DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 80

Burkina Faso ta saki sojojin Nijeriya 11 da take tsare da su

Gwamnatin Mulkin Soji a Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya 11 da ta tsare bayan jirgin da ya tashi daga Legas ya yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso saboda matsalar na’urori.

Kungiyar kasashen kawance ta AES ta bayyana lamarin a matsayin “Rashin dattako,” inda jirgin na Nijeriya kirar C-130 ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izininsu ba.

An tabbatar da cewa dakarun da ke cikin jirgin sun samu damar komawa Najeriya, duk da har yanzu ba a bayyana ko an saki jirgin ba.

Gidan Talabijin na TVC ya ruwaito jirgin ya sauka ne bisa ka’idojin tsaro na kasa da kasa yayin tafiya zuwa Portugal.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ya ce an yi bincike, kuma sojojin da aka tsare an kula da su yadda ya kamata, yayin da ake shirin ci gaba da aikin jirgin.

Sojojin Nijeriya na dada mamayar maboyar Turji – Daily Trust

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da mamayar maboyar fitaccen shugaban barayin daji Bello Turji, bayan ajalin babban abokinsa a ta’addanci Kachalla Kallamu a gagarumin samamen da sojojin runduna ta 8 suka kai a Sabon Birni, Jihar Sokoto.

Majiyar soja ta tabbatar cewa an yi ajalin Kallamu ne tare da hadin guiwar ’yan sa-kai a Kurawa, inda sojoji suka kuma hallaka wani babban mai samar wa Turji kayan aiki.

Kallamu, ɗan asalin Garin-Idi, ya jima ya na hargitsa yankin gabashin Sokoto ta hanyar daukar rayuka, garkuwa da mutane da kuma ka hari a kauyuka, inda yake da kimanin mayaka 100 a karkashinsa.

Wani masanin harkokin tsaro Farfesa Murtala Ahmed Rufa’i ya shaida wa Daily Trust cewa duk da Rashin Kallamu ayyukan Turji na iya ci gaba, kasancewar ba ya cikin manyan kwamandojin sa kai tsaye, domin yana biyayya ga Sa’idu Malam wato Sa’idu Buzu, na biyu a matsayin mataimakin Turji kuma surukinsa.

Nijeriya ta fara sulhu da Burkina Faso kan batun sojojinta

Gwamnatin Nijeriya ta fara tattaunawar diflomasiyya domin kubutar da sojojin Najeriya da jirgin saman yaƙin kasar C-130 da gwamnatin sojin Burkina Faso ta tsare saboda zargin karya dokar shiga sararin samaniyarta.

Sojojin da jirgin, waɗanda ake tsare da su tsawon kwanaki uku, sun ci gaba da kasancewa a hannun hukumomin Burkina Faso, inda majiyoyin soji suka tabbatar cewa Ma’aikatar Harkokin Waje ce yanzu ke jagorantar lamarin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ne ya tabbatar da yadda ofishin jakadancin Najeriya a Ouagadougou ya fara tattaunawa da hukumomin ƙasar domin ganin an saki dakarun da jirgin.

A bangaren Burkina Faso, hukumar labarai ta ƙasa ta sanar cewa an tilasta jirgin na NAF dauke da sojoji 11 yin saukar gaggawa bayan zargin karya dokar shiga sararin samaniya, lamarin da ƙungiyar AES ta kira take hakkinsu na ikon ƙasa.

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce sojojin da ke cikin jirgin suna cikin koshin lafiya, tana mai bayyana cewa jirgin ya sauka ne a Bobo-Dioulasso bayan gano matsalar na’ura jim kadan bayan tashi daga Legas.

Nijeriya ce a gaba cikin kasashen da ke karan tsaye ga hukuncin kotun ECOWAS

Najeriya ce a sahun gaba na mafi yawan hukuncin Kotun ECOWAS da ba a aiwatar ba, a cewar alkaluman da Mataimakin Babban Rijistaran Kotun, Gaye Sowe, ya gabatar yayin bikin Ranar Kare Hakkokin Dan Adam ta Duniya a ranar Laraba.

Sowe ya bayyana cewa Najeriya na da hukunci 50 da har yanzu ba a aiwatar da su ba, cikin jimillar 125 na shari’u da kotun ta yanke kan ƙasar.

Inda ya ce wannan na nuna matsalar rashin bin hukunci a ƙasashe da dama na yankin.

Jaridar Punch ta Ambato shi na bayyana cewa tun kafuwar Kotun ECOWAS, ta yanke hukunci 492 kan ƙasashe mambobi 12, inda 192 daga ciki suka kasance masu bukatar aiwatarwa kai tsaye. A halin yanzu akwai shari’u 136 da ke jiran hukunci.

A bayanin rabon ƙasashe, Sowe ya ce kasashen Benin, Cape Verde, Côte d’Ivoire, Ghana, Guinea, Senegal, Sierra Leone da Togo suma na da tarin hukuncin da ba su aiwatar ba. Amma Najeriya ce ta fi yawan adadin.

Shugaban Kotun ta ECOWAS, Ricardo Gonçalves, ya ce duk da yanke muhimmam hukunci kan ’yancin rayuwa, ’yancin bayyana ra’ayi, taro, ilimi da sauran su, ƙasashe da dama sun kasa aiwatar da su, lamarin da ke tauye ingancin kare hakkin dan adam a yankin.

Amurka damu matuka da hallin da ‘yan gudun hijira ke ciki a Najeriya

Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilan Amurka ya sake jaddada ƙudirin Amurka na yaƙi da cin zarafin addini a duniya, musamman a Najeriya.

Jaridar Punch ta Ambato wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na X a ranar Laraba, sun ce Amurka ba za ta yi shiru ba yayin da ake kashe rayuka ba gaira ba dalili.

Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da tawagar ‘yan majalisar Amurka ƙarƙashin jagorancin Riley Moore suka kai Najeriya bisa umarnin Shugaba Donald Trump.

Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar da cewa ziyarar ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci, inganta tsaro a yankin, da kuma karfafa dangantakar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Akwai tabbaci kan zargin kaso 80% na rashawa a Nijeriya – ICPC

0

Hukumar ICPC ta bayyana cewa matsalar rashawa a Najeriya ta yi zurfi matuka, inda ta ce idan aka aiwatar da dokoki yadda ya kamata, kusan kashi 80% na ‘yan kasa na iya fuskantar hukunci.

Bayanin hakan ya fito ne daga Kwamishinan hukumar ICPC na Kaduna, Sakaba Ishaku, a taron horaswa kan inganta gaskiya da rikon amana a kananan hukumomi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi cewa rashawa ta shafi kusan dukkan bangarorin gwamnati da al’umma, kuma tana haifar da tasirin da ya hada da karancin albarkatu, karuwar talauci, da tsaikon cigaba ga kasa.

Ya kuma jaddada cewa rashin ingantacciyar kulawa da amana yana lalata kudaden jama’a, tare da yin kira ga shugabannin kananan hukumomi su kauce wa abin da zai munana tarihinsu.

Gwamnatin Tinubu na tuhumar Stella Oduah, da cin hancin ₦5bn

0

Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Saman Nijeriya, Stella Oduah, ta gurfanar a gaban kotu Abuja ranar Laraba kan zargin cin hanci da rashawa na biliyan 5

An shigar da kara ne bisa laifuka biyar da suka shafi yaudara, ciki har da samun ₦2.4 biliyan daga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta kamfanin Broad Waters Resources da ikirarin kudin na kula da aikin fasaha ne.

Kodayake Oduah da abokin laifinta, Gloria Odita, sun musanta dukkan tuhumar.

Alkalin kotu, Justice Hamza Muazu, ya ba Oduah belin kanta da kanta, tare da rike fasfo dinsu, sannan ya haramta mata fita daga ƙasar ba tare da izinin kotu ba.

Wannan shi ne karo na biyu gwamnatin tarayya ke gurfanar da Oduah kan wannan batu, bayan karar farko da EFCC ta shigar a kotun ta Abuja an janye ta.

Hukumar EFCC ta sake tsare Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami

0

Tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami, na tsare a hannun EFCC bayan an gayyace shi makon jiya kan wasu mu’amaloli da suka shafi dawo da wani ɓangare na kudin Abacha.

Rahoton jaridar Daily Trust ya gano cewa Malami ya musanta duk wani hannu a cikin lamarin, yana mai cewa bai san kome ba kuma bai aikata laifi ba.

A cikin wata sanarwa, ya ce shekaru da ya shafe a matsayin Babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a ya yi aikinsa ne wajen ƙarfafa yaki da harkokin ta’addanci da daukar nauyin ta’adda a kasar.

Malami ya bayyana cewa labarin kage ne kuma an yi amfani da shi wajen siyasa da nufin bata masa suna.

Hukumar NFF ta ce za ta biya bashin da kocin Super Eagles ke binta

0
Wani babban jami’in hukumar NFF ya bayyana cewa za a biya kocin Super Eagles, Eric Chelle, albashin watanni uku da yake bi, yayin da Najeriya ke shirin shiga gasar AFCON 2025 a Morocco.
An ruwaito cewa Chelle yana bin hukumar ta NFF albashin fiye da watanni uku, kafin fara gasar da za a yi daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga Janairu 2026.
Inda Najeriya za ta fitar da jerin ‘yan wasa 28 da za su halarci gasar tsakanin yau da Alhamis.
Jami’in hukumar ta NFF ya tabbatar wa jaridar The PUNCH cewa za a biya Chelle nan kusa.

‘Yan sandan Abuja sun cafke mai kai wa ‘yan bindigar Zamfara harsasai

0

Jami’an ‘Yan Sandan Birnin Tarayya sun kama wani mutum mai shekaru 32, Ahmed Abubakar, bisa zargin ƙoƙarin sayar da harsasai guda 1,000 ga ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na FCT, Miller G. Dantawaye, ya ce an kama Ahmed ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma a Unguwar Dodo, Gwagwalada, bayan samun sahihan bayanai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Bincike ya nuna cewa Ahmed yana hulɗa da wani mai suna Yusuf Mohammed, kuma an aika shi da wannan aikin ne ta hannun ƙanin sa, Ahmed Yakubu, wanda ake kyautata zaton yana da hannu a harkar laifuka kuma har yanzu ba a kama shi ba.

An ce ana ƙoƙarin cafke Yakubu da kuma rushe wannan hanyar laifi baki ɗaya, yayin da Ahmed ke hannun ‘yan sanda a yanzu.