Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 67

Kananan hukumomi sun bukaci a rika biyan kudadensu kai tsaye daga asusun Gwamnatin Tarayya

0

Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi (NULGE) sun mara wa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu baya kan shirin tilasta biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Tinubu ya yi gargaɗin cewa zai fitar da umarni na shugaban ƙasa idan gwamnonin jihohi suka ƙi bin hukuncin Kotun Ƙoli.

Kotun Ƙoli a ranar 11 ga Yuli, 2024 ta haramta wa jihohi riƙe ko sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi, tare da bayyana tsarin kwamitin rikon ƙwarya a matsayin saɓa wa Kundin Tsarin Mulki. Duk da haka, har yanzu ba a aiwatar da hukuncin gaba ɗaya ba.

Binciken The PUNCH ya nuna cewa jihohi sun cigaba da sarrafa Naira tiriliyan 7.43 na kuɗaɗen ƙananan hukumomi daga Yuli 2024 zuwa Disamba 2025, duk da umarnin biyan kuɗaɗen kai tsaye.

Gwamnatin Nijeriya ta mika daliban da aka ceto ga gwamnan Neja tare da alkawarin sake bude makarantun da aka rufe fadin kasar

0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa za ta sake buɗe dukkan makarantun da aka rufe a Nijeriya sakamakon hare-haren ’yan ta’adda da sace ɗalibai.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya sanar da hakan a Minna yayin tarbar ɗalibai 130 da malamansu da aka ceto daga makarantar St. Mary’s da ke Agwara, Jihar Neja.

Shugaban ƙasar, ta bakin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce an samu nasarar ceto su ne ta hanyar haɗin gwiwar sojoji, ’yan sanda da DSS, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ɗauki matakan tsaro na gaggawa tare da haɗa shugabannin al’umma domin kare makarantu da rayukan jama’a.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, ya nuna godiya ga Shugaban ƙasa, mai ba shi shawara kan tsaro da hukumomin tsaro bisa nasarar ceto dukkan ɗalibai da malamansu lafiya, yana mai cewa wannan nasara ta musamman ce wadda za ta ba iyaye da al’umma kwarin gwiwa.

An fitar da jihohi 4 a Gasar Kokawar Nijar ta 2025

Kwana na uku da fara gasar kokawar gargajiya a Nijar tuni an yi waje da jihohi hudu daga cikin takwas na kasar daga jerin wanda za su dauki takobi

Jihohin hudu sun hada da Agadez, Diffa, Tillaberi da babban birnin Niamey

Cikin jimillar ‘yan kokawa 80 da suka fito daga jihohi takwas na kasar ya zuwa wannan rana ta uku, 12 suka rage.

Jihar Maradi ce ke kan gaba da yawan ‘yan kokawar cikin wadanda ba su fadin ba inda take da biyar yayin da jihar Tahoua ke biya mata da mutum hudu, sai jihar Dosso da biyu sai kuma ta karshe Zinder da mutum daya.

Tuni zakaran gasar kokawar na bara Abba Ibrahim na babban birnin Yamai ya sha kasa tun a kwana na biyu na gasar ta 2025.

Ya kamata a canza salon yadda ake yakar ‘yan bindiga a Nijeriya

Daga: Farfesa Usman Yusuf
Litinin : 22 Disamba 2025

Ban taɓa gudu ko ja da baya ba ko nuna wata fargaba wajen bayyana matsayina a kan yaƙin da ake kan yi da ‘yan fashin daji da aka kwashe shekara goma sha biyu ke nan ana ta fama.

Wannan ‘yancina ne na faɗin albarkacin bakina a matsayina na ɗan ƙasa da lamarin ya shafe ni kai tsaye nake cikinsa tsundum ba wai mai rungume hannu ya zura ido kawai ko wanda ya ƙware wajen haddasa fitina ba.

Na yi wannan ɗan rubutu ne domin jaddada matsayin da na kwashe fiye da shekara 6 ina nanatawa a cikin rubuce-rubucena masu yawan gaske da hirarrakin da aka yi da ni a gidajen rediyo da talabijin daban-daban.

Mun san cewa waɗannan fitintinu na ‘yan fashin daji sun somo ne a matsayin matsaloli na zamantakewa da wasu dalilai na cikin gida suka haifar, sanadiyyar halayyar wasu ‘yan siyasa da ba su san ciwon kan su ba, suka yi sake suka yi watsi da lamarin har ƙaramar magana ta zama babba, har take nema a yanzu haka ta jefa duka ƙasar cikin mawuyacin hali.

A shekarun nan goma sha biyu, martanin da gwamnatocin jihohi da na tarayya suke mayarwa shi ne na ci gaba da cusa soja cikin wannan taƙaddama da mummunan sakamako.

Akwai lokacin da yake takamaiman aikin da ya kamata a ce na soja ne, amma ba ta amfani da ƙarfin soja ba ne za a iya shawo kan wannan matsala ta ‘yan fashin daji. Saboda a tarihi na taƙaddama, ko faɗace-faɗace irin wannan, ba a taɓa samun nasara a fagen daga ba.

Na sha faɗi ina nanatawa cewa duka matsalolin, matsaloli ne na cikin gida kuma dole ne maganinsu yana nan a cikin gida ba sai an je da nisa ba.

Wasu manyan tsare-tsare daga Abuja ba tare da an sanya masu ruwa da tsaki na cikin gida ba, ba su taɓa haifar da ɗa mai ido ba tsawon shekaru 12 da suka wuce, kuma ba za su taɓa yin wani tasiri ba.

Saboda haka, ci gaba da maimaita abu guda a yi tsammanin za a samu wani sakamako daban tamkar ana iya cewa mafarki ake yi.

Gaskiyar maganar shine, aikin ya yi wa sojojinmu yawa don ana ta tuttura su duka jihohi 36 na ƙasar nan har da Babban Birnin Tarayya Abuja. Sojoji na ci gaba da gajiya da jigata saboda daukar tsawon lokaci suna kai-komo har wasun su suna fita hayyacin su, wasu kuma su koma suna mu’amala da miyagun ƙwayoyi.

Dole ne mu saurari koke-koken neman taimako daga ‘ya’yanmu wanda sune mayaƙanmu da suke sadaukar da rayuwarsu a kowacce wayewar garin Allah saboda mu.

Babu yadda za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan al’ummar da ke da tsananin rashawa irin na Nijeriya, ga rashin shugabanci na gari, ga yunwa da gwamnati ta ƙaƙaba wa jama’a, ga matsananciyar fatara, ga yara ba sa zuwa makaranta, ga matasa ba aikin yi, ga mu’amala da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, ga ƙaruwar gilmawar ƙananan makamai, ga gubar ƙiyayya da rashin yarda tsakanin mabiya addinai daban-daban, da ƙabilanci da ya yi katutu da kuma jin haushin juna da ‘yan siyasa da ba su san ciwon kan su ba, suke ci gaba da rurutawa.

Zuba jari ba ɗan kaɗan ba ga shawo kan waɗannan matsaloli na zamantakewa zai fi taimakawa wajen rage kashe kuɗaɗe da ceto rayuwa maimakon ci gaba da zubar da jini da ci gaba da kashe maƙudan kuɗi ɓangaren soja.

Rashin sa Sarakunan Gargajiya, da Malamai, da Dattawa da shugabannin al’umma cikin neman maslahar wannan matsalar tun da farko, babban kuskure ne da ke buƙatar a yi gyara a kan sa.

Tattaunawa ta sulhu da sasanci halastacciyar hanya ce ta warware dukkan wani rikici, da ya kamata a bi ta ɗoɗar domin kai wa ga dauwamammen zama lafiya.

Za a iya kwance ɗamara da karɓe makaman ‘yan fashin daji, da ‘yan bijilante da dukkan sauran ‘yan ta’adda da ke riƙe da makamai ne, bayan tattaunawa da sulhu na tsakani da Allah, da ke iya maido da yarda da amana da tsohuwar ‘yan uwantaka da shekaru da aka kwashe ana zubar da jinin juna babu gaira babu dalili suka ɗaiɗaita.

A daidai lokacin da wannan yaƙin ke shiga shekararta ta goma sha uku a shekarar da ke shirin kankama ta 2026, ya kamata Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan ƙasar nan ya faɗaɗa tintiɓa tare da ba da umarnin a canza tako wato a canza salon yadda ake wannan yaƙi da ta’addamci.

‘Yan Nijeriya sun gaji da wannan yaƙi da zubar da jini da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Usman Yusuf, Farfesa ne Ɓangaren Cututtukan Da Suka Shafi Jini da kuma Dashen Ɓargo.

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta shawo kan rikicin diflomasiyya tsakaninta da Amurka

0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa matsalar diflomasiyya da ta taso tsakanin Nijeriya da Amurka kwanan nan ta shawo kanta bayan tattaunawa mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

Ministan yada Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana haka a taron manema labarai na karshen shekara a Abuja ranar Litinin inda ya ce rikicin ya samo asali ne bayan maganganun Shugaba Donald Trump da suka yi zargin kisan kiristoci a Nijeriya da yiwuwar shiga da sojoji, amma an warware ta hanyar tattaunawa.

Idris ya ce Nijeriya ta gudanar da al’amuran cikin natsuwa da ka’ida, wanda ya haifar da dangantaka mafi karfi da Amurka. Ya nuna sabuwar yarjejeniya kan hadin gwiwar kiwon lafiya a matsayin hujja ta kyakkyawar alaka.

Wannan yarjejeniya ta shekaru biyar ta kai dala biliyan 5.1, inda Amurka za ta bayar da dala biliyan 2.1 a matsayin tallafi, Nijeriya kuma ta bada dala biliyan 3 don inganta tsarin kiwon lafiya.

Ministan ya ce wannan yarjejeniya za ta inganta samar da lafiya, ceci rayuka, da jawo karin zuba jari a kasar. Ya kuma kara da cewa ci-gaban ya nuna cewa damuwa kan tabarbarewar dangantaka tsakanin Nijeriya da Amurka ba su da tushe.

Kasafin kudin Shugaba Tinubu na 2026 tarkon bashi ne ba gyara ba – Jam’iyyar ADC

0

Jam’iyyar ADC ta soki kudirin kasafin kuɗin shekarar 2026 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar, tana mai cewa kasafin tarkon bashi ne da aka lullube da sunan gyara, wanda ke dogaro da karɓar rance fiye da kima da kuma hasashen kudaden shiga da ba su da tabbas.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, ADC ta ce kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 58.18 bai kawo sabon abu ba illa ci-gaba da abin da ta kira sakacin tafiyar da kuɗin gwamnati, inda aka gabatar da irin kasafin shekarun 2024 da 2025 da ba a aiwatar da yawansu ba.

Jam’iyyar ta ce duk da ikirarin gwamnati na kashe Naira tiriliyan 25.68 kan ayyukan raya ƙasa, gibin kasafin da ya kai Naira tiriliyan 23.85 na nuna cewa kusan dukkan ayyukan za a yi su ne da bashi mai tsada, tana mai gargadin cewa hakan na iya jefa Nijeriya cikin ƙarin matsin tattalin arziki da ɗaure makomar ’ya’ya masu zuwa.

Ghana ta mayar da karuwai da karin masu aikata lafuka 42 a Nijeriya

0

Akalla ’yan Nijeriya 42 ne aka kora daga yankin Ashanti na ƙasar Ghana bayan hukuncin kotuna kan laifuffuka da suka haɗa da karuwanci, zamba da wasu laifuka makamantansu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan yankin Ashanti, Frank Amoakohene, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce an kuma kori ’yan Kamaru 13, ’yan Ivory Coast 3, ’yan Burkina Faso 3 da ’yan Benin 7, wanda ya kai adadin mutanen da abin ya shafa 68 baki ɗaya.

Ministan ya yaba wa Hukumar Shige da Ficen Ghana bisa yadda ta aiwatar da dokoki tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam.

Matakin ya zo ne yayin da ake ƙara samun rahotannin tsananta sa ido da kama ’yan Nijeriya a ƙasashen waje kamar yadda rahoton jaridar Punch ta ruwaito.

Akpabio ya garzaya kotun koli kan batun dakatar da Sanata Natasha

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya garzaya Kotun Koli kan rikicin shari’a da ya biyo bayan dakatar da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar.

Takardun kotu sun nuna cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce ƙarar ba ta inganta ba saboda karya ƙa’idojin kotu, ciki har da amfani da rubutu da tazara da ba su dace ba, wuce adadin shafuka da aka kayyade, da kuma rashin neman izinin kotu.

Binciken jaridar PUNCH ya nuna cewa kotun ta yanke hukuncin ne bisa doka, ba bisa son rai ba.

Duk da haka, Akpabio ya nemi Kotun Koli ta soke hukuncin, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jama’a, inda wasu masana shari’a ke ganin ba ruwan shugaban Majalisar Dattawa ya shiga shari’ar kai tsaye. Rikicin ya kuma kara fitowa fili sakamakon sabanin siyasa da ke tsakaninsa da Sanata Natasha, wadda ta shahara wajen sukar shugabancin Majalisar.

Ana ci gaba da matsa lamba kan batun dokar haraji da za ta fara aiki a sabuwar shekarar 2026 a Nijeriya

0

Ana ci gaba da samun matsin lamba daga ’yan Majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da a dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji da aka shirya fara aiki da su a ranar 1 ga Janairu, 2026, sakamakon zargin cewa an sauya wasu sassa bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.

Wani dan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki (PDP, Sokoto), ya tayar da batun a zaman Majalisa ranar Laraba, inda ya ce akwai bambance-bambance tsakanin dokokin da ’yan Majalisa suka amince da su da kuma wadanda daga bisani aka wallafa a cikin jaridar gwamnati (gazette).

Sai dai Majalisar Dattawa da Ofishin Babban Lauyan Tarayya ba su yi martani ba kan zargin, lokacin da jaridar Daily Trust ta tuntube su. Dokokin harajin guda hudu sun hada da Dokar Hukumar Haraji ta Kasa, Dokar Hukumar Hadin Gwiwar Haraji, Dokar Gudanar da Haraji a Nijeriya da Dokar Haraji ta Nijeriya.

Dokokin dai an amince da su ne a Majalisar Tarayya a watan Maris, aka fitar da bayanan kuri’u a Mayu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma ya sanya hannu a watan Yuni, yayin da aka wallafa su a jaridar gwamnati a ranar 26 ga Yuni. Sai dai binciken Daily Trust ya nuna akwai manyan sabani tsakanin dokokin da aka amince da su da wadanda aka wallafa.

A wani bangare, wani dan Majalisar Wakilai, Mansur Manu Soro (Bauchi), ya ce bincikensa ya tabbatar da cewa an samu “manyan sauye-sauye masu muhimmanci” a dokokin da aka wallafa. Ya ce shi da wasu ’yan Majalisa na shirin kai batun gaban Majalisa domin neman dakatar da aiwatar da dokokin har sai an warware matsalar.

Shugaba Trump ya janye jakadan Amurka a Nijeriya

0

Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya umarci a janye Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, tare da wasu ƙwararrun jakadu daga muƙamansu, a wani mataki da ake cewa na da nufin daidaita wakilcin diflomasiyyar Amurka da manufofin “America First.”

Rahoton Politico ya ce jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da cewa yawancin jakadun da abin ya shafa an naɗa su ne a zamanin tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, kuma wa’adinsu zai ƙare nan da Janairu. An ce za su iya komawa Washington domin wasu ayyuka idan suna so.

Rahoton ya nuna cewa Afirka ce ta fi shafa, inda jakadu daga ƙasashe 13 ciki har da Nijeriya, Burundi, Kamaru, Côte d’Ivoire, Senegal da Uganda suka fuskanci janyewa. Haka kuma an shafi yankunan Asiya-Pasifik, Turai, Gabas ta Tsakiya, Kudancin Asiya da Latin Amurka.

A wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce wannan al’ada ce a kowace gwamnati, tana mai jaddada cewa jakadu na aiki ne bisa yardar shugaban ƙasa, kuma hakki ne nasa ya zaɓi wakilan da za su aiwatar da manufofinsa na Amurka Farko.