DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 79

Tinubu ne ke da rijayen kuri’un Rivers a zaben 2027 – Gwamna Fubara

0

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa zai jagoranci kokarin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa hadin kai tsakanin jihar da gwamnatin tarayya zai kara wa Rivers ci-gaba.

Fubara, wanda ya yi wannan jawabi yayin kaddamar da hanyar Egbeda–Omerelu mai tsawon 12km, ya ce zai yi duk abin da ya dace domin tabbatar da zaman lafiya a jihar, saboda ci-gaba ba ya zuwa idan rikici ya yi yawa.

Ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta yi aiki tare da dukkan kungiyoyin goyon bayan Tinubu domin ganin an samu nasara a 2027.

A gefe guda, wata kungiya a APC ta kare ficewar Fubara daga PDP, tana cewa matakin ba kuskure ba ne, illa martani ga rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP.

EFCC na tuhumar Chris Ngige da zargin rashawa ta N2.2bn

0

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati a Nijeriya EFCC za ta gurfanar da tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, a kotun babban birnin tarayya da ke Gwarinpa, kan zargin almundahana da cin hancin da ya kai N2.26bn.

Ngige na fuskantar tuhume-tuhume guda takwas, ciki har da amfani da mukami wajen fifita kamfanonin abokansa yayin da yake kula da NSITF daga 2015 zuwa 2023.

EFCC ta ce ya ba wa kamfanonin Cezimo Nigeria Ltd, Zitacom Nigeria Ltd, Jeff & Xris Ltd, da Olde English Ltd kwangiloli na biliyoyin Naira ba bisa ka’ida ba.

Rahoton na jaridar Punch haka nan ya ce ana zarginsa da karɓar gudummawar kuɗi daga wasu kamfanonin kwangila a 2022, ciki har da N38.6m, N55m da N26.1m ta hanyar wasu shirye-shiryensa.

Kazalika an ruwaito cewa ana sa ran Ngige zai gurfana a kotu domin karanto masa kunshin tuhumar da ke kansa.

Amurka ta gama hada rahoton binciken zargin kisan Kiristoci a Nijeriya

0

Tawagar majalisar dokokin Amurka karkashin Riley Moore ta kammala bincike a Nijeriya kan zargin kisan Kiristoci, musamman a Benue, kuma za ta gabatar wa Shugaba Donald Trump da cikakken rahoto kafin ƙarshen Disambar nan.

Tawagar ta gana da ’yan gudun hijira, shugabannin Kiristoci, sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati, inda Moore ya ce sun ji labarai masu tayar da hankali game da hare-haren da ake zargin Fulani da masu tsattsauran ra’ayin addini suka yi.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ambato yadda gwamnatin Nijeriya ta ce rikicin ba na addini ba ne, batu ne da ya fi karkata ga sauyin yanayi da kabila.

A cire dukkanin shingen binciken da ke ba bisa ka’ida ba – DHQ

Hedikwatar tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta ba da umarnin gaggawa na cire dukkan shingayen bincike marasa izini a manyan hanyoyin ƙasar, bisa rahoton cewa suna rage ingancin aiki tare da jefa jami’an tsaro cikin haɗari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa umarni ne wanda Birgediya Janar A. Rabiu ya sanyawa hannu a madadin Ministan Tsaro Christopher Musa, da ya bukaci kwamandoji su cire dukkan shingayen da ba su wajabta ba a yankunansu.

Hanyoyin da abin ya shafa sun haɗa da Abuja–Lokoja–Enugu, Abuja–Kaduna–Kano, Abuja–Okene–Benin da Lagos–Ore–Asaba.

Ma’aikatar tsaron ta ce za a maye gurbin waɗannan shingaye da sintiri na musamman da kuma tattara bayanan sirri don inganta tsaro.

Tinubu ya fasa bai wa Abdullahi Ramat mukamin shugabancin hukumar NERC?

0
A wata wasika da shugaban Nijeriyar ya aike wa Majalisar Dattawa a cikin makon nan, Tinubu ya bukaci sanatoci su amince masa ya nada Aisha Mahmoud Kanti-Bello da Fouad Animashaun a matsayin kwamishinonin hukumar ta NERC mai kula da harkokin lantarki, amma ba a ga sunan Abdullahi Ramat a cikin wasikar ba.
Jaridar Daily Trust ta ce Tinubu ya shaida wa yan majalisar cewa sabuwar wasikar da ya turo musu ta shafe tsohuwar wasikar da ya tura musu a watan Agusta wadda ke dauke da sunan dan siyasar na jihar Kano.

Hukumar KAROTA ta mika wa HISBAH motocin barasar da ta kama a Kano

0

Hukumar Kula da Harkokin sufiri ta Jihar Kano wato KAROTA ta mika manyan motoci guda uku da ke ɗauke da kwalaben giya na miliyoyin naira ga Hukumar Hisba ta jihar.

Motocin da ke ƙunshe da kwalabe 4,920 sun shiga komar KAROTA ne yayin sintiri da daddare a birnin Kano.

Hukumar ta ce wannan mataki na cikin ayyukan sa ido kan kayan da ake jigilar su a tituna domin hana shigo da abubuwan sha masu haɗari ga lafiyar jama’ar jihar.

Hukumar EFCC ta kama tsohon Gwamnan Anambara Chris Ngige

0

Rahotanni daga gidan Talabijin na TVC a Nijeriya su ruwaito cewa jami’an tsaro dauke da makamai ne suka tsohon gwamnan Jihar Anambra, Sanata Chris Ngige a gidansa da ke Abuja.

Kodayake ba’a a bayyana dalilin kama shi ba, kuma hukumar da ta EFCC da ke yaki da rashawa a Nijeriya haryanzu ba ta yi karin haske ba game da kamun nasa.

Sai dai majiyoyi sun ce lamarin ya biyo bayan harin da aka kai wa motarsa a Anambra kwanaki kadan da suka wuce.

Yayin da masu ruwa da tsaki ke cewa suna kan binciken musabbabin kamun na sa,.

An haramta rufe lambar mota a jihar Katsina

0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta haramta yawan rufe lambar mota ba bisa ka’ida ba, lamarin da ta ce barazana ce ga tsaron jihar. Gwamnatin ta ce ana kara yawaita rufe lambar a kan motocin manyan jami’a da wasu mutane, abin da ka iya bai wa miyagu damar aikata laifi cikin sauƙi.

A kan haka ne Gwamna Dikko Umaru Radda ya umurci Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Katsina tare da sauran hukumomin kula da zirga-zirga su ɗauki mataki domin magance lamarin da kuma tabbatar da tsaron al’umma.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnati na Jiha, Abdullahi Garba Faskari, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta shawarci jama’a su daina wannan dabi’a domin kauce wa kamawa da gurfanar da su gaban kotu.

Ana mayar da ofisoshin gwamnati saniyar tatsa a Nijeriya – Sunusi Lamido

0

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi, ya soki yadda shugabancin siyasa a Najeriya, ke rikidewa daga hanyar ci gaba zuwa mallakar dukjya ta hanyar yaki halal yaki haram.

Sanusi ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru 15 na Enough is Enough (EiE) Nigeria a Lagos, inda ya ce rashin cigaba yana faruwa ne saboda shugabanni na fifita kansu da masoyansu fiye da bukatun al’umma.

Tsohon gwamnan Bankin Najeriya (CBN) ya yi kira ga matasa su kalubalanci tsarin da ke kawo rikici na kabilanci, addini, da son kai, su hada kai wajen gina Najeriya mai manufa.

Jaridar Daily Trust ta ambato shi ya na jaddada cewa kasar mallakar kowa ce, ba gwamnati ba, kuma kowa na da hakkin bayar da gudummawarsa wajen ci gaban ta wajen ginuwarta.

Burkina Faso ta saki sojojin Nijeriya 11 da take tsare da su

Gwamnatin Mulkin Soji a Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11 da ta tsare bayan jirgin da ya tashi daga Legas ya yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso saboda matsalar na’urori.

Kungiyar kasashen kawance ta AES ta bayyana lamarin a matsayin “Rashin dattako,” inda jirgin na Nijeriya kirar C-130 ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izininsu ba.

An tabbatar da cewa dakarun da ke cikin jirgin sun samu damar komawa Najeriya, duk da har yanzu ba a bayyana ko an saki jirgin ba.

Gidan Talabijin na TVC ya ruwaito jirgin ya sauka ne bisa ka’idojin tsaro na kasa da kasa yayin tafiya zuwa Portugal.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ya ce an yi bincike, kuma sojojin da aka tsare an kula da su yadda ya kamata, yayin da ake shirin ci gaba da aikin jirgin.