziki da bin doka muhimmanci, kuma rayuwar ’yan ƙasa ta fi daukar hankali fiye da bukatun siyasa.

‘Yan sanda sun cafke wata daliba ‘yar Nijeriya da ta boye hodar iblis a cikin biredi a Indiya

0

Masu binciken manyan laifuka (Central Crime Branch) a ƙasar Indiya sun cafke wata ’yar Nijeriya mai shekara 29, Olajide Esther Iyanuoluwa, bisa zargin safarar hodar iblis da ta ɓoye gram 121 a cikin biredi.

Jaridar Punch ta ruwaito, an kama Olajide ne a Bengaluru bayan samun bayanan sirri, inda aka ƙiyasta darajar hodar iblis ɗin da aka ƙwato da kusan rupee crore 1.2. An ce ta shigo Indiya da takardar ɗaliba amma ba ta taɓa yin rajista a wata makaranta ba.

’Yan sanda sun ce ta rika sauya matsuguni a Mumbai da kewaye, tana karɓar hodar iblis daga wani mutum da kanta tana kai ma wani ɗan Nijeriya a Bengaluru domin kauce wa shakku.

An gano hodar iblis ɗin ne bayan bincike, inda aka samu ta ɓoye a cikin burodin da aka hurhuda rami aka cika da ƙwayoyin. Daga bisani an kama wanda za a miƙa wa kayan, wanda aka ce an kore shi daga Indiya, yayin da bincike ke ci-gaba domin gano sauran masu hannu a safarar.

Tabarbarewar tsaro ba ta da alaka da gazawar jami’an tsaro sai dai siyasantar da matsalar – Rabi’u Kwankwaso

0

Jagoran Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tabarbarewar tsaro a Nijeriya ba gazawar sojoji ba ce, illa dai rashin ƙwazon shugabannin siyasa.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a Kano yayin ƙaddamar da rundunar Kano State Neighbourhood Watch Corps da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa, inda aka gabatar da jami’ai 2,000 da aka horas domin taimakawa tsaron al’umma.

A cewarsa, sojojin Nijeriya jajirtattu ne kuma kwararru, amma abin da aka rasa shi ne ƙwazon siyasa, musamman daga Babban Kwamandan Rundunonin Tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati ta samar da kayan aiki, makamai da horo ga jami’an tsaro.

Tsohon Ministan Tsaron ya kuma yaba wa gwamnatin Kano kan kafa rundunar tsaron unguwanni, yana mai cewa mataki ne da ya dace domin fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan iyaka da makwabtan jihohin.

Wike ya yi ma Tinubu alkawarin rike masa PDP don kar su ba shi matsala a zaben 2027 – Seyi Makinde

0

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce saɓanin da ke tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya samo asali ne daga furucin Wike na cewa zai “riƙe PDP” domin taimaka wa Shugaba Bola Tinubu sake cin zaɓe a 2027.

Makinde ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Ibadan, inda ya ce ya yi mamaki lokacin da Wike ya faɗi hakan a gaban Shugaba Tinubu, alhali shugaban Nijeriyar bai nema ba kuma bai amince da hakan ba. Ya ce Wike na da ’yancin goyon bayan Tinubu, amma bai kamata ya hana sauran ’yan PDP kare jam’iyyar da dimokuraɗiyya ba.

Sai dai mai taimaka wa Wike kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya caccaki Makinde, yana cewa gwamnan Oyo mutum ne mai bin son zuciyarsa kawai ba tare da biyayya ga jam’iyya ko mutum ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Olayinka ya zargi Makinde da sauya jam’iyya sau da dama saboda muradin kansa, yana mai cewa bayan zaɓen 2027 ma, Makinde zai sake ficewa daga PDP.

Kotu ta amince da a bayar da belin Abubakar Malami 

Babbar Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta amince da belin tsohon ministan shari’ar Nijeriya Abubakar Malami, SAN, wanda ke fuskantar  zarge-zargen cin hanci daga hukumar EFCC.

Umurnin kotun ya fito ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, inda mai shari’a Justice Bello Kawu ya yanke hukuncin amincewa da belin Malami bayan sauraron roƙon gaggawa (motion ex-parte) da lauyansa ya shigar, tare da la’akari da hujjar da aka gabatar a gaban kotu.

Kotun ta umurci Malami da ya miƙa fasfo dinsa na ƙasashen waje, tare da cika sharuddan beli kamar yadda EFCC ta tanada tun da farko. Daga cikin sharuddan akwai bayar da masu tsayawa masa  mutum biyu, ciki har da Darakta Janar na wata hukumar shari’a da kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Augie/Argungu.

Har ila yau, kotun ta amince da sake farfaɗo da sharuddan belin da aka cika a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga Janairu, 2026.