Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 8

Kotu ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da ɗansa

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron shari’ar tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da dansa Abdulaziz Malami, kan zargin daukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Kotun wadda Justice Joyce Abdulmalik ke jagoranta ta dage shari’ar zuwa ranakun 15 da 16 ga Afrilu, 2026, domin fara sauraron karar.

A zaman kotun da aka yi ranar Talata, lauyan masu gabatar da kara, Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotu cewa an ba shi aikin jagorantar shari’ar ne kwanan nan, don haka yana bukatar karin lokaci domin ganawa da shaidu da kuma shirya takardun shari’ar.

Ya ce an ba shi umarnin karɓar shari’ar ne a ranar Litinin, don haka ya bukaci kotu ta ba su sabon lokaci domin su shirya yadda ya kamata.

Kotu ta ci Gwamnatin Kano tarar miliyan 1, a shari’arsu da tsoffin kwamishinoni

Babbar kotun ma’aikata, reshen Kano, ta ci gwamnatin jihar Kano tarar Naira miliyan 1, a shari’ar da wasu tsofaffin kwamishinonin jihar suka shigar domin hana gwamnati karɓar motoci na aiki da aka ba su lokacin da suke kan mukamansu.

Kotun, wadda Justice Mahmood Abba Namtari ke jagoranta, ta yanke hukuncin ne a zaman da aka gudanar ranar Talata, inda ta ce gwamnati za ta bayar da dubu 200,000 a matsayin tara a kowanne daga cikin shari’o’i biyar da ke da alaka da batun.

A zaman kotun, lauyan gwamnatin Kano, S. U. Jibril, ya bayyana cewa bangaren gwamnati ba su shirya ci gaba da shari’ar ba, saboda an sanar da shi a kurarren lokaci, lamarin da ya ce bai ba shi isasshen lokaci ba wajen shirya takardun da ake bukata.

Sai dai Solace base ta rawaito cewa lauyan tsofaffin kwamishinonin, Suraj Sa’ed, ya ce ba su da matsala da bukatar dage shari’ar, amma ya roki kotu ta sanya tara domin diyya ga wadanda suka shigar da karar.

Bayan dogon nazari, kotu ta amince da dage sauraron karar tare da sanya tara ta N200,000 a kowace shari’a, sannan ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga Afrilu, 2026.

Ruwan tafki ya ci ran wasu matasa biyu da suka yi gudun tsira daga masu kwacen waya a Kano

Wasu matasa biyu sun rasa rayukansu bayan sun nutse a cikin wani tafki yayin da suke gudun wasu da ake zargin ‘yan kwacen waya ne a jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yankin Ring Road Kureken Sani da ke karamar hukumar Kumbotso.

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce matasan da suka rasu sun hada da Sadiq Isyaku mai shekaru 18 da kuma Auwal Isyaku.

Ya bayyana cewa jami’an kashe gobara sun ciro su daga cikin ruwan, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsu.

Gwamnatin Nijeriya na shirin yin doka kan kananan yara masu amfani da shafukan sada zumunta

Gwamnatin Nijeriya ta fara neman ra’ayoyin jama’a kan yiwuwar yin doka da za su kare yara a intanet, ciki har da kayyade shekarun da yara za su iya amfani da kafafen sada zumunta.

Ministan sadarwa da kirkire-kirkire, Bosun Tijani, ne ya sanar da wannan shiri a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

Ya bayyana cewa duk da cewa intanet na ba yara damar koyo, kirkira da sadarwa, amma yana iya jefa su cikin hadurruka kamar cin zarafi a yanar gizo, kallon abubuwan da ba su dace ba, da kuma barazanar da sabbin fasahohi ke haifarwa.

Farashin man fetur ya karu da kashi 30% a Egypt sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya

Gwamnatin Egypt ta sanar da karin farashin man fetur da kashi 30 cikin 100, tana danganta matakin da matsin tattalin arzikin makamashi na duniya sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ma’aikatar man fetur ta kasar ta bayyana cewa karin farashin ya shafi fetur, dizal da iskar gas da ake amfani da ita a motoci, inda ta ce matsalolin samar da mai da tsadar jigilar kaya a teku ne suka haddasa wannan mataki.

A cewar ma’aikatar, rikicin da ke gudana tsakanin Amurka, Israel da Iran ya janyo tangarda a hanyoyin samar da mai da kuma zirga-zirgar jiragen ruwa, lamarin da ya sa farashin mai ya kai matakin da aka dade ba a gani ba cikin shekaru da dama.

Majalisar dattawan Nijeriya ta cire sunan Sanata Natasha a wakilcin da za suje taro MDD

Shugabancin majalisar dattawan Nijeriya ya cire sunan sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, daga cikin tawagar Nijeriya da za su halarci taron mata na majalisar dinkin duniya da ake gudanarwa a birnin New York, inda aka maye gurbinta da sanata namiji.

Jaridar Premium times ta rawaito cewa taron da aka fara a ranar 9 ga Maris kuma za a kammala 19 ga Maris, inda ake tattauna hanyoyin inganta damar mata wajen samun adalci da kuma kara daidaiton jinsi a duniya.

Sanatar ta bayyana cewa tun da fari ma’aikatar mata ta gayyace ta cikin tawagar Nijeriya, inda aka bukace ta da ta tura bayanan fasfo ɗinta na kasa da kasa.

Ta ce ta tura bayanan cikin sa’o’i kadan bayan an bukace ta, amma daga bisani an sanar da ita cewa ba za ta halarci taron ba saboda an ce ta makara wajen tura bayanan.

Ba mu da shirin tattaunawar sulhu da Amurka a halin yanzu – Gwamnatin Iran

Gwamnatin Iran ta bayyana cewa ba ta da niyyar fara tattaunawa da Amurka a halin yanzu, yayin da rikicin da ya barke tsakanin kasashen aka shiga rana ta 11, tare da ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana haka a wata hira da tashar PBS News, inda ya ce Iran ba ta ganin tattaunawa da Amurka a matsayin wani abu da ke cikin ajandarta a yanzu.

A cewarsa, Iran ta samu wasu dalilai a tattaunawar da ta gabata da Amurka, lamarin da ya sa gwamnatin ta yi watsi da batun komawa teburin sulhu a wannan lokaci.

‘Yan bindiga sun sake yin ɓarna a jihohin Kaduna, Kogi da Ondo

Akalla mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu huɗu suka fada hannun masu garkuwa da mutane a hare-hare daban-daban da ‘yan bindiga suka kai a jihohin Kaduna, Kogi da Ondo.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun kai hari a unguwannin Titin Bariki da Tsangaya da ke ƙaramar hukumar Makarfi a daren Lahadi tsakanin karfe 9:15 zuwa 10:00 na dare, inda suka halaka wani mutumi tare da sace wata tsohuwa.

A wani hari na daban a jihar Kogi kuma, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani manomi mai suna Raphael yayin da yake aiki a gonarsa kusa da kogin Lawri River a garin Odo‑Ere da ke ƙaramar hukumar Yagba West a ranar Asabar da rana.

A jihar Ondo kuwa, wasu ‘yan bindiga uku dauke da makamai sun sace mutane biyu a wani mazaunin manoma da ke Kajola, a yankin Ilu‑Abo da ke ƙaramar hukumar Akure North.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami’anta sun fara bincike domin ceto mutanen da aka sace tare da kamo wadanda suka aikata laifin.

Rikicin Gabas ta Tsakiya na iya sa farashin fetur ya kai ₦2,000 a Nijeriya — PETROAN

Kungiyar masu gidajen sayar da mai ta Nijeriya PETROAN, ta yi gargadin cewa farashin fetur na iya kaiwa kusan ₦2,000 a kan kowace lita, yayin da dizal zai iya kusantar ₦3,000, idan rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

Shugaban kungiyar na kasa, Billy Gillis-Harry, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a Ignatius Ajuru University of Education da ke Port Harcourt.

A cewarsa, tashin farashin mai a duniya da rikicin da ke kara tsananta tsakanin kasashen Israel, Iran, da kuma Amerika na iya jefa kasuwar makamashi cikin rudani, lamarin da zai iya janyo karin tsadar mai a Nijeriya da sauran kasashen duniya.

An bai wa ‘yan wasa 23, jan kati a wani rikici da ya ɓarke ana tsaka da wasa

Wani rikici ya barke a wasan ƙarshe na kofin Campeonato Mineiro tsakanin Cruzeiro Esporte Clube da Atlético Mineiro a Belo Horizonte, inda aka bai wa ‘yan wasa 23 daga bangarorin biyu jan kati saboda haddasa rikicin.

Al’amarin ya fara ne a ƙarshen wasan, lokacin da mai tsaron raga na Atlético, Everson, ya cakuɗa Christian na Cruzeiro bayan ya yi karo da shi yayin fafatawa kan kwallo da mai tsaron ragar ya ɗauka.

Bayan rikicin, alkalan wasan sun bayar da jan kati guda 23 ga ‘yan wasan – 12 daga Cruzeiro da 11 daga Atlético, duk da wasan ya ƙare ba tare da fitar da ‘yan wasa nan take ba.

Rikicin ya kunshi har ‘yan wajen fili da masu horaswa, kuma an ɗauki lokaci mai yawa kafin a samu nasarar shawo kan lamarin.