Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 74

‘Yan sandan Nijeriya sun sanar da dawo da aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta sake fara aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu (Tinted Glass Permit), duk da cewa har yanzu batun yana gaban kotu. Rundunar ta bayyana cewa babu wani umarnin kotu da ya hana ta aiwatar da dokar, sai dai a baya ta dakatar da hukunta masu laifi ne domin bai wa masu mota damar daidaita takardunsu cikin sauki. Sai dai yanzu, ‘yan sanda sun ce karuwar laifuka da ake aikatawa ta amfani da motoci masu gilashi masu duhu ba tare da izini ba ya tilasta musu daukar mataki cikin gaggawa.

A cewar Rundunar, wasu bata-gari da kungiyoyin masu aikata manyan laifuka na amfani da irin wadannan motoci wajen boye fuskokinsu domin aikata fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka masu tsanani. Saboda haka, rundunar ta sanar da cewa aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu zai fara ne daga 2 ga watan Janairu, 2026. Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa za a aiwatar da dokar cikin kwarewa, mutunta hakkin jama’a, da bin doka da oda, tare da kira ga masu motoci da su nemi lasisin ta hanyoyin da aka amince da su.

Nijeriya ta musanta zargin leken asiri kan jirginta da ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta musanta zargin leken asiri da ake jinginawa jirginta a Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso, Burkina Faso, ya je aikin leken asiri a boye.

Runudunar ta ce rahoton karya ne kuma ba shi da tushe, tana mai jaddada cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Portugal domin gyara, kuma saukar gaggawar da ya yi ta faru ne saboda dalilan tsaro bisa ka’idojin sufurin jiragen sama na duniya.

Bayanai da Jaridar The Nation sun ce wata majiya a hedkwatar tsaron NAF ta ce jirgin yana dauke da dukkan takardun izini, kuma an bi dukkan matakan da doka ta tanada.

Dangote ya zayyana irin zagon kasan da ake yi wa matatun mai a Nijeriya

0

Shugaban matatar man Dangote, Aliko Dangote, ya ce kungiyoyin da ke zagon kasa a bangaren mai da gas a Najeriya da ya kira “oil mafia” sun fi karfin masu safarar kwayoyi.

Ya bayyana cewa an saci kayan matatar Dangote da darajarsu ta kai $82m, lamarin da ya janyo karin tsaro a matatar.

Dangote ya ce an yi gagarumin zagon kasa, har da cire muhimmin sashi daga babbar injin tukunyar ruwa yayin aiki, da kuma lalata bututun man fetur a fadin kasa. Ya ce wadannan ayyuka na nufin kassara aikin tace mai a cikin gida domin ci gaba da dogaro da shigo da fetur.

Jaridar Punch ta ruwaito shi na jaddada cewa zagon kasar da ake yi wa matatun mai na cikin gida na barazana ga tattalin arzikin kasa.

Tsadar kudin haya na hana samari aure a Sokoto – Daily Trust

0

Mazauna Jihar Sokoto sun koka kan tashin kudin haya, suna cewa lamarin na jinkirta aure tare da jefa matasa cikin matsin tattalin arziki da barazanar tarbiyya. Sun ce a al’adar jihar, yawancin samari ba sa aure sai sun samu gida, amma tsadar filaye da kayan gini ya sa hakan ya gagara.

‘Yan kasuwar gidaje sun ce ko mafi karancin haya ya wuce karfin talakawa, inda daki daya ke kaiwa ₦300,000, self-contain ₦400,000, yayin da gidaje masu dakuna biyu ke kaiwa ₦1.5–2m a shekara.

Dalilin haka ne wasu gidaje ma ke zaune babu masu haya saboda tsadar da ake sanya musu a cewar Rahoton Daily Trust.

Shugaban Hisbah na jihar ya ce suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki don a sassauta tare da samar da gidaje masu saukin kudi da kuma daidaita kudin haya.

Gwamnatin Sokoto ta ce tana gina gidaje 1,000 da kuma kammala wasu 500, yayin da gwamnatin tarayya ke gina gidaje 250, amma mazauna na bukatar a tabbatar da adalci da gaskiya wajen rabon su.

Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-baci

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da ikon Shugaban Kasa na ayyana dokar ta-baci a kowace jiha domin hana tabarbarewar doka da oda.

A hukuncin da ya samu rinjayen kaso 6–1, kotun ta ce shugaban kasa na da ikon dakatar da zababbun shugabanni a lokacin dokar ta-baci, amma dole ne hakan ya kasance na dan wani lokaci ne kawai.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Mai shari’a Mohammed Idris ya ce Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki ya ba shugaban kasa damar daukar matakai na musamman domin dawo da zaman lafiya, kodayake bai fayyace irin matakan ba.

Hukuncin ya shafi karar da Jihar Adamawa da wasu jihohin PDP 10 suka shigar, suna kalubalantar dokar ta-baci da Shugaba Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers, inda aka dakatar da gwamna da sauran zababbun jami’ai na tsawon watanni shida, inda Kotun ta yi watsi da karar.

Sai dai Mai shari’a Obande Ogbuinya na da sabanin ra’ayi, yana cewa ko da shugaban kasa na iya ayyana dokar ta-baci, ba shi da ikon dakatar da zababbun shugabanni.

Mutane uku sun hadu da ajalinsu a lokacin da suka fita sallar Asuba a Abuja

0

Mutum uku sun rasa rayukansu bayan wani mutum ya farmake su da wuka a harabar wani masallaci da ke Kado Bimko, Unguwar 1st Avenue, Gwarinpa a Abuja, yayin da suke jiran sallar asuba.

Shaidu sun ce wanda ake zargi, Laminde Boka, ya fara lahanta wani dattijo da ake kira Alhaji Wanzam da wuka yayin da yake tsaftace masallacin da sassafe.

Daga nan ya sake farmaki wani mutum da ya yi yunkurin tare shi, wanda ya mutu a kan hanyarsa ta zuwa asibiti. Mutum na uku ma ya rasu nan take bayan da wanda ake zargin ya riske shi ya fadi.

Rahotanni sun ce jama’a sun farmaki wanda ake zargin da duwatsu da sanduna, lamarin da ya jawo mutuwarsa na take.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Dagacin Kado Bimko, Malam Ibrahim Isiaku, ya ce an rufe masallacin na wani lokaci bayan lamarin, tare da yanke shawarar hana kowa kwana a harabar masallacin nan gaba.

Yayin da rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin.

Dimokuradiyyar Najeriya na cikin hadari gabanin zaben 2027 – shugabannin adawa

Manyan jagororin adawa sun zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da EFCC da sauran hukumomi wajen tsoratar da ‘yan adawa da raunana tsarin jam’iyyu da dama a Najeriya.

Sun ce ana fifita wasu wajen aiwatar da doka, inda ake matsa wa ‘yan adawa lamba yayin da ake watsi da zarge-zarge kan ‘yan jam’iyya mai mulki.

Jagororin sun bukaci a kare ‘yancin EFCC, a kafa hukumar bincike mai zaman kanta da za ta duba asusun gwamnati daga 2015 zuwa 2025, tare da saka matakan rigakafin cin hanci kai tsaye cikin harkokin biyan kudi na gwamnati.

Sun yi gargadin cewa idan ba a dakatar da wannan salo ba, dimokuradiyyar Najeriya na fuskantar barazana gabanin zaben 2027.

Saidai fadar shugaban kasa ta sha musanta wannan zargin.

Matatar Dangote za ta rage farashin mai a gidajen mai

0

Gidajen mai da ke hulɗa da matatar Dangote za su rage fetur zuwa ₦739 daga gobe

Shugaban Matatar Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa gidajen mai da ke hulda da kamfanin za su fara sayar da litar man fetur ₦739 daga ranar Talata a Legas.

Dangote ya ce matatar ta riga ta sauke farashin sari daga tasha daga ₦828 zuwa ₦699 tun 11 ga Disamba, wanda ya zama sauyi na 125 a farashin fetur a bana.

Ya bukaci ‘yan kungiyar IPMAN su rika saye a ₦699, yana mai tabbatar da wadatar kayayyakin musamman a yayin bukuwan karshen shekara na bana.

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

0

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050, yana mai cewa ta’addanci a Sahel da raunin hadin kan kasa da kasa na kawo cikas ga ci-gaban yankin.

Touray ya bayyana haka ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 69 an Abuja, inda ya ce wadannan kalubale na tilasta wa kasashen yankin daukar matakai masu wahala da ka iya shafar dunkulewar kungiyar.

Touray ya kara da cewa duk da matsalolin tsaro da siyasa da ke karkatar da hankali daga ci-gaba, ECOWAS za ta ci gaba da mayar da hankali kan hadewar tattalin arziki domin cimma burin Vision 2050.

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

1

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun yi ajalin wata mata mai juna biyu tare da danta mai watanni 18 a cikin gidansu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na dare, lokacin da mijin matar ya dawo daga aiki ya tarar da kofar gida a kulle, inda bayan ya shiga ya gano gawar matar da jaririn a ciki.

Wani jagora a unguwar, Ahmad Sani, ya ce al’umma sun kadu matuka, yana mai korafin rashin jami’an tsaro a yankin duk da an gina ofishin ‘yan sanda, tare da rokon Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Dr Ibrahim Adamu Bakori, da ya dauki matakin gaggawa.

‘Yan sanda sun ce bincike na gudana, yayin da mazauna yankin ke neman a hanzarta kamo wadanda suka aikata laifin.