Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 68

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana barayin daji a matsayin ‘yan ta’adda

0

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyin tada kayar baya a matsayin ‘yan ta’adda, mataki da ke nuna tsanantawa a yaki da satar mutane, hare-hare kan manoma, da tashin hankali a al’ummomi.

Wannan sanarwar ta fito daga Ministan Harkokin Labarai, Mohammed Idris, yayin taron manema labarai na karshen shekara an Abuja.

Ministan ya bayyana cewa daga yanzu, duk wanda ke garkuwa da yara, kai hari kan manoma, ko tayar da tarzoma a cikin al’umma za a dauke shi a matsayin dan ta’adda.

Hakazalika ya ce wannan sabon tsari zai karfafa musayar bayanai da hadin gwiwar aiki tsakanin hukumomin tsaro, wanda zai sa daukar mataki ya zama cikin sauri da tasiri.

Idris ya jaddada cewa hadin gwiwar hukumomi ya riga ya haifar da sakamako, inda a shekarar 2025 aka kama wasu daga cikin ‘yan fashi da ake nema a duniya baki daya ta hanyar ayyukan tsaro masu hadaka.

Jinkirta dokokin haraji zai cutar da ‘yan kasuwa, ma’aikata da masu karamin karfi – Taiwo Oyedele

0

Shugaban Kwamitin Gyaran Manufofin Kuɗi da Haraji na Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya gargaɗi cewa jinkirta aiwatar da sabbin dokokin haraji bayan 1 ga Janairu, 2026 na iya jefa ma’aikata da ’yan kasuwa cikin matsala a faɗin Nijeriya, musamman a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan bambancin dokokin da Majalisa ta amince da su da waɗanda aka wallafa.

Oyedele ya ce idan ba a aiwatar da dokokin ba, kashi 98 cikin 100 na ma’aikata za su cigaba da fuskantar haraji fiye da kima, yayin da ’yan kasuwa kuma za su rasa rangwamen da dokokin ya tanada, su cigaba da biyan haraji masu yawa, lamarin da ke ƙara musu nauyi tare da tsadar rayuwa ta hanyar boyayyen VAT kan abinci, lafiya da ilimi.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels, Oyedele ya ce maimakon dakatar da dokokin gaba ɗaya, ya fi dacewa a gano sassan da ake zargin an sauya su, a aiwatar da abin da Majalisa ta amince da shi, sannan a gyara kura-kuran da ke ciki ta hanyar gyaran doka, yana mai amincewa cewa akwai wasu sassa da ke buƙatar gyara ta hannun Shugaban Ƙasa.

APC a Kano ta caccaki Kwankwaso kan kalamansa na sa ido ga INEC gabanin zaben 2027

0

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yi watsi da kalaman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, inda ya ce jam’iyyarsa za ta sanya ido kan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) gabanin zaɓen 2027.

Da yake magana da jaridar PUNCH a ranar Lahadi, kakakin APC a Kano, Ahmad Aruwa, ya bayyana kalaman Kwankwaso a matsayin “marasa ma’ana kuma ba dole ba,” yana mai cewa tsohon gwamnan ya riga ya rasa tasiri a harkokin siyasar Nijeriya. Aruwa ya ce Kwankwaso ba shi ne halastaccen jagoran NNPP ba, kuma ba ɗan takarar kowace jam’iyya ba ne a halin yanzu.

A cewarsa, APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun riga sun kammala dukkan shirye-shiryen da za su tabbatar da nasara a Kano, yana mai cewa jam’iyyar na da cikakken ƙwarin gwiwa ga INEC.

Aruwa ya zargi Kwankwaso da ƙoƙarin raunana amincewar jama’a ga tsarin zaɓe, tare da kira ga al’umma da su yi watsi da kalamansa.

Jam’iyyar PDP tsagin Turaki ta nemi kotu ta umurci ‘yan sanda su bude sakatariyar jam’iyyar

0

Jam’iyyar PDP bangaren Kabiru Turaki (SAN) ta shigar da ƙara a Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman umarni da zai tilasta wa ’yan sanda su buɗe tare da ficewa daga sakatariyar ƙasa ta jam’iyyar da ke Wadata Plaza.

An rufe sakatariyar ne tun watan Nuwamba bayan rikici tsakanin bangaren Turaki da bangaren da ke goyon bayan Ministan FCT, Nyesom Wike, sakamakon shirya taruka a rana guda, lamarin da ya janyo tsoma bakin ’yan sanda da kulle ginin.

Bangaren Turaki ya ce kullen ya hana shugabancin jam’iyyar gudanar da ayyukanta, inda suke roƙon kotu ta umarci ’yan sanda su cire shingaye tare da hana su sake kulle ofisoshin PDP a Abuja da jihohi 36 har sai an yanke hukunci.

Rooney na hasashen Declan Rice zai zamo kyaftin na tawagar kwallon kafar Ingila

0

Tsohon ɗan wasan Manchester United da Ingila, Wayne Rooney, ya yaba wa tauraron Arsenal, Declan Rice, inda ya ce yana ganin shi a matsayin kyaftin ɗin tawagar Ingila nan gaba bayan rawar gani da ya taka a wasan Premier League da suka doke Everton da ci 1-0.

Rooney, wanda ya kalli wasan a fili, ya ce Rice ya nuna cikakken shugabanci a tsakiyar fili, yana tsara wasa tare da nuna jajircewa da basira. A cewarsa, Rice na da halayen da suka dace da ɗaukar ragamar kyaftan daga Harry Kane nan gaba.

Kamar yadda BBC Sport ta ruwaito, Rooney ya ce: “A gare ni, shi ne mutumin da ke jiran ranar da Harry Kane zai ajiye takalmansa. Ƙwazonsa da halayensa sun bambanta shi da sauran ’yan wasa.”

Rooney ya ƙara da cewa yadda Rice ke taka leda daga kare baya, zuwa raba kwallo a tsakiyar fili, har zuwa kai hari na nuna irin cikakken ɗan wasan da Ingila ke buƙata. Ya jaddada cewa Rice ɗan wasa ne da ake ƙauna, kuma yana da muhimmanci sosai ga makomar tawagar ƙasa.

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutun Kirsimeti da Boxing Day

0

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana Alhamis 25 ga Disamba da Juma’a 26 ga Disamba, 2025 a matsayin ranakun hutun Kirsimeti da Boxing Day, tare da ayyana Alhamis 1 ga Janairu, 2026 domin bikin Sabuwar Shekara.

Sanarwar ta fito ne cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Ciki, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a madadin Ministan Harkokin Ciki, Olubunmi Tunji-Ojo, a ranar Litinin.

Ministan ya buƙaci ’yan Nijeriya su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen tunani kan ƙauna, zaman lafiya da sadaukarwa, tare da yin addu’o’i domin zaman lafiya, ingantaccen tsaro da ci gaban ƙasa, yana kuma yi wa al’umma fatan barka da Kirsimeti da sabuwar shekara mai albarka.

Dangote ya yi barazanar neman hakkin Biliyan 100 a kotu bisa kalaman batanci da wani dan kasuwa ya yi masa

0

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bai wa wani ɗan kasuwa mazaunin Kaduna, Kailani Mohammed, wa’adin kwana bakwai da ya janye kalaman da ya yi tare da neman afuwa a bayyane, ko kuma ya fuskanci ƙarar bata suna ta Naira biliyan 100 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakan na cikin wata wasiƙa da lauyan Dangote, Ogwu Onoja (SAN), ya rubuta a ranar 20 ga Disamba, 2025, inda ya zargi Mohammed da yin kalaman ƙarya da rashin tushe kan tushen dukiyar Dangote da kuma zarginsa da “harkokin kasuwanci marasa tsafta” a shekarun 1980.

An ce kalaman sun fito ne a wata hira da TrustTV a ranar 17 ga Disamba, 2025, yayin da Mohammed ke tsokaci kan wani ƙorafi da aka kai wa ICPC game da tsohon shugaban NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed.

Lauyoyin Dangote sun ce kalaman sun ɓata masa suna matuƙa a cikin gida da ƙasashen waje, suna mai jaddada cewa Dangote sanannen ɗan kasuwa ne da ya gina dukiyarsa ta hanyar aiki tuƙuru da gaskiya, kuma duk wata magana akasin haka bata suna ce kai tsaye.

CDD ta horas da ‘yan jarida a Katsina kan yaki da labaran karya

0

Cibiyar bunkasa dimokradiyya ta CDD ta horas da ‘yan jarida a jihar Katsina kan aiki mai inganci.

CDD ta ce wannan na a wani yunkuri na karfafa kwarewa a aikin jarida tare da inganta rahoto kan ka’ida da gaskiya.

Jami’ar kula daga cibiyar ta CDD, Ms Chioma Valerie, ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin bai wa ‘yan jarida dabarun da za su taimaka musu wajen yaki da labaran karya da kuma tafiyar da bayanai cikin kwarewa.
Ta ce daya daga cikin muhimman sakamakon bitar shi ne samar da ‘yan jarida da za su iya taimakawa wajen gina al’umma mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta hanyar rahoto mai bin ka’idojin da’a da gaskiya.

A yayin bitar, an yi bayani dalla-dalla kan ma’anar tantance gaskiyar labari (fact-checking), manufarsa da muhimmancinsa, tare da bambance shi da tantance sahihancin bayani (verification), da yadda dukkan su ke taimakawa wajen samar da rahoto mai inganci.
Haka kuma, an yi gargadi kan illolin wallafa bayanan da ba a tantance ba, inda aka bayyana irin matsalolin da labaran karya ka iya jefa ‘yan jarida da al’umma a ciki.

‘Yan bindiga sun halaka mutum 1,sun kuma mutane 5 a Zamfara

0

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda suka halaka mutum ɗaya tare da sace mutane biyar, a daren Asabar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen tun cikin dare har zuwa wayewar gari.

Wani mazaunin ƙauyen, Malam Sani, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen da dare, inda suka halaka mutum ɗaya, suka sace mutane, sannan suka harbe wani mutum da ya samu mummunan rauni, wanda aka kai shi Asibitin koyarwa na Sokoto domin jinya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro suna kokari domin kubutar da wadanda aka sace kuma nan ba da jimawa ba za a ji labari mai daɗi.

‘Yan sanda sun kama wata mata a ake zargi da garkuwa da kanta

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wata matar aure mai shekaru 26 tare da wani mutum mai shekaru 30, bisa zargin yin garkuwa da kanta da neman kudin fansa miliyan 2.5 daga hannun mijinta.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cafke mutanen a wata sanarwa da ta fitar a Legas, inda ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa a 24 ga watan Nuwamba daga wajen mijin matar, inda ya ce an sace matarsa.

Ta ce an sanar da ‘yansanda cewa masu garkuwar sun fara neman kudin fansa Naira miliyan 10, daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 3, kuma bayan biyan Naira miliyan 2.5, ba a saki matar ba, lamarin da ya sa rundunar ta tura jami’anta don bincike,inda a nan ne suka gano abinda ake zargi a kanta.