Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 71

Majalisar wakilai ta amince da hukuncin shekaru 2 a gidan gyaran hali ga masu saye da sayar da kuri’u

0

Majalisar Wakilai ta amince da gyare-gyare masu tsanani ga dokar zabe, inda aka sanya hukunci mafi tsauri ga saye da sayar da kuri’u, wanda ya hada da aƙalla shekaru 2 a gidan gyaran hali ko tarar Naira miliyan 5, ko duka biyun, tare da hana mutum tsayawa takara na tsawon shekaru 10.

Hukunci mafi tsauri ya shafi saye da sayar da kuri’u da katin zabe, inda yanzu aka kara hukunci fiye da wanda ake da shi a baya na N500,000 ko shekaru biyu a gidan yari. An kuma amince da sabbin dokoki kan tura sakamakon zabe daga kowace rumfa ta hanyar na’urar IREV a lokaci guda da tattara sakamakon hannu, domin karfafa gaskiya da sahihancin zabe.

Bugu da kari, an kara hukunci ga shugabannin rumfunan zabe da suka karya ka’idoji wajen kirga, bayyana, ko aika sakamakon rumfa, inda sabon hukunci ya tanadi aƙalla tarar N500,000 ko watanni shida a gidan gyaran hali, ko duka biyun.

An amince da sakin kudaden zabe ga INEC aƙalla shekara ɗaya kafin babban zabe, da kuma amfani da katin zabe mai QR code don tabbatar da masu kada kuri’a kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majalisar wakilan Nijeriya ta kafa kwamitin bincike kan zargin sauya dokokin haraji

0

Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya kafa kwamitin wucin-gadi mai mambobi bakwai domin binciken zargin sabani tsakanin kudirin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su da kuma nau’ukan da aka rattaba hannu a kansu tare da wallafawa a jaridar gwamnati.

Hon. Muktar Aliyu Betara zai jagorancin kwamitin, yayin da sauran mambobin suka hada da tsohon Mataimakin Kakaki, Ahmed Idris Wase, da Sada Soli, James Abiodun Faleke, Fred Agbedi, Babajimi Benson da kuma Iduma Igariwey.

Matakin ya biyo bayan korafin da dan majalisa mai wakiltar Sokoto, Hon. Abdulsammad Dasuki (PDP), ya gabatar inda ya ce dokokin harajin da aka wallafa ba su yi daidai da abin da ‘yan majalisa suka tattauna kuma suka amince da shi ba, lamarin da ya bayyana a matsayin karya tsarin majalisa da kundin tsarin mulki.

Dasuki ya ce bayan kwashe kwanaki yana kwatanta rubuce-rubucen dokokin da aka wallafa da bayanan kuri’u da kuma sigar da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka amince da ita, ya gano bambance-bambance masu yawa, yana mai cewa abin da aka wallafa ba shi ne abin da aka zartas ba.

Kotu ta hana Abubakar Malami beli

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince hukumar EFCC ta ci gaba da tsare tsohon Ministan Shari’a kuma Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN).

Mai shari’a Babangida Hassan ya yi watsi da bukatar beli da Malami ya shigar, yana mai cewa tsarewar na gudana ne bisa sahihin umarnin da wata kotu mai matsayi ta daya ta bayar a baya.

A cewar sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, lauyan Malami ya yi ikirarin cewa an tsare Malami ba bisa ka’ida ba, amma lauyan EFCC ya shaida wa kotu cewa Mai shari’a S. C. Oriji ya bayar da umurnin hakan kamar yadda dokar ACJA ta tanada.

Rahotanni sun ce Malami na tsare tun ranar 8 ga Disamba bayan ya kasa cika sharuddan beli da EFCC ta gindaya, yayin da ake bincikensa kan zarge-zarge 18 da suka hada da cin zarafin ofis da zargin tallafa wa ta’addanci.

Kotu ta amince ta bai wa Ngige beli tare da sharaɗin nemo babban jami’in gwamnati da zai tsaya masa

0

Babbar Kotun Abuja da ke Gwarinpa, ta amince tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya cigaba da cin gajiyar belin da hukumar EFCC ta ba shi tun da farko.

Alkaliyar kotun, Mai shari’a Maryam Hassan, ta bayar da wannan hukunci ne yayin yanke shawara kan bukatar beli da lauyan Ngige, Barista Patrick Ikwueto (SAN), ya shigar a madadinsa.

Kotun ta umarci Ngige da ya gabatar da mai tsaya masa wanda dole ne ya kasance darakta a aikin Gwamnatin Tarayya kuma mai fili. Haka kuma, kotun ta ce dole ne mai tsayawar ya ajiye takardun filin da kuma takardun tafiyarsa a gaban kotu har sai Ngige ya karbo fasfonsa na kasa da kasa.

Tun da farko, EFCC ta ba Ngige beli ne bisa amincewar kansa, inda ta umarce shi da ya mika takardun tafiyarsa tare da gabatar da mai tsaya masa guda daya.

Akpabio yana nan garas cikin koshin lafiya – Hadiminsa

0

Mai ba Shugaban Majalisar Dattawa shawara kan sadarwa, Kenny Okolugbo, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ba shi da lafiya.

Okolugbo ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a shirin Morning Brief na Channels TV, inda ya ce Akpabio lafiyarsa kalau kuma yana ci-gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum a majalisa.

Ya kwatanta jita-jitar da irin wadda aka taba yadawa kan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, inda aka ce ba shi da lafiya amma washegari aka gan shi yana kaddamar da ayyuka a bainar jama’a.

Okolugbo ya bukaci a sanya tsari mai tsauri kan kafafen sada zumunta domin dakile yada labaran karya, yana mai cewa doka ta hana yada bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba.

Sufurin jiragen cikin gida a Nijeriya na daga cikin mafi arha a duniya – Shugaban kamfanin United Airlines

0

Shugaban kamfanin jiragen United Airlines Limited, Farfesa Obiora Okonkwo, ya ce duk da koke-koken fasinjoji kan tsadar tikitin jirgi, zirga-zirgar jiragen cikin gida a Nijeriya na daga cikin mafi arha a duniya.

Okonkwo, wanda shi ne kakakin kamfanonin jiragen sama a Nijeriya, ya bayyana haka ne a shirin Morning Brief na Channels TV, inda ya ce kamfanonin jirgi na aiki ne a karkashin matsin tattalin arziki mai tsanani, amma har yanzu suna kokarin rike farashi a kasa idan aka kwatanta da sauran kasashe.

A cewarsa, kamfanonin jirage a duniya na amfani da jirage iri daya kuma suna biyan ma’aikata kusan iri daya, na Nijeriya na fuskantar manyan kudade kamar haraji da yawa, bashi mai tsananin ruwa, da kuma kashe-kashen da ake biya da dalar Amurka.

Ya karyata zargin cewa kamfanonin jirgi na yin tsauraran farashi da gangan, yana mai cewa karin kudin tikiti da ake gani a yanzu ya samo asali ne daga karuwar bukatar tafiya a lokacin bukukuwan karshen shekara, kamar yadda ake gani a sauran kasashen duniya.

Magoya bayan Buhari za su ci gaba da faɗa wa Gwamnatin Tinubu gaskiya domin tabbatar adalci – Alhassan Ado Doguwa

0

Dan Majalisar Wakilai daga Kano kuma jagoran ’yan Arewa a Majalisar, Alhassan Ado Doguwa, ya ce magoya bayan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari za su cigaba da “faɗin gaskiya ga masu mulki” domin tabbatar da ɗorewar APC gabanin zaɓen 2027.

Doguwa ya bayyana hakan ne an Abuja yayin ƙaddamar da littafin tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, inda ya ce biyayya ga jam’iyya ba ya na nufin shiru idan abubuwa ba su tafiya daidai ba. Ya ce hakan zai taimaka wa jam’iyyar kada ta rasa kusanci da jama’a kafin zaɓe.

Ya jaddada cewa Buhari ya rasu a matsayin cikakken mamba na APC, yana mai cewa wannan muhimmin abin koyi ne ga magoya bayansa, musamman a Arewa. A cewarsa, ’yan Buhari za su cigaba da kare muradun talakawa da marasa ƙarfi kamar yadda tsohon shugaban ya yi.

Doguwa ya ƙara da cewa Arewa za ta ci gaba da kasancewa a dunkule a siyasa, inda malamai da sarakuna za su taka rawa wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa shigarsu cikin harkokin mulki.

Kungiyar tarayyar Turai za ta karfafa hadin guiwar tsaro da Nijeriya

0

Kungiyar tarayyar Turai (EU) da Nijeriya na ɗaukar sabbin matakai domin ƙarfafa dangantakarsu ta tsaro, a wani yunƙuri na fuskantar kalubalen tsaro da ke ƙara rikitarwa a ƙasar.

Jakadan EU a Nijeriya da ECOWAS, Gautier Mignot, ya bayyana haka ne a Abuja yayin ziyarar girmamawa da ya kai wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, inda ya taya shi murna kan sabon muƙaminsa.

Mignot ya jaddada muhimmancin Nijeriya ga EU, yana mai cewa ƙasashe 19 daga cikin 27 na EU na da ofisoshin jakadanci a Nijeriya, tare da tabbatar da ci-gaba da tallafin EU wajen magance matsalolin tsaro.

Ya ƙara da cewa tallafin EU ba na soji kaɗai ba ne, har da shirye-shiryen zaman lafiya, hana rikici, inganta shugabanci da bunƙasa hukumomi, musamman a wannan lokaci mai sarkakiya ga Nijeriya.

Kiris ya rage na ajiye mukamina na minista a lokacin Buhari – Lai Mohammed

0

Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa ya kusan yin murabus a wani lokaci da ya kira mafi wahala a lokacin mulkin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya bayyana haka ne a Abuja yayin ƙaddamar da littafinsa mai taken “Headlines & Soundbites,” inda ya ce kasancewarsa a tsakiyar harkokin gwamnati na tsawon shekaru takwas ya ɗora masa nauyin fayyace gaskiya da gyara fahimtar da aka yi kuskure game da mulkin Buhari.

Mohammed ya ce littafin ya bayyana yadda aka tafiyar da sadarwar gwamnati a lokutan rikici, labaran ƙarya da matsin lamba, yana mai jaddada cewa ‘yan Afirka su ne ya kamata su ba da labarin kansu.

A taron, Ministan Yaɗa Labarai na yanzu, Mohammed Idris, ya yaba da rawar da Lai Mohammed ya taka, yayin da Halima Buhari ta ce mahaifinta yana sane da suka da yabon da ake yi wa gwamnatinsa a lokacin mulki.

Eng Faruk Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar NMDPRA

Shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta sahale masa nada sabbin shugabannin hukumomin kula da man fetur bayan da Injiniya Farouk Ahmed, ya yi murabus a matsayin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya, tare da takwaransa Gbenga Komolafe, shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama (NUPRC).

Dukkaninsu tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada su a shekarar 2021, bayan kafa hukumomin karkashin Dokar Man Fetur ta PIA.

Wannan na zuwa ne bayan zargin da attajirin dan kasuwa Aliko Dangote ya yi wa Farouk Ahmed, na rayuwa fiye da karfin albashin ma’aikacin gwamnati, musamman dangane da kudaden da ake zargin ya kashe wajen karatun ’ya’yansa a kasar Switzerland.

Zargin ya haifar da muhawara Dangote ya hakikance cewa akwai bukatar bincike inda ya gabatar da korafi a gaban Hukumar ICPC.

Sai dai a cikin sanarwar ta fito ne daga Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce Shugaba Tinubu ya nada Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban NMDPRA, tare da  Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin shugabar NUPRC.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance tare da amincewa da nadin sababbin shugabannin manyan hukumomin kula da harkokin man fetur da iskar gas na kasa.