DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 81

Jam’iyyar Accord ta bai wa Adeleke takarar gwamnan Osun

0

Jam’iyyar Accord ta ayyana gwamnan Osun Ademola Adeleke a matsayin dan takara daya tilo a zaben fidda gwanin gwamnan jihar

Kasa da sa’o’i 16 bayan Ademola Adeleke ya koma jam’iyyar Accord, shugabancin jam’iyyar na kasa ya amince da shi ya shiga zaben fidda gwani na gwamnoni.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Adeleke ya sauya sheka ne da yammacin Talata tare da mataimakinsa, Kola Adewusi, da wasu manyan jami’ai.

Shugaban kwamitin tantancewa na Accord, Elder Ibe Thankgod, ya tabbatar cewa an tantance Adeleke gabanin zaben fidda gwanin da za a yi a ranar Laraba.

Sojojin Najeriya sun yi ajalin na hannun damar Bello Turji a Sokoto

0

Sojojin rundunar 8 Division na Najeriya sun tabbatar da shafe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, daga duniya, a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Majiyar tsaro da ta nemi a boye sunanta ta shaida wa manema labarai cewa an yi nasarar ajalin Kallamu ne a wani gagarumin samame da aka yi tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai.

Rahotan jaridar The Nation ya nuna cewa Kallamu na daga cikin manyan amintattun Bello Turji, kuma yana taka muhimmiyar rawa a ayyukan ta’addanci a yankin kafin a kawo karshen sa a wannan rangadi na musamman.

Bai kamata Seyi Tinubu ya rika yawo da cincirindon sojoji ba – Wole Soyinka

Farfesa Wole Soyinka ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya kula da yadda ake amfani da jami’an tsaro ga wasu mutane na musamman, musamman dangin masu mulki.

Rahoton Jaridar Punch ya ce ya ce Soyinka ya ga abin mamaki a wani otel a Ikoyi, yayin da ake bai wa Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa tsatstsauran tsaro da yace sun isa kwace karamar kasa.

Soyinka ya ce abin ya dame shi sosai, har ya kira mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, domin jin dalili.

Kodayake ya yi jawabin ne cikin barkwanci cewa, idan rikici ya tashi a ƙasa, “ko a tura Seyi ya je ya magance shi tunda yawan tsaron nasa ya yi yawa,” amma ya nuna cewa akwai bakatar adalci a tsaron al’umma.

Gwamna Zulum zai ba duk dan Borno da ke hijira a Kamaru N500,000

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatin jiharsa za ta ba kowane ɗan gudun hijira ɗan Borno da yake a Kamaru N500,000 idan ya amince ya koma gida.

Zulum ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ‘yan gudun hijira a sansanin Minawao, da ke yankin Arewa ta Gabashin Kamaru.

Jaridar Punch ta ambato shi na cewa samar da cikakken tsaro a yankunan da za su koma, musamman bayan manyan hare-haren soji da ƙarfafa tsaron farar hula a Gwoza da sauran yankuna na jihar.

Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

Najeriya da Masarautar Saudiyya sun kulla sabuwar yarjejeniya ta shekaru biyar domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da dangantakar soja tsakanin kasashen biyu.

A cewar wata sanarwa daga Ofishin Sakataran Yaɗa Labarai na Ministan Tsaron kasar, Ahmed Dan Wudil, yarjejeniyar za ta haɗa da musayar bayanan leken asiri, horaswar soja, ƙera kayan tsaro, da haɗin gwiwa a fagen ayyukan tsaro domin bunƙasa zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Karamin Ministan Tsaron Nijeriya, Mohammed Matawalle, ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dr Khaleed H. Al-Biyari ya wakilci Saudiyya.

Sanarwar ta ce wannan mataki babban ci gaba ne wajen ƙarfafa hulɗa, inganta haɗin kai da kuma yaki da sabbin kalubalen tsaro dake tasowa a yankin.

Majalisar dattawa ta gayyaci ministan sufurin jiragen sama kan tsadar tikitin jirgi

Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da manyan masu ruwa da tsaki a bangaren sufurin jirage domin tattaunawar gaggawa bayan korafe-korafen jama’a game da tsadar tikitin jirgin sama a kasar.

Wannan matakin ya biyo bayan korafin da Sanata Buhari Abdulfatai ya gabatar, inda ya gargadi cewa hauhawar farashin jirgi na iya haifar da matsalar sufuri a fadin kasar, musamman yayin da ake shiga hutun karshen shekara.

A yayin tattaunawar, Sanata Buhari ya ce ‘yan Najeriya na kuka da tsadar jirgin cikin gida da ke kara tashi daga wata zuwa wata.

Ya bayyana cewa tikitin jirgi daga Abuja zuwa Legas yanzu ya kai tsakanin N400,000 zuwa N600,000, wanda ya sanya mutane da dama daina tafiya-tafiye ta sama.

Sanatan daga Jihar Oyo ya kara da cewa abin na kara dagule wa jama’a saboda matsalolin tsaro da wahalar tafiya a manyan hanyoyin mota.

Faransa ta samar da kayan aiki wajen dakile yunkurin juyin mulkin Jamhuriyar Benin – Gidan talabijin na France 24

Wani hadimin shugaban Faransa ya shaida wa gidan talabijin na France24 cewa Shugaba Emmanuel Macron ya tallafa wajen dakile yunkurin juyin mulkin da aka so yi a Jamhuriyar Benin.

Gidan talabijin din ya ruwaito hadimin Macron din na cewa mai gidansa ya tattauna da shugabannin ECOWAS da suka hada da Najeriya da Saliyo kafin samar da kayan aikin da ake bukata kafin samun damar kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyi9n mulkin. Hadimin shugaban Faransa da ya bukaci kada gidan talabijin na France24 ya bayyana sunansa ya ce tallafin da Faransa ta bayra ga sojojin Jamhuriyar Benin sun hada da bayanan sirri domin tabbatar da cewa juyin mulkin da aka so yi bai yi nasara ba.

Tinubu ya taimaki Nijeriya ta hanyar dakile juyin mulkin Benin

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana cewa gaggawar daukar matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ta hana afkuwar babbar barazanar tsaro ga Najeriya.

Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce idan juyin mulkin ya yi nasara, zai ba wa ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin da ke aiki a yankin Sahel damar kara tayar da hankula a Najeriya, musamman ganin cewa wasu sassan Benin sun riga sun cika da gungun masu bore.

Jaridar Punch ta ambato shi na cewa rushewar tsarin mulki a Benin zai iya shafar yankunan kan iyaka na Najeriya kai tsaye.

Gwamnonin sun jinjinawa Sojojin Najeriya bisa saurin mayar da martani da ya taimaka wajen dawo da daidaito a Benin, tare da jaddada cewa barazanar tsaro ga manyan biranen Benin kamar Porto Novo, Cotonou ko Parakou na da tasiri kai tsaye ga Najeriya.

ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a ƙasashen yammacin Afirka

ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a ƙasashen yammacin Afirka saboda ƙaruwar juyin Mulki

Kungiyar ECOWAS ta ayyana dokar gaggawa a duk fadin Yammacin Afrika, sakamakon tabarbarewar tsaro da karuwar kalubalen siyasa a kasashen mambobi.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da hakan a Abuja yayin zaman Majalisar Sulhu da Zaman Lafiya ta ministoci.

Touray ya ce rahotannin da ke gaban ministocin sun nuna cewa mafi yawan kasashen yankin suna cikin matakin haɗari mai tsanani, daga juyin mulki, wahalar sauyin mulki, takura wa zabe, karuwar ayyukan ta’addanci, zuwa matsin lambar ƙasashen waje kan dangantaka da manufofin yankin.

Ya ce abubuwan da suka faru kwanakin nan ciki har da yunkurin juyin mulki a Guinea-Bissau da Jamhuriyar Benin sun tabbatar da bukatar daukar matakin gaggawa.

Ya jaddada cewa zabe ya zama babban abin tayar da hankalin siyasa a yankin, tare da ci gaba da barazanar ‘yan ta’adda, da kuma masu tayar da tarzoma a iyakoki.

ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a Yammacin Afirka

Kungiyar ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a yankin Yammacin Afirka, sakamakon ƙarin tabarbarewar tsaro da kuma yawaitar juyin mulki a wasu ƙasashen mamba.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin zaman kwamitin sulhu na majalisar karo na 55 na matakin ministoci da aka gudanar a Abuja.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Touray ya ce halin da ake ciki ya nuna buƙatar yin nazari mai zurfi kan makomar dimokuraɗiyya a yankin, tare da ƙara zuba jari a fannin tsaro don kare al’ummomin ƙasashe mambobin kungiyar.

Majiyar DCL Hausa ta ruwaito cewa taron ya gudana ne a daidai lokacin da ake fama da juyin mulki a Guinea-Bissau, Mali, Burkina Faso da Nijar, tare da ƙoƙarin kifar da gwamnati a Jamhuriyar Benin da wasu sassan yankin, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin shugabanni.