Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 7

Gwamnan Jihar Plateau ya kafa kwamitin shawarwari kan kafa ‘yan sandan jihohi

0

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya kaddamar da kwamitin mutane 14 domin nazarin batun kafa ‘yan sandan jiha a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga jihohi na su fara shirye-shiryen kafa ‘yan sandan jiha.

Gwamnan ya ce kwamitin zai yi cikakken nazari kan yadda tsarin ‘yan sandan jiha zai dace da tsarin tarayyar Nijeriya, tare da gabatar da shawarwari da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaro a matakin kasa.

Shugaban kwamitin, tsohon DIG Habila Joshak, ya ce za su gudanar da aikinsu da gaskiya domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Gwamnatin Nijeriya ta karbi allurar rigakafin cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV

0

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da karɓar sabuwar allurar rigakafin HIV mai suna Lenacapavir domin ƙarfafa yaƙi da cutar a Nijeriya.

Jami’an ma’aikatar lafiya ta tarayyar sun ce matakin na daga cikin kokarin rage yaduwar cutar ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin kiwon lafiya.

Shugaban shirin yaki da cutar HIV da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i na kasa, Dakta Adebobola Bashorun, ya ce gwamnati tare da abokan hulda za su tabbatar da an gabatar da maganin cikin tsari tare da shigar da shi cikin shirye-shiryen rigakafin cutar HIV na kasa.

Allurar Lenacapavir magani ne da ake yi sau biyu kacal a shekara, wanda ake ganin zai taimaka wajen saukaka wa mutane samun kariya daga kamuwa da cutar, maimakon shan kwaya kullum.

Gwamnati ta ce shirin zai taimaka wajen kara hanyoyin rigakafi da rage sabbin kamuwa da HIV a fadin Nijeriya.

Dakarun sojin Nijar sun yi wani gagarumin aiki

Rundunar sojin Nijar ta ce ta halaka akalla ‘yan ta’adda 265 tare da kama wasu 132 da ake zargi da taimaka musu ko aikata laifuka a sassa daban-daban na kasar cikin watan Fabrairu.

A wani rahoto da cibiyar kula da ayyukan hadin gwiwa ta soji ta fitar, ta ce sojojin sun gudanar da hare-haren hadin gwiwa na sama da kasa tare da sumame da kuma a tabbatar da tsaro a wurare daban-daban da ake gudanar da ayyukan soja.

A cewar rahoton, wadannan hare-hare sun kuma kai ga lalata da kwace motoci 47, bindigu 79, babura 152 da ake amfani da su wajen aikata laifuka.

‘Yan bindiga sun sake yin barna a jihar Katsina

Aƙalla mutane uku ne ake fargabar sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Jikamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa a jihar Katsina.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:10 na yammacin ranar Talata, lokacin da wasu mazauna garin ke shirin buɗe baki a rana ta 21 ga watan Ramadan, inda ‘yan bindigar suka riƙa harbi ba kakkautawa tare da jefa al’umma cikin firgici.

Rahotanni sun ce maharan sun kuma shiga shaguna daban-daban a garin, inda suka wawushe kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Mutanen da suka jikkata a harin an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Koriya ta Arewa ta zargi Amurka da Israel da haddasa rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya

Gwamnatin Koriya ta Arewa ta bayyana cewa tana girmama zabin da al’ummar Iran suka yi na naɗa sabon jagoran addini na kasar, yayin da ta zargi Amurka da Israel da haddasa rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa kafar yada labaran gwamnatin Koriya ta Arewa, ta bayyana cewa Pyongyang na mutunta ‘yancin al’ummar Iran na zabar sabon jagoransu.

A ranar Lahadi ne dai Iran ta sanar da nadin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin kasar, bayan rasuwar mahaifinsa Ali Khamenei, wanda ya mutu sakamakon wani hari da Israel ta kai a ranar 28 ga Fabrairu.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya bayyana cewa kasarsa na girmama zabin da al’ummar Iran suka yi, yana mai zargin Amurka da Israel da lalata zaman lafiya da tsaro a yankin.

Ministan tsaron Nijeriya ya kira taron gaggawa da harfsoshin tsaro

Ministan tsaron Nijeriya, Christopher Musa, ya kira taron gaggawa da dukkan hafsoshin rundunonin soji ofishinsa domin tattauna yadda za a shawo kan hare-haren da ake kai wa sansanonin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa manyan jami’an tsaron sun hada da babban hafsan tsaro Olufemi Oluyede, da babban hafsan sojin ƙasa, Waidi Shaibu, sauran sun hada da babban hafsan sojin sama, Sunday Aneke, da na sojin ruwa, Idi Abass.

Rahotanni sun ce taron ya biyo bayan sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai kan sansanonin sojoji a jihar Borno, inda akalla kwamandoji uku masu manyan suka rasa rayukansu.

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da bayar da lasisin shigo da fetur domin karfafa samar da shi a cikin gida

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da bayar da lasisin shigo da man fetur daga kasashen waje na tsawon wata na biyu, matakin da ke nuna yunƙurin gwamnati na karfafa samar da fetur a cikin gida.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa wannan mataki na zuwa ne yayin da hukumomi suka fara aiwatar da wasu tanade-tanade na dokar masana’antar man fetur, wadda ta tanadi cewa za a ba da izinin shigo da fetur ne kawai idan na cikin gida bai wadatar da bukatar ‘yan kasa ba.

Bayanan da hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA), ta fitar sun nuna cewa ba a bayar da wani sabon lasisin shigo da fetur ba a watan Fabrairu.

Sallar Juma’a ta gagari kauyuka kusan 10 a jihar Katsina ta dalilin ayyukan barayin daji

Fargaba ta mamaye wasu kauyuka a jihar Katsina bayan wani mummunan rikici tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga da ya tilasta wa mazauna sama da kauyuka goma dakatar da sallar Juma’a saboda tsananin harbe-harben bindiga da ya dauki tsawon sa’o’i.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa rikicin ya faru ne a yankunan karkara da ke iyaka da kananan hukumomin Musawa, Kankara da kuma Malumfashi, inda aka yi musayar wuta tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga na tsawon lokaci, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin fargaba.

Rahotanni sun ce tun kafin lokacin sallar Juma’a, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a garin Dangani da rana tsaka, inda suka shiga garin kan babura fiye da 70.

Maharan sun lalata shagunan sayar da wayoyi tare da kwace wayoyin da ake cajawa a wuraren caji da kuma wadanda suka samu a hannun mazauna yankin.

Gwamnatin jihar Jigawa ta kara alawus din masu unguwanni zuwa N10,000

Gwamnan Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da ƙara alawus ɗin da ake bai wa masu unguwa na wata-wata daga naira dubu uku zuwa naira dubu goma.

An sanar da wannan mataki ne bayan zaman majalisar zartarwar jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse a ranar Talata.

Da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon zaman, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jiha, Dr. Nura Kazaure, ya ce karin alawus ɗin na nuna kulawa da tausayi da gwamnatin gwamnan ke nunawa shugabannin gargajiya na matakin ƙasa.

Jaridar Punch ta ambato shi na cewa, an dauki matakin ne, duba da halin da tattalin arziki ke ciki da kuma nauyin da shugabannin gargajiya ke ɗauka wajen hidimar al’umma.

Kungiyar Lauyoyin gwamnati a Kano za su shiga yajin aikin sai baba ta gani

Kungiyar lauyoyin gwamnati ta Law Officers Association of Nigeria (LOAN) reshen Kano ta sanar da cewa mambobinta za su shiga yajin aikin sai baba ta gani daga tsakar dare na ranar 11 ga Maris, 2026, sakamakon abin da ta kira rashin magance matsalolin da suke fuskanta a aiki.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bakin shugabanta,Barista Abdullahi Aminu Shamsu ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan tattaunawa da suka yi da gwamnati lokuta da dama amma ba a warware matsalolin ba.

Kungiyar ta ce tun daga shekarar 2025 take gabatar da koke-koke ga gwamnati, har ma aka kafa kwamiti domin duba matsalolin, sai dai a cewarsa duk da amincewar gwamnati kan wasu shawarwari, har yanzu ba a aiwatar da su ba.

Ya kuma bayyana cewar suna ta fama da shari’u musamman na manyan laifuka da kuma barazana da suke fuskanta daga mutane amma duk da haka hakkinsu na lauya baya fita, wannan dalilin ya sanya kungiyar daukar wannan mataki.