Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 69

Fadar mai alfarma sarkin musulmi ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar 1 ga watan Rajab 1447AH

0

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, tare da haɗin gwiwar kwamitin duban wata suka fitar a ranar Asabar, 20 ga Disamba, 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Rajab ba daga ko ina a fadin Nijeriya a daren Asabar wanda ya yi daidai da 29 ga watan Jumada Sani, don haka watan ya cika kwana 30.

Sakamakon haka, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya amince da rahoton tare da ayyana Litinin a matsayin 1 ga watan Rajab.

An mika tutar rundunar haɗin gwiwa ta kasashen AES, Nijar, Mali da Burkina Faso

0

Shugaban mulkin sojin Mali kuma shugaban kungiyar AES, Janar Assimi Goïta, ya jagoranci bikin miƙa tutar rundunar haɗin gwiwar ta kasashen AES a wani biki na musamman da aka gudanar a Bamako a ranar Asabar, 20 Disamba, 2025.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an tsaro da wakilan ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar, inda aka bayyana miƙa tutar a matsayin matakin da ke nuna fara aiki tare na rundunar haɗin gwiwar AES domin tsaurara tsaro da kare yankin Sahel.

Matakin na da nufin inganta tsaro tare da aiki da jami’an hadin gwiwa na kasashen domin fuskantar matsalar tsaro da ke addabar yankin.

Mai neman yi wa kansa kofar rago ne kawai zai yi takara da Tinubu a 2027 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa mai neman yi wa kansa kofar ragone kawai zai tsaya takarar shugaban kasa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Shettima ya fadi hakan ne a yayin taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC da ya gudana a ranar Juma’a,inda ya jaddada cewa duk da dimokuradiyya ta ba kowane dan kasa damar tsayawa takara, yanayin siyasar da ke tafe zuwa 2027, ya bayyana karara cewa shugaba Tinubu ke da nasara.

A cewarsa, irin nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu, tare da karfin jam’iyyar APC da goyon bayan da shugaban kasa ke da shi a fadin Nijeriya, sun nuna cewa ‘yan adawa ba su da wata dama ta mai kyau a zabe mai zuwa.

Jam’iyyar PDP a Jigawa ta soki dakatar da Sule Lamido, daga kwamitin amintattu na jam’iyyar

0

Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta nuna rashin jin daɗi kan matakin dakatar da Sule Lamido, CON, daga ayyukan kwamitin amintattu na jam’iyyar,tana mai kira da a gaggauta janye hukuncin.

A wata sanarwa da shugaban PDP na Jigawa, Babandi Ibrahim Gumel, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana dakatarwar a matsayin rashin adalci,kuma hakan zai ƙara rarraba kan jam’iyya, musamman a lokacin da ake buƙatar haɗin kai domin fuskantar jam’iyyar APC mai mulki.

Ya ce zargin da aka jingina wa tsohon gwamnan na halartar wasu tarurruka da ake ganin barazana ne ga haɗin kan jam’iyyar ba hujja ba ce, domin Lamido ya yi abin da doka da kundin tsarin mulki suka ba shi dama.

Gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka AFCON za ta koma duk bayan shekaru 4 – CAF

0

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, ta sanar da cewa gasar cin kofin kasashen Afrika AFCON, za ta koma duk bayan shekara huɗu bayan kammala gasar da aka tsara a 2028.

Shugaban na CAF, Patrice Motsepe, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin ganawa da manema labarai a Rabat, da ke Maroko, inda ya ce sauyin yana cikin gyaran tsarin wasannin ƙwallon ƙafa a nahiyar domin ya dace da jadawalin wasannin duniya.

Motsepe ya bayyana cewa duk da AFCON na taimaka wa ƙungiyoyin ƙasashe ta fuskar kuɗaɗe, CAF ta yanke shawarar ƙaddamar da gasar African Nations League wadda za a rika yi kowace shekara, makamanciyar UEFA Nations League.

Tinubu ya ziyarci jihar Borno domin bude ayyuka

Shugaba Tinubu, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin ƙaddamar da manyan ayyuka da halartar bikin auren ɗan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ali Modu Sheriff.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito cewa jirgin shugaba Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Janar Muhammadu Buhari, Maiduguri, da misalin karfe 12:55 na rana.

Ana sa ran ziyarar za ta haɗa da ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar da ta tarayya suka aiwatar, tare da halartar taron bikin aure kafin shugaban ƙasar ya ci gaba da sauran tafiye-tafiyen da aka shirya zai yi.

‘Yan bindiga za su dandana kudarsu a shekarar 2026 – Kwamandan sojin Nijeriya, Birgediya Janar Adebisi Onasan

0

Kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta Guwards Brigade , Birgediya Janar Adebisi Onasanya, ya gargaɗi ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a Abuja da sauran wurare cewa za su dandana kudarsu a shekarar 2026, domin za a ƙara matsa musu lamba ta fuskar tsaro.

Janar Onasanya ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Asabar, yayin ganawa da manema labarai a Aso Rock.

Ya bayyana cewa shekarar 2025 ta kasance mai matuƙar ƙalubale, sakamakon ƙarin buƙatun tsaurara tsaro fiye da aikin kare shugabanni kaɗai.

A cewarsa, rundunar ta tsabtace yankuna a wurare daban daban a Abuja da wasu sassan jihar Neja, inda aka kama masu laifi, aka kwato makamai, tare wasu ’yan ta’adda,ya ce nasarorin sun samu ne ta hanyar haɗin gwiwa da ’yan sanda, NSCDC, DSS, da kuma goyon bayan sojin ruwa da sojin sama.

Wata kotu a Amurka ta daure wani dan Nijeriya shekaru 20 a gidan yari bisa laifin zambar kudin tallafi

0

Wata kotun Amurka ta sami wani ɗan ƙasar Nijeriya da laifi kan zambar kuɗin tallafi (charity fraud) da ya kai dala miliyan 7.5, lamarin ya jawo masa hukuncin daurin shekaru 20.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bayanan shari’a, sun nuna cewa an tuhumi mutumin ne da laifukan damfara ta hanyar yanar gizo da kuma satar bayanan mutane, inda ake zargin ya yi amfani da kungiyoyin jin ƙai na bogi domin karkatar da kuɗaɗen da aka tara.

Kotun ta ce laifukan sun shafi yaudarar masu bayar da gudummawa, tare da amfani da hanyoyin banki da na intanet wajen canja kuɗaɗen ba bisa ka’ida ba.

Ci gaban matasan Nijeriya shi ne abinda shugaba Tinubu ya saka a gaba – Ministan Sadarwa

0

Ministan sadarwa Dr. Bosun Tijani, ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru domin gina rayuwar matasa, al’umma da kuma makomar ƙasar baki ɗaya.

Dr. Tijani ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin buɗe gasar kwallon kwando ta matasa daya gudana a babban birnin jihar Ogun.

Ministan ya ce gasar, wadda ta zo daidai da bukukuwan ƙarshen shekara, an tsara ta ne domin samar da nishaɗi da haɗin kai, inda matasa za su haɗu, tare da kulla alaƙa mai ɗorewa ta hanyar aiki tare.

Ya ce, idan aka tallafa wa matasa a irin waɗannan wurare, suna bayyana basirarsu ba kawai a wasanni ba, har ma a matsayin shugabanni da masu ba da gudummawa ga al’umma.

Ya kara da cewa irin wadannan abubuwa sun yi daidai da manufar shugaba Tinubu na gina makomar matasan Nijeriya.

Da na kammala wa’adina zan daina shiga harkar siyasa – Gwamnan Abia

0

Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya jaddada cewa zai yi ritaya daga siyasa bayan kammala wa’adinsa a matsayin gwamna, yana mai cewa baya da burin neman shugabancin Nijeriya, mataimakin shugaba ko Sanata a nan gaba.

Dr. Otti ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a fadar gwamnatin jihar, yayin da yake mayar da martani a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, bayan ziyararsa ga Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali na Sokoto.

Ya ce ya fada a baya kuma yanzu nana maimaitawa bayan ya gama wa’adinsa na gwamna, zan yi ritaya, ba zai kara neman wata takara ba.