Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 66

INEC ta yi watsi da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki

0

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta amince da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP da Kabiru Turaki ke jagoranta ba, bisa dalilin hukuncin kotu da ke nan daram da kuma batutuwan shari’a da har yanzu ba a kammala ba.

INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 22 ga Disamba, 2025, wadda Sakatariyar hukumar, Dakta Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu. Hukumar ta ce ta karɓi buƙatu daga lauyoyin PDP na neman a amince da kuma sabunta sunayen shugabannin jam’iyyar da aka ce an zaɓa a babban taron ƙasa da aka yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.

Sai dai INEC ta ce bayan nazari, ta gano akwai hukuncin Kotun Tarayya da ke Abuja guda biyu waɗanda suka hana hukumar sa ido, amincewa ko aiwatar da sakamakon taron PDP ɗin, har sai an bi duk umarnin kotu. Hukumar ta jaddada cewa hukuncin kotun na ƙarshe ne kuma wajibi ne ga kowa.

Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara muhawara kan kasafin kudin 2026 na Nairan tiriliyan 58

0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara muhawara kan kasafin kuɗin shekarar 2026, inda shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele daga Ekiti Ta Tsakiya, ya jagoranci tattaunawar kan kudirin da ke neman amincewa da kashe kuɗin har tiriliyan ₦58.47 a shekarar 2026.

Sanata Bamidele ya bayyana hakan ne a zaman majalisar ranar Talata, yana mai cewa kudirin shi ne zai ba da damar aiwatar da kasafin kuɗin 2026 da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Majalisar Ƙasa baki ɗaya a ranar 19 ga Disamba, 2025, wanda a dalilin haka aka ɗauka cewa ya riga ya tsallake karatu na farko.

A cewarsa, dokar kasafin kuɗin tana da matuƙar muhimmanci wajen tafiyar da mulki da kula da tattalin arziki, domin tana sauya manufofin kasafin kuɗin shugaban ƙasa zuwa kuɗaɗen da za a kashe bisa doka. Bamidele ya bayyana cewa kasafin na shekarar 2026 an tsara shi ne bisa sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa domin dawo da daidaito, gyara kura-kurai da ƙarfafa kuɗaɗen gwamnati.

Sanatan ya ƙara da cewa kasafin kuɗin 2026 ba gwaji ba ne, illa kasafi ne na ƙarfafa sauye-sauyen da aka fara, daidaita manyan alamomin tattalin arziki, da hanzarta ci-gaba ta hanyar saka hannun jari na gwamnati a muhimman fannoni.

Gwamnatin Nijeriya za ta rufe shafukan sada zumunta na ‘yan ta’adda

1

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa hukumomin tsaro na Nijeriya na aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano tare da rufe asusun da ‘yan ta’adda da masu laifi ke amfani da su wajen tallata ayyukansu da tara kuɗi.

Babban Daraktan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka, ya bayyana hakan ne a taron ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja, inda ya ce ‘yan ta’adda na amfani da kafafe irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X wajen nuna hare-harensu, baje kayayyakin da suka sace, da sadarwa da magoya bayansu.

Ya ce hukumomin tsaro sun yi tarurruka da dama da wadannan kamfanoni domin magance wallafe-wallafe da asusun da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Laka ya ƙara da cewa dabarun ‘yan ta’adda na ci gaba da sauyawa, ciki har da amfani da sunaye na bogi da asusun da ba a tantance ba, amma ya jaddada cewa hukumomin tsaro na ci gaba da daidaita dabarunsu domin tinkarar sabbin barazanar tsaro a Nijeriya.

Lambobin shaidar zama dan kasa da na CAC ne za su koma lambobin haraji daga 1 ga watan Janairu – FIRS

0

Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya (FIRS) ta bayyana cewa lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da Hukumar NIMC ke bayarwa ta zama kai tsaye lambar haraji (Tax ID) ga daidaikun ‘yan Nijeriya, a ƙarƙashin sabbin dokokin haraji.

FIRS ta sanar da hakan ne a wani shirin wayar da kai kan sabbin dokokin haraji da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, inda ta ce ‘yan kasuwa masu rijista ma ba za su ƙara buƙatar wata lambar haraji ta daban ba, domin lambar rijistar CAC (RC) za ta zama lambar harajinsu.

Hukumar ta ce Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya (Nigeria Tax Administration Act – NTAA), wadda za ta fara aiki daga Janairu 2026, ta tanadi amfani da Tax ID a wasu mu’amaloli, ciki har da mallakar asusun banki, amma ta jaddada cewa wannan ba sabon tsari ba ne tun daga Dokar Kuɗi ta 2019.

A cewar FIRS, sabon tsarin zai haɗa dukkan lambobin haraji zuwa guda ɗaya, rage maimaituwa, toshe hanyoyin gujewa biyan haraji, tare da inganta gaskiya da adalci a tsarin karɓar haraji a Nijeriya.

‘Yan majalisa wakilai 6 daga Jihar Rivers sun sauya sheka zuwa APC

0

‘Yan Majalisar Wakilai 6 daga Jihar Rivers sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda suka danganta matakin da rikicin shugabanci da rabuwar kai da ke addabar PDP.

Wadanda suka sauya sheka sun hada da Dumnamene Dekor, Cyril Hart Godwin, Solomon Bob, Victor Obuzor, Blessing Amadi da Felix Uche, inda Kakakin Majalisar, Hon. Abbas Tajudeen, ya karanta wasiƙunsu a zaman majalisar ranar Talata.

‘Yan majalisar sun ce rikice-rikicen cikin gida a PDP sun hana su cimma muradunsu na siyasa da na majalisa. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ‘yan majalisa 4 daga Rivers sun koma APC daga PDP da LP, lamarin da ya ƙara raunana jam’iyyun adawa a jihar.

Masu lura da siyasa na alakanta wannan sauya sheka da sabon jeri na siyasa a Rivers bayan Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya koma APC.

Da wannan sabon ci-gaba, ‘yan PDP uku kaɗai suka rage daga Rivers a Majalisar Wakilai, wato Shugaban ‘Yan Adawa Kingsley Chinda, Kelechi Nworgu da Anderson Allison Igbiks.

Jihohin Yobe da Benue ne suka fi samun yawan ‘yan gudun hijira a Nijeriya – NHRC

0

Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta bayyana cewa Jihohin Yobe da Benue ne ke kan gaba wajen yawan ‘yan gudun hijira a Nijeriya a tsakiyar shekarar 2025.

Rahoton hukumar ya nuna cewa Yobe ta samu ‘yan gudun hijira 2,047, yayin da Benue ke da 1,850, lamarin da ke nuna tsananin matsalar tsaro a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Babban Sakataren NHRC, Dr Tony Ojukwu (SAN), ya bayyana hakan ne yayin gabatar da kundin bayanan hukumar, kamar yadda kafar dillancin labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito.

Ojukwu ya ce jimillar ‘yan gudun hijira da aka yi rajista sun kai 9,290 a jihohi 11, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya, da ta’addanci, wanda ya lalata rayuwar jama’a da hanyoyin samun abinci.

Dr Ojukwu ya ƙara da cewa yara ne suka fi shan wahala, inda suka kai kashi 82 cikin 100 na mutanen da abin ya shafa. Ya kuma ce akwai masu neman mafaka 215 da ke fuskantar matsalar rajista a Taraba da Cross River, tare da ‘yan gudun hijira 583, galibinsu a waɗannan jihohin.

Wadanda suka yi garkuwa da ‘yan Mauludi 28 a jihar Plateau na neman kudin fansa N1.5m kan kowane mutum

0

‘Yan bindiga da ake zargin sace mutane 28 a ƙauyen Zak, karamar hukumar Wase, Bashar, jihar Filato, sun tuntubi iyalan wadanda suka yi garkuwa da su suna neman a biya su kuɗin fansa na Naira miliyan 1.5 ga kowane mutum.

An sace mutanen ne a daren Lahadi yayin da suke kan hanyarsu zuwa bikin Maulidi a ƙauyen Sabon Layi da ke Bashar. An kai musu hari a mota, aka sace su, aka bar motar a wurin.

Ibrahim Musa, ɗaya daga cikin ‘yan uwa, ya shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun tabbatar musu cewa suna cikin koshin lafiya amma sun dage a biya N1.5m ga kowane mutum. Yace sun roƙi ’yan bindigan su yi tausayi saboda iyalan fursunonin ba su da ƙarfin wadannan kuɗin.

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Filato ta tabbatar da lamarin a ranar Litinin, tana mai cewa suna kan binciken al’amarin. Al’ummar yankin sun bukaci ƙarin tsaro don rage satar mutane, fashi da makami, da satar shanu a Karamar Hukumar ta Wase.

Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar dokokin haraji

0

Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji, tana mai cewa rikice-rikicen da suka taso sun girgiza amincewar jama’a da tsarin dokar ƙasar.

Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
Kungiyar ta ce zargin sauya dokokin bayan Majalisar Tarayya ta amince da su ya tayar da manyan tambayoyi kan gaskiya, tsari da sahihancin aikin majalisa.

Wannan dai ya biyo bayan abin da jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Abdulsammad Dasuki (PDP, Sokoto), ya yi ikirarin cewa dokokin da aka zartar sun bambanta da waɗanda aka fitar a cikin kundin gwamnati. Tun daga lokacin, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da wasu ‘yan majalisa ke kira da a dakatar da dokokin.

A cewar Osigwe, dokoki masu girma irin haka dole ne su fito ta hanya mai tsabta da ɗaukar alhaki. NBA ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa domin yin cikakken bincike a fili, domin kare tsarin mulki kwanciyar hankalin tattalin arziki da kuma tabbatar da bin doka da oda, tare da dawo da cikakkiyar amincewar jama’a ga aikin majalisa.

Babu wasu sauye-sauye a dokokin haraji – Gwamnatin Nijeriya

0

Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa salo guda ɗaya ne kacal sahihi na sabbin dokokin gyaran haraji da aka rattaba wa hannu, tare da musanta zargin cewa an sauya dokokin bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana haka a taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar an Abuja.

Ministan ya ce dokokin sun bi dukkan matakan doka a Majalisar Tarayya kafin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba musu hannu, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da su kamar yadda aka tsara. Sai dai ya ce Majalisar Tarayya na duba koken da aka shigar game da zargin bambanci tsakanin abin da aka amince da shi da abin da aka wallafa a mujallar gwamnati.

Rigimar ta biyo bayan korafin dan Majalisar Wakilai Abdussamad Dasuki na Kebbe/Tambuwal, wanda ya ce akwai wasu sashe a dokokin da ba a tattauna ba amma aka saka su. Duk da sukar da wasu ‘yan siyasa suka yi, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, gwamnati ta ce dokokin za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, yayin da shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce jinkirta aiwatarwa na iya jefa Nijeriya cikin matsala.

Tsohon Sakataren kudi na PDP na kasa ya fice daga jam’iyyar

0

Tsohon Shugaban Matasa na Ƙasa kuma Sakataren Kuɗi na Jam’iyyar PDP, Rt. Hon. Abdullahi Hussaini MaiBasira, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

MaiBasira ya bayyana hakan ne a wata wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 22 ga Disamba, wadda ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na mazabarsa ta Tudun Wada ta Kudu, Karamar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja, inda ya ce murabus ɗin ya fara aiki nan take.

A cikin wasiƙar, MaiBasira ya nuna godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi ya yi aiki a matakai daban-daban tsawon shekaru, yana mai bayyana shawarar barin PDP a matsayin mai matuƙar wahala. Duk da haka, bai fayyace dalilin murabus ɗin ba, sai dai ya ambaci abin da ya kira “yanayi bayyanannu da matsin lamba na zahiri” a cikin jam’iyyar.

Ficewar tasa na da tasiri a siyasar PDP a Jihar Neja, la’akari da rawar da ya taka a harkokin matasa da tsare-tsaren jam’iyya a matakin jiha da ƙasa.

Ko da yake bai bayyana inda zai dosa ba, majiyoyi daga jam’iyyar na hasashen cewa MaiBasira na iya komawa Jam’iyyar ADC, musamman ganin alaƙarsa da goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.