DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 78

Tsare-tsaren Tinubu na da manufar inganta harkar lafiya a Nijeriya – Mohammed Idris

0

Ministan yaɗa labarai da wayar da Kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya ce manufofin Shugaba Bola Tinubu na fara magance matsalar ficewar ƙwararrun likitoci (japa) da sauran ƙalubalen lafiya a Nijeriya.

Idris ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin rantsar da daliban MBBS na jami’ar Nile ajin 2025, inda ya ce sabbin likitocin za su taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya da gwamnatin tarayya ke kokarin gyarawa.

A cewarsa, gwamnati na ƙirƙirar yanayi mai kyau da zai sa ƙwararru su zauna su yi aiki a gida, yana mai ƙara da cewa tuni wasu da suka bar ƙasar suna komowa Nijeriya, sakamakon sabbin tsare-tsaren da aka kafa, musamman a bangaren lafiya.

Obasanjo ya ziyarci fadar shugaban kasa a karin farko tun bayan rantsar da Tinubu

0

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock a ranar Juma’a, karo na farko tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau mulki, abin da ya ja hankalin jama’a ganin yadda ya dade bai halarci fadar ba.

Obasanjo, wanda ya sha sukar gwamnatin Tinubu, ya halarci taron Service of Nine Lessons and Carols na 2025 da Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya.

A taron, ya tuna da lokutan da Nijeriya ke da cikakken tasiri a Afirka, inda ya ce tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter kan sanar da Nijeriya duk wani mataki da Amurka za ta dauka a Afirka.

Kodayake bai yi tsokaci kai tsaye kan rikicin kalaman Amurka da Nijeriya ba, kasancewar Obasanjo a Aso Rock tare da manyan baki irinsu Janar Yakubu Gowon ya kara ɗaga darajar taron, tare da sake bude tattaunawa kan matsayar Nijeriya a idon duniya.

Ko da za a ba ni Dala biliyan 1 ba zai ja ra’ayina shiga siyasa ba – Limamin wani coci a Nijeriya

0

Babban limamin Cocin Living Faith Church Worldwide (Winners Chapel), Bishop David Oyedepo, ya ce ba zai shiga siyasa ba ko da an ba shi dala biliyan ɗaya, yana mai jaddada cewa siyasa ba ta cikin kiran da Allah ya yi masa.

Oyedepo ya faɗi hakan ne a yayin taron Shiloh 2025 a Canaanland, Ota, Jihar Ogun, inda ya shawarci mambobin cocin su maida hankali kan kiran da Allah ya ba su.

A cewarsa, a shekarar 2015 na gargadi coci cewa wahala na tafe kuma wahalar ta zo.

Oyedepo ya ce Shiloh 2025, wanda ya fara ranar 9 ga Disamba kuma zai ƙare 14 ga watan, na nufin ƙarfafa bangaskiya da shirya mabiya don tasiri mai kyau ga al’umma.

Wasu jami’an DSS sun fara kamun kafa don a sanya su rakiyar manya wato VIPs a Nijeriya – Rahoton jaridar Punch

0

Biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye ’yan sandan da ke tsaron manyan mutane, wasu jami’an hukumar farin kaya ta DSS sun fara neman manyan ’yan Nijeriya domin a ɗauke su a matsayin masu tsaro na sirri, kamar yadda Saturday PUNCH ta ruwaito.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin janyewar ne a ranar 24 ga Nuwamba, a wani yunkuri na mayar da jami’an tsaro kan aikin kare al’umma, musamman ganin karuwar garkuwa da mutane a jihohin Arewa. Daga baya, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an janye jami’ai 11,566 daga ayyukan tsaron VIP.

Rahotanni sun nuna cewa bayan wannan mataki, manyan mutane sun fara tuntubar NSCDC da kamfanonin tsaro masu zaman kansu. Sai dai an gano cewa wasu jami’an DSS suna kai ziyara a asirce ga wasu fitattun mutane, suna roƙonsu su nemi daraktocin DSS na jihohi a tura su matsayin sabbin masu tsaro.

Da yiwuwar litar fetur ta koma kasa da N800 a Nijeriya bayan sauke farashin da Dangote ya yi

0

Matatar Dangote ta sake rage farashin fetur a matakin ex-depot daga N828 zuwa N699 kan lita, matakin da ya saukar da farashin ƙasa da N800 a karon farko cikin watanni. Ragewar ta kai N125 kan lita, wadda ke nuna faduwar farashi da kusan kashi 15.58.

Kamar yadda bayanan Petroleumprice.ng suka nuna a ranar Juma’a, sabon farashin ya fara aiki ne tun 11 ga Disamba, 2025.

Wani mai magana da yawun Dangote, Tony Chiejina, ya tabbatar da sauyin farashin, yana mai cewa wannan shi ne sauyi na 20 da matatar ta yi a bana kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi sun ce an yi wannan ragin ne domin rage kuɗin sufuri gabanin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, lokacin da ’yan Nijeriya ke yawan tafiye-tafiye don haduwa da iyalai.

Babu batun kisan kare dangi kan wani addini a Nijeriya – Tinubu

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa babu wani kisan kare dangi da ake yi a kan mabiya wani addini a kasar, walau Musulmi ko mabiya addinin Kirista.

 

Tinubu ta bakin babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a Lateef Fagbemi SAN, ya bayyana haka ne a Abuja, a wajen taron kungiyar Nasrul-Lahi-l-Fatih karo na 8, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

A cewar sa, hare-haren da ake samu sun samo asali ne daga tarihi, matsalolin tattalin arziki da kuma wanzuwar ayyukan ta’addanci, yana mai cewa basu da alaka da wani addini.

ECOWAS ta amince John Mahama ya mata takarar shugabancin AU a 2027

0

Majalisar Ministocin ECOWAS ta amince da Shugaban Ghana, John Mahama, a matsayin ɗan takarar kungiyar da zai nemi kujerar Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) a shekarar 2027, lokacin da jagorancin zai koma yankin Yammacin Afrika.

An cimma wannan matsaya ne a taron ministocin karo na 95 da aka gudanar a Abuja, inda aka bayyana Ghana a matsayin muhimmiyar ƙasa a ECOWAS wadda ke ba da gudunmuwa ga martabar ƙungiyar a matakin duniya.

Jaridar Premium Times ta ambato Ministan Harkokin Wajen Ghana, Sam Ablakwa, ya bayyana cewa shugabannin kasashen ECOWAS za su tabbatar da wannan matsaya ranar Lahadi.

Neman tazarce na hana wasu gwamnoni yin aiki – Umar Bago

0

Neman tazarce a 2027, ne ke hana ni korar jami’an da ba su da amfani a gwamnatina – In ji Gwamna Umar Bago

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sake jaddada goyon bayansa ga tsarin wa’adin zangon mulki guda ɗaya ga gwamnoni a Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi na cewa wannan mataki zai ƙara inganta ayyuka, ya ƙara himma, kuma ya kawo ƙarshen rikice-rikicen neman tazarcen mulki da ke rage wa gwamnati aiki yadda ya kamata.

Dangote ya sauke farashin litar man fetur zuwa N699

0

Kamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin Fetur daga N828 zuwa N699 a kowace lita, an samu ragin da ya kai N129 ko kusan kashi 15.6%.

Shafin Petroleumprice.ng ya nuna sabbin bayanan farashin da suka fara aiki daga ranar 11 ga Disamba, 2025.

Wani jami’in kamfanin ya tabbatar da saukar farashin, wanda shi ne karo na 20 da kamfanin ke sake daidaita farashin fetur a bana.

Sabon ragin na zuwa ne kwanaki biyar bayan Aliko Dangote ya ce kamfanin zai ci gaba da sauke farashi domin zama abokin gogayya da kayayyakin da ake shigo da su daga waje.

Dangote ya ce farashin zai ci gaba da raguwa yayin da masana’antar ke kara samarwa da kuma inganta gasa da man da ake shigo da shi.

Tinubu ne ke da rijayen kuri’un Rivers a zaben 2027 – Gwamna Fubara

0

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa zai jagoranci kokarin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa hadin kai tsakanin jihar da gwamnatin tarayya zai kara wa Rivers ci-gaba.

Fubara, wanda ya yi wannan jawabi yayin kaddamar da hanyar Egbeda–Omerelu mai tsawon 12km, ya ce zai yi duk abin da ya dace domin tabbatar da zaman lafiya a jihar, saboda ci-gaba ba ya zuwa idan rikici ya yi yawa.

Ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta yi aiki tare da dukkan kungiyoyin goyon bayan Tinubu domin ganin an samu nasara a 2027.

A gefe guda, wata kungiya a APC ta kare ficewar Fubara daga PDP, tana cewa matakin ba kuskure ba ne, illa martani ga rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP.