Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 73

Dangote ya shigar da ƙorafi ga hukumar ICPC kan shugaban hukumar NMDPRA

0

Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar ICPC yana zargin Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, da cin hanci da almundahanar kudade.

A ƙorafin da ya miƙa ta hannun lauyansa, Dangote ya buƙaci a kama, bincika tare da gurfanar da Farouk bisa zargin kashe fiye da dala miliyan bakwai wajen karatun ‘ya’yansa a Switzerland, ba tare da sahihin tushen kuɗi ba.

Jaridar Punch ta ruwaito Dangote ya ce Farouk ya yi amfani da mukaminsa wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati don amfanin kansa, lamarin da ke saɓa wa dokar rikon amana ga jami’an gwamnati.

Inda ya bukaci ICPC ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare gaskiya da martabar gwamnati a kasar.

Sojojin Nijeriya da ke Burkina Faso sun koka kan tsawaita zamansu a kasar

0

Jami’an Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) guda 11 da ke tsare a Burkina Faso sun koka kan tsawaita zamansu a kasar, suna mai kira ga gwamnatin Nijeriya musamman Ma’aikatar Harkokin Waje da ta dauki lamarin da muhimmanci.

Jami’an sun bayyana cewa suna kan tafiya ne zuwa Portugal domin gyaran jirgi, amma suka sauka a Bobo-Dioulasso sakamakon cikas din Na’ura da jirgin ya samu.

Rundunar ta NAF ta musanta zargin leken asiri ko ayyukan sirri, tana mai cewa saukar jirgin ta kasance bisa ka’idojin tsaro na jiragen saman kasa da kasa.

Daily Trust ta ruwaito mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya ce jami’an har yanzu na tsare, amma an fara tattaunawa ta diflomasiyya.

Ya bayyana cewa mukaddashin jakadan Nijeriya ya je Burkina Faso amma aka hana shi ganinsu, yayin da ake ci gaba da ganawa domin a sako su kafin Kirsimeti.

Jerin attajiran Afirka guda 22 a shekarar 2025 -Forbes

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya sake rike matsayi na daya karo na 14 a jere da dukiyar dala biliyan 23.9, sakamakon fara aiki da matatar man fetur dinsa da ke Lagos.

Mujallar Forbes da ta saba bincike da wallafa sunayen attajirai a duniya ta bayyana cewa attajiran Afirka sun kai 22 a shekarar 2025, inda jimillar dukiyarsu ta haura dala biliyan 105, karo na farko a tarihin nahiyar.

Duk da kalubalen tattalin arziki, kasuwannin hannun jari na duniya sun taimaka wajen karuwar dukiyar masu arziki a Afirka.

Rahoton ya ambato kasashen Afirka ta Kudu ne ke da mafi yawan attajirai (7), sai Najeriya da Masar da ke da 4 kowannensu, yayin da Moroko ke da 3.

Ga jerin attajiran Afirka a 2025:

Aliko Dangote – $23.9bn (Najeriya)

Johann Rupert & iyali – $14bn (Afirka ta Kudu)

Nicky Oppenheimer & iyali – $10.4bn (Afirka ta Kudu)

Nassef Sawiris – $9.6bn (Masar)

Mike Adenuga – $6.8bn (Najeriya)

Abdulsamad Rabiu – $5.1bn (Najeriya)

Naguib Sawiris – $5bn (Masar)

Koos Bekker – $3.4bn (Afirka ta Kudu)

Mohamed Mansour – $3.4bn (Masar)

Patrice Motsepe – $3bn (Afirka ta Kudu)

Issad Rebrab & iyali – $3bn (Aljeriya)

Mohammed Dewji – $2.2bn (Tanzaniya)

Michiel Le Roux – $2.2bn (Afirka ta Kudu)

Othman Benjelloun & iyali – $1.6bn (Moroko)

Anas Sefrioui & iyali – $1.6bn (Moroko)

Aziz Akhannouch & iyali – $1.5bn (Moroko)

Jannie Mouton & iyali – $1.5bn (Afirka ta Kudu)

Femi Otedola – $1.5bn (Najeriya)

Christoffel Wiese – $1.5bn (Afirka ta Kudu)

Youssef Mansour – $1.4bn (Masar)

Yasseen Mansour – $1.2bn (Masar)

Strive Masiyiwa – $1.2bn (Zimbabwe)

Rahoton na Forbes ya nuna cewa duk da matsin tattalin arziki da kalubalen siyasa a sassan Afirka, manyan ’yan kasuwa sun ci gaba da bunkasa dukiyarsu, lamarin da ke kara haskaka rawar da kasuwanci da zuba jari ke takawa wajen ci gaban nahiyar.

Dukiyar Elon Musk ta haura dala bilyan 600 – In ji Mujallar Forbes

0

Attajirin duniya Elon Musk ya zama mutum na farko a tarihi da dukiyarsa ta haura dala biliyan 600, inda Forbes ta kiyasta dukiyarsa ta kai kusan dala biliyan 677.

Karuwar dukiyar ta fi fitowa ne daga darajar kamfanin sararin samaniya na sa, SpaceX, wanda aka kimanta a dala biliyan 800 bayan wani sabon tayin hannun jari.

Attajirin dan kasuwar na Amurka na da kusan kashi 42 cikin 100 na hannun jarin SpaceX.

Saidai Jaridar Punch ta Ambato shafin mullar Forbes ta ce SpaceX ita ce mafi girman kadarar Musk, yayin da hannun jarinsa a Tesla da kuma kamfanin AI dinsa, xAI, ke kara masa arziki.

Rahoton ya nuna Musk na da tazarar fiye da dala biliyan 400 tsakaninsa da mutum na biyu mafi arziki a duniya.

APC ta lashe daukacin kujerun zaben ƙananan hukumomin Borno 27

0

Jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 27 da kuma na kansiloli a zaben ƙananan hukumomi da aka gudanar a Jihar Borno ranar 13 ga Disamba.

Shugaban Hukumar Zaben Jihar Borno (BOSIEC), Alhaji Tahiru Shettima, ne ya sanar da sakamakon a Maiduguri, yana mai ayyana zaben a matsayin sahihi, mai cike da adalci kuma a bayyane.

Shettima ya ce jam’iyyu shida ne suka shiga zaben duk da cewa BOSIEC ta bai wa kowa dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya bukaci sojoji su ci gaba da zama ‘yan ba ruwan mu a siyasa

0

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci Rundunar Sojojin Ƙasa ta Nijeriya da ta kiyaye rashin shiga harkokin siyasa tare da bin kundin tsarin mulki.

Ya bayyana hakan ne a wajen bude taron shekara-shekara na Shugaban Sojojin Ƙasa da ke gudana a Legas, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi.

Jaridar Daily Trust ta ce Tinubu ya jaddada cewa aikin sojoji shi ne kare ƙasa da ’yan ƙasa, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa rundunar ta fuskar kayan aiki da horo.

Ya yaba da nasarorin da sojoji ke samu a yaki da ta’addanci, yayin da Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu, da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, suka jaddada muhimmancin tsaro da haɗin gwiwar hukumomi wajen kare kasa.

An wayi gari babu hotunan kyamfen din Tinubu a manyan titunan Abuja

0

Hotunan da ke dauke da fuskar Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, wadanda aka manna a kan titin Airport Road da wasu muhimman wurare a Abuja dangane da zaben 2027, sun bace gaba ɗaya.

Jaridar Daily Trust ta lura cewa hotunan, da suka tayar da ce-ce-ku-ce kan kamfen tun kafin lokaci, an cire su daga City Gate zuwa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, inda yanzu aka maye gurbinsu da tallace-tallacen kasuwanci da sanarwar shirye-shiryen addini.

Batun hotunan ya jawo suka daga ’yan kasa, kungiyoyin farar hula da INEC, wadda ta sha gargadin cewa kamfen kafin lokaci ya sabawa doka. Fadar Shugaban Kasa ta nesanta kanta daga hotunan, tana mai cewa Tinubu bai amince da su ba.

Trump ya shigar da kara kan BBC, yana neman diyyar dala bilyan 5

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da kara a kotu yana neman diyya ta dala bilyan 5 (kimanin fam biliyan 3.7) kan BBC, bisa zargin yadda aka yi wa jawabinsa kwaskwarima da ya yi a ranar 6 ga Janairu, 2021 a cikin wani shirin bincike na Panorama.

A cewar takardun shari’ar da aka gabatar a jihar Florida, Trump na zargin gidan talabijin din da bata masa suna, tare da saba dokokin aiki.

BBC ta nemi afuwa ga Trump a watan da ya gabata, amma ta yi watsi da bukatarsa ta biyan diyya, tana mai jaddada cewa babu wani sahihin dalili na shigar da kara kan bata suna.

Lauyoyin Trump sun zargi BBC da gurbata jawabinsa da gangan, cikin mugunta da yaudara, domin bata masa suna. Har zuwa yanzu, BBC ba ta fitar da martani kan karar da aka shigar a kotu ba.

Marigayi Buhari ya nuna cewa mulki amana ce, ba hanyar tara dukiya ba – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana marigayi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin jagora mai karfin hali cikin natsuwa da kan ladabi, kuma mai kima da mutunci har zuwa karshen rayuwarsa. Ya ce Buhari ya bar suna na gaskiya, rayuwa mai sauki, tare da akidar cewa rike mukamin gwamnati amana ce, ba damar tara dukiya ba.

Shugaba Tinubu ya yi wannan bayani ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, yayin kaddamar da littafin From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari.

Shugaban ya bukaci iyalan Buhari su samu kwarin gwiwa da ta’aziyya daga addu’o’in ‘yan Nijeriya, yana mai jaddada cewa sunan Buhari zai ci gaba da zama abin koyi da zaburarwa wajen hidimar kasa.

Idan rikicin PDP ya ki ci, ya ki cinyewa za mu shiga kawance in ji Sule Lamido

0

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa dole na iya sanyawa jam’iyyar ta shiga kawance da wasu jam’iyyu idan ƙoƙarin da ake yi na warware rikicin cikin gida bai yi nasara ba.

Alhaji Sule Lamido ya yi wannan furucin ne yayin da yake karɓar shugabanni da masu ruwa da tsaki na PDP daga Jihar Jigawa a ofishinsa da ke Kano, inda ya jaddada buƙatar gaggauta sulhu domin ceto jam’iyyar daga ci gaba da durƙushewa.

Ya bayyana cewa rashin haɗin kai da sulhu na iya ƙara raunana PDP, yana mai kira ga shugabanni da mambobin jam’iyyar da su fifita haɗin kai da sasanci don dawo da ƙarfinta a siyasar Nijeriya.