Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 72

FIFA ta sanya $60 a matsayin kudin tikitin kallon kofin duniya na 2026

0
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ƙaddamar da sabon rukuni na tikiti a dalar Amurka 60 ga kowane ɗayan wasannin 104 na Gasar Kofin Duniya ta 2026 a Amurka, Kanada da Mexico, bayan korafin magoya baya kan tsadar tikiti.
FIFA ta ce tikitin na $60 za a keɓe shi ne ga masu goyon bayan ƙungiyoyi da suka cancanta, kuma zai zama kashi 10 cikin ɗari na rabon kowace ƙungiyar ƙasa.
An bayyana cewa tsarin an tsara shi ne domin taimaka wa magoya baya masu biye da ƙungiyoyinsu a gasar.
Sai dai ƙungiyar magoya baya ta Football Supporters Europe (FSE) ta ce tikitin bai isa ba, tana mai cewa mafi yawancin magoya baya har yanzu za su ci gaba da biyan tsadar tikiti fiye da kowace gasar da ta gabata.
Haka kuma an yi suka kan rashin samar da tikitai na musamman ga masu nakasa da abokan tafiyarsu.

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a Ingila

0

Ƙungiyar British Medical Association (BMA) ta tabbatar da ci gaba da gudanar da yajin aiki, bayan kashi 83 cikin ɗari na mambobinta sun amince da a kuri’ar intanet, duk da sabon tayin da gwamnati ta gabatar.

Yajin aikin likitocin da aka fi sani da resident doctors (masu neman kwarewa) zai fara ne da karfe 7:00 na safiyar Laraba.

Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya bayyana takaicinsa, yana mai kiran matakin da “rashin ɗa’a”, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar matsin lamba daga cutar mura (flu) a kasar.

Gwamnati ta ce sabon tayin bai shafi karin albashi ba, tana mai cewa albashin likitocin ya riga ya ƙaru da kusan kashi 30 cikin ɗari cikin shekaru uku, yayin da BMA ke jaddada cewa albashin su ya ragu idan aka yi la’akari da hauhawar farashi tun 2008.

Tsohon Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya yi ritaya

0
Tauraron ƙwallon ƙafa Ahmed Musa ya sanar da yin murabus daga buga wa Najeriya ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa, bayan shekara 15 yana taka leda da Super Eagles.
Musa ya bayyana hakan ne ta cikin saƙon da ya wallafa a kafafen sada zumunta ranar Laraba, inda ya ce ya yanke shawarar ne bayan dogon tunani, yana mai nuna alfahari da wakiltar Najeriya tsawon shekaru.
Dan wasan mai shekaru 33 shi ne dan wasa mafi yawan bugawa Najeriya wasa (caps) guda 111, kuma yana daga cikin ’yan wasan zamani da suka fi samun nasara a tarihin Super Eagles.
Ahmed Musa ya kasance cikin tawagar da ta lashe Kofin Nahiyar Afirka AFCON a 2013, sannan ya kafa tarihi a Kofin Duniya inda ya zama dan Najeriya na farko da ya ci kwallaye fiye da guda a wasa daya, kana kuma ya zura kwallo a Kofin Duniya biyu (2014 da 2018).

Mutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgi a jihar Imo

0

Mutane huɗu sun tsira daga hatsarin jirgin Cessna 172 na kamfanin Skypower Express da ya yi saukar gaggawa (crash-landing) a Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe da ke Owerri, Jihar Imo, da yammacin Talata.

Hukumar Nigerian Safety Investigation Bureau (NSIB) ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 6:58 na yamma yayin da jirgin ke kokarin sauka a kan hanyar tashi da saukar jirgi (Runway 17).

Jirgin mai lambar rajista 5N-ASR na kan hanyarsa ne daga Kaduna zuwa Port Harcourt kafin matukan jirgin su yi gaggawar shawarar karkata zuwa Owerri.

Hukumar kiyaye afkuwar hadduran ta bayyana cewa jami’an tsaro da na agajin gaggawa na filin jirgin sun kai dauki cikin hanzari, inda aka ceto dukkan mutanen da ke cikin jirgin, ba tare da tashin wuta ba.

Rahoton ya ce biyu daga cikin matukan jirgin suna cikin koshin lafiya, yayin da sauran biyun da suka suma tun farko aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Tinubu da Ministan Kudin Nijeriya sun yi baki biyu kan kudin shigar 2025

Ministan Kuɗi kuma na Nijeriya, Wale Edun, ya saɓa wa furucin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce gwamnatin tarayya ba ta kai burin kudaden shiga na 2025 ba.

Edun ya bayyana cewa zuwa yanzu gwamnati ta samu naira tiriliyan 10.7, ne kacal daga cikin naira tiriliyan 40.8 da aka yi hasashen samu a shekarar 2025.

Tun da farko, Tinubu ya shaida wa jama’a cewa Najeriya ta kai burin kudaden shiga na 2025 tun watan Agusta, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta ƙara dogaro da rancen kuɗi wajen aiwatar da kasafin kuɗi ba.

Sai dai bayanin Edun ya nuna cewa akwai gagarumin gibi a kudaden shiga na bana, lamarin da ke sake tayar da hankula kan ɗorewar harkokin kuɗin gwamnatin Najeriya.

Trump ya haramta wa al’ummar Nijar bizar shiga Amurka

0
Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗaɗa haramcin shiga Amurka, inda aka hana karin ‘yan ƙasashe biyar.
Fadar White House ta ce an ɗauki wannan mataki ne don kare tsaron Amurka, kuma dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga Janairu.
Cikakken haramcin shiga ƙasar zai shafi ‘yan Burkina Faso, Mali, Nijar, Sudan ta Kudu da Syria.

Sabbin dokokin haraji za su kawo sauƙi ga talaka mai karamin karfi – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kwantar wa ’yan Najeriya hankali kan sabbin dokokin haraji da za a fara aiwatarwa a 2026, yana mai cewa za su amfanar da talakawa, masu ƙaramin albashi da ƙananan ’yan kasuwa.

Tinubu ya ce dokokin ba za su shafi abinci, magunguna, ilimi, noma da sufuri daga ba, tare da rage nauyin haraji ga ’yan kasuwa, yana ƙara da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Jaridar Punch ta ruwaito saƙon shugaban ƙasar ya fito ne ta hannun Shugaban Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS), Zaccheus Adedeji, inda Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka sun zama wajibi domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.

Jagororin NLC sun hadu a Abuja domin zanga-zanga matsalar tsaro

Mambobin ƙungiyar kwadago ta kasa NLC sun fara taruwa a hedikwatar NLC da ke Abuja domin gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan ƙaruwar matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Daga cikin manyan shugabannin da suka halarci taron akwai shugaban NLC, Joe Ajaero, tare da abokan hulɗa daga ƙungiyoyin farar hula.

Haka kuma, Omoyele Sowore da mambobin ƙungiyarsa ta Revolution Now Movement na daga cikin fitattun mutane da aka gani a wurin.

Rahotanni sun nuna cewa an jibge jami’an tsaro a yankin, ciki har da ’yan sanda, Civil Defence, da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) domin tabbatar da tsaro.

Tun da farko, Ajaero ya jaddada cewa ba za su fasa zanga-zangar ba, yana mai cewa manufarta ita ce ja hankalin gwamnati kan mummunan tasirin rashin tsaro ga rayuwar al’umma da tattalin arzikin ƙasa.

Kotu a Kano ta tura matar da ta yi ajalin diyar kishiyarta shekaru 10 a gidan yari

0

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zama a Kano Municipal ta yankewa wata mace mai suna Hafsa Umar hukuncin daurin shekara 10 a gidan gyaran hali bayan ta same ta da laifin ajalin ’yar mijinta.

Kotun ta saurari cewa Hafsa ta yi wa yarinyar duka ne bayan zargin ta da satar kuli-kuli, inda masu gabatar da ƙara suka bayyana cewa dukan ya wuce kima har ya jawo mutuwar yarinyar.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce a yayin shari’ar, lauyar gwamnati Barrista Hafsa Adam da Barrista Jamilu Abubakar sun gabatar da shaidu da hujjoji domin tabbatar da laifin wadda ake tuhuma, yayin da bangaren kariya ya gabatar da shaidu biyu.

Da take yanke hukunci, Mai shari’a Aisha Mahmud ta ce ɓangaren ƙara ya tabbatar da laifin wanda ake tuhuma ba tare da shakka ba.

Alkalin kotun ta bayyana cewa laifin ya saba wa Sashe na 226 na Kundin Hukunta Laifuka (Penal Code), tare da yanke mata hukuncin shekara 10 a gidan gyaran hali.

Super Eagles ta fara farfado da burinta na zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026

0
Hukumar kwallon kafar Nijeriya ta fara dawo da burin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta shigar da ƙorafi kan zargin tawagar DR Congo
da coge a ‘yan wasan da ta yi wasannin share fagen Kofin Duniya na 2026 da su.
NFF ta ce wasu ‘yan wasan da suka sauya ƙasa na riƙe da shaidar ƙasa biyu, abin da kundin tsarin mulkin DR Congo bai yarda da shi ba.
Lamarin da wasu ke tunanin ya iya sake buɗe wa Super Eagles hanyar zuwa gasar da za a yi a Amurka, Kanada da Mexico.