Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 70

Wani jirgin kasa ya murkushe Giwaye bakwai a Indiya

0

Wani jirgin kasa ya buge garken giwaye a yankin arewa maso gabashin Indiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar giwaye bakwai nan take, kamar yadda jami’ai a kasar suka sanar a ranar Asabar.

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke tafiya a kan layin dogo, inda giwayen suka tsallaka hanyar, abin da ya haifar da faruwar lamarin, a cewar jami’an gwamnatin kasar.

Jami’an sun ce ana gudanar da bincike domin gano dalilin hatsarin, tare da duba matakan kare dabbobin daji a yankin, musamman a wuraren da layin dogo ke ratsawa kusa da gandun daji.

Dan wasan kungiyar Real Madrid Endrick zai koma Olympique Lyon

0

Matashin ɗan wasan dan kasar Brazil, Endrick, na dab da komawa Olympique Lyon a matsayin aro, inda ake sa ran yarjejeniyar za ta kammala nan ba da jimawa ba.

Babu zaɓin saye a cikin yarjejeniyar, kuma Endrick zai koma Real Madrid a watan Yunin 2026 bayan kammala zamansa na aro a kungiyar.

Wannan mataki na zuwa ne domin ba Endrick damar samun ƙarin dama da gogewa a manyan gasanni kafin dawowarsa Santiago Bernabéu.

INEC ta shiga tsakani kan rikicin shugabanci a PDP

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta shiga tsakani kan rikicin shugabancin PDP, inda ta gayyaci bangarorin jam’iyyar biyu zuwa hedikwatarta da ke Abuja a ranar Juma’a.

 

Taron ya hada bangaren da Tanimu Turaki ke jagoranta da kuma bangaren Abdulrahman Mohammed, wanda ke samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

 

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar INEC Farfesa Joash Amupitan ya ce kiran bangarorin biyu ya zama wajibi ne sakamakon ta’azzarar rikicin cikin gida a jam’iyyar ta PDP.

 

Bayan gabatar da jawabi an shiga taron sirri, inda ake sa ran samun sasanci tsakanin bangarorin da ke rikici da juna bayan haka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

APC ta yi wa Gwamnan jihar Plateau maraba da shiga cikinta

0

Jam’iyyar APC reshen jihar Plateau ta bayyana yi wa Gwamnan jihar Caleb Mutfwang maraba da shiga cikinta, bayan ficewa daga jam‘iyyar PDP.

 

Sakataren jam’iyyar Shitu Bamaiyi ne ya bayyana wa jaridar Punch haka, yayin tattaunawa a garin Jos.

 

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai jam’iyyar APC ta bakin shugabanta na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ta bayyana ficewar gwamnan daga PDP tare da komawa cikinta, yayin taronta a Abuja.

 

A cewar jam’iyyar, za ta ci gaba da bai wa gwamnan dukkanin wani goyon baya da yake bukata a tafiyarsa ta siyasa, tare da cewa kofa a bude take ga duk mai bukatar shiga tafiyar.

Tinubu ya jaddada wa Amurka kudurin kafa ‘yansandan jihohi a Nijeriya

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudurinsa na kafa ‘yansandan jihohi a Nijeriya, yana mai cewa ya shaida hakan ga Amurka da sauran kawayen Nijeriya na Turai.

 

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar APC a Abuja, inda ya nanata bukatar gwamnoni su sakar wa kananan hukumomi ‘yancinsu na kashe kudade.

 

Tinubu ya ce wajibi ne a samar da jami’an don tabbatar da tsaron cikin gida da kuma inganta shugabanci, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majalisar dokokin Nijeriya ta kayyade adadin kudin za a kashe wajen kamfe

0

Majalisar dokokin Nijeriya ta kayyade Naira biliyan 10 ga masu takarar shugaban kasa da Naira biliyan 3 ga masu takarar Gwamna a matsayin adadin kudin da za a kashe wajen yakin neman zabe a kasar.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na daga cikin kudurin gyaran dokar zabe ta shekarar 2025, bayan yin la’akari da rahoton kwamitin da ke kula da harkokin zabe na majalisar ya gabatar karkashin jagorancin Adebayo Balogun.

 

Kazalika an amincewa masu neman kujerar Sanatoci su kashe Naira miliyan 500 sabanin miliyan 100 a baya, sai kuma ‘yan majalisar wakilai Naira miliyan 250 daga miliyan 70.

 

Ga majalisun jihohi kuwa, Naira miliyan 100 aka amince daga miliyan 30, sai masu neman shugabannin kananan hukumomi Naira miliyan 60 daga miliyan 30, baya ga kansiloli da ya kasance Naira miliyan 10 daga miliyan 5.

Sojojin Nijeriya sun dakile harin ‘yan bindiga a jihar Borno

0

Rundunar sojin Nijeriya karkashin shirin ‘Operation Hadin Kai’ ta samu nasarar dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka shirya kaddamarwa a yankin Bitta daga tsaunukan Mandara a jihar Borno.

 

Yayin gumurzun dai sojojin sun hallaka ‘yan ta’adda da dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta hannun Laftanar Kanal Sani Uba a shafinta na X, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren Alhamis, inda sojojin suka gano motsin ‘yan ta’addan zuwa yankin.

 

Bayan fatattakar su, sanarwar ta kuma ce an samu nasarar kwato tarin makamai da sauran kayayyakin da ‘yan bindigar ke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare kan al’umma.

DCL Hausa na Neman Ma’aikata a Kano (Full-Time)

 

DCL Hausa na gayyatar ƙwararru masu jajircewa domin cike guraben aiki na cikakken lokaci (full-time) a ofishinta da ke Kano. Ana neman mutane masu kwarewa, bin ka’ida, da iya aiki cikin lokaci.

Guraben Aiki da ake nema

  • Mai Gyaran Bidiyo (Video Editor)
  • Mai Rahoto na Kauyuka (Rural Reporter)

Mai Gyaran Bidiyo (Video Editor)

Wuri: Jihar Kano
Nau’in Aiki: Cikakken aiki (Full-Time, a ofis)

Sharuddan Aiki

  • Mazaunin Jihar Kano
  • Ƙwarewa wajen gyaran bidiyo
  • Iya amfani da Adobe Premiere Pro da Canva
  • Kwarewar haɗa rahotanni da labaran bidiyo (na gajere da na dogon lokaci)
  • Iya aiki cikin lokaci da bin tsarin aiki
  • Lokacin zuwa ofis (awanni 8 a rana, kwana 5 a mako)

👉 Cike bayananka/ki nan: https://forms.gle/v8NBCdymW3hzRJeX8


Mai Rahoto na Kauyuka (Rural Reporter)

Wuri: Jihar Kano
Nau’in Aiki: Yin rahoto a karkara

Sharuddan Aiki

  • Mazaunin Jihar Kano tare da damar shiga yankunan karkara
  • Iya yin rahoto a fili da tattaunawa da jama’a
  • Iya ɗaukar bidiyo (wayar hannu ma ta isa)
  • Sanin ka’idojin aikin jarida da mutunta al’umma
  • Iya aiki cikin lokaci da bin tsarin aiki

👉 Cike bayananka/ki nan: https://forms.gle/FyZDritkPRepk8rd8


Muhimmin Bayani

  • Ana buƙatar ladabi, amana, da jajircewa
  • Za a tuntubi waɗanda aka tantance kawai

 

Mataimakin kwamishina ya ce ga garinku nan bayan ya fadi a jihar Ebonyi

0

Wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ogbon-Inu Taiwo Popoola, ya mutu a Jihar Ebonyi yayin da yake halartar taron shugabanci a hedkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abakaliki.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Talata, inda marigayin, wanda shi ne jami’in kula da Sashen Leken Asiri na jihar, ya fara fama da matsananciyar wahalar numfashi a tsakiyar taron.

An gaggauta kai shi asibitin ‘yan sanda da ke hedkwatar rundunar a Abakaliki, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. Binciken farko ya nuna cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya da ke da alaƙa da hawan jini.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Joshua Ukandu, ya tabbatar da rasuwar, yana mai cewa marigayin bai kasance mara lafiya ba kafin faruwar lamarin, tare da bayyana shi a matsayin jami’i mai jajircewa da kwarewa. An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Alex Ekwueme da ke Abakaliki.

Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da Fani-Kayode, Reno Omokri da wasu 64 a matsayin jakadu

0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da nadin jakadu 64 da Shugaba Tinubu ya miƙa mata, ciki har da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan kafafen sada zumunta, Reno Omokri.

Tabbatarwar ta biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar kan Harkokin Waje, wanda shugaban kwamitin Sanata Sani Bello ya ce an tantance dukkan sunayen tare da gano cewa sun cancanta, ba tare da wani ƙorafi ko koke a kansu ba.

Daga cikin waɗanda aka amince da su akwai tsohon Ministan Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau, tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, tsofaffin gwamnonin Enugu da Abia, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu, da kuma tsohuwar Sanata, Grace Bent. Jimillar sun haɗa da jakadu 34 na aikin ƙwararru da 30 na siyasa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya taya sabbin jakadun murna tare da buƙatar su wakilci Nijeriya da mutunci a inda za a tura su, yana mai jaddada cewa babu wani ƙorafi da majalisar ta karɓa kan nadin, duk da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.