DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 82

Gwamnatin Tinubu ta wajabta amfani da POS a ma’aikatun kasar

Gwamnatin Nijeriya ta haramta karɓar kuɗi a hannu domin biyan kudaden shiga, tare da umartar dukkan ma’aikatunta su girka na’urar POS cikin kwanaki 45.

Sabon umarnin ya fito ne daga ofishin Akantan Janar na Ƙasa, Shamseldeen Ogunjimi, wanda ya ce duk huldar biyan kuɗi ga Gwamnatin Tarayya dole ne ya rika bi ta tsarin amfani da asusun bai daya (TSA).

Takardar ta bayyana cewa duk wani karɓar kuɗi kai tsaye–ko a Naira ko a sauran kudade ya sabawa dokokin gwamnati, kuma yana lalata amincin tsarin e-payment da e-collection.

Yadda jirgin sojin Nijeriya ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso

Babu dokar da muka karya a saukar gaggawa da jirginmu ya yi a Burkina Faso in ji Rundunar sojin sama ta Nijeriya
Hukumomin sojin Nijeriya sun ce saukar gaggawa da jirginsu ya yi a birnin Bobo-Dioulasso na Burkina Faso matakin kariya ne da ya dace da ka’ida, ba kuma take dokar sararin samaniya ba.
A cikin wata sanarwa, Daraktan Yada Labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce tawagar jirgin ta lura da wata matsala ta na’ura bayan tashinsu daga Legas zuwa kasar Portugal, abin da ya sa suka nufi filin jirgin da ya fi kusa domin saukar kariya, kamar yadda dokokin tsaro na kasa da kasa suka tanada.

Nijeriya ta tura manyan aiyukanta na 2025 zuwa kasafin 2026

Gwamnatin Nijeriya ta dage aiwatar da kashi 70% na manyan ayyukan 2025 zuwa 2026 saboda karancin kudaden shiga da kuma bukatar kammala ayyukan da ake kan yi.

Cikin wani rahoto da jaridar Punch ta fitar, sabon umarnin ma’aikatar tsare-tsaren tattalin arziki ya hana sabbin manyan ayyuka a kasafin 2026, inda ma’aikatun gwamnati za su ci gaba da aiki da kudaden da aka ware musu a 2025.

Sanarwar tace kashi 30% na kasafin manyan ayyuka na bana ne kawai za a saki, sauran 70% za su zama tushen kasafin 2026, an kuma umurci hukumomin da kada su wuce iyakar kashe kudin ‘overhead’ na shekarar da ta gabata.

Gwamnati ta ce hakan zai inganta tsari, rage batar da kudi, kuma ya tabbatar da cewa kudin gwamnati ya tafi kan muhimman abubuwa kamar tsaro, tattalin arziki, ilimi, lafiya da makamashi.

APC ta nemi a kara yi wa jami’an tsaron Nijeriya uzuri

Jam’iyyar APC ta yi kira da a kara hakuri da kuma bai wa jami’an tsaro goyon baya yayin da suke kokarin ceto yaran da aka sace da kuma yaki da matsalar tsaro a fadin Nijeriya.

A wata hira da Channels TV, kakakin jam’iyyar, Felix Morka, ya ce kare rayuwar yaran da aka sace shi ne babban abin da gwamnati ke muradi, don haka dole jami’an tsaro su yi aiki cikin taka tsantsan.

Ya ce ayyukan ceto yara na bukatar kulawa ta musamman saboda kuskure kadan na iya jefa su cikin hatsari. Morka ya roki ‘yan Najeriya da su nuna hakuri da fahimta ga kokarin rundunonin tsaro.

Rahoton jaridar Punch ya ce Morka ya kuma yaba da jajircewar sojoji da sauran jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu don kare kasar.

IHR ta bukaci a mayar da rarar kudaden da Alhazan 2025 suka biya

0

Wata kungiyar fararen hula wadda ke gudanar da harkokin da suka shafi addini mai suna ‘Independent Hajj Reporters’ ta sake mika kira ga hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON, da hukumomin jin dadin Alhazai na jihohi su mayar da rarar kudaden da mahajjata sama da dubu 40 suka biya a yayin aikin hajjin 2025.

 

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Ibrahim Muhammad, ta ce kowane Alhaji cikin wadanda suka biya kudaden da suka yi yawa, na bin abin da ya kama daga Naira 400,000 zuwa 437,000, dogaro da bambancin da ke tsakanin farashin kasuwar canjin kudade da kuma yadda suka biya a lokacin aikin hajjin na 2025.

 

A cewar kungiyar, kafin wannan lokaci hukumar NAHCON ta bayyana yiwuwar mayar wa da Alhazan kudaden su bayan kammala aikin 2025, tana mai jaddada bukatar yin hakan cikin gaggawa kafin a fara aikin hajjin 2026.

‘Yan sanda sun koka da yawan yada labaran karya a Nijeriya – IGP

Shugaban ‘yan sanda a Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce babu wata hukuma a Najeriya da ke fuskantar mummunan tasiri daga labaran karya kamar ‘yan sanda.

Shugaban ya fadi hakan ne a taron hulda da Jama’a da aka shirye a Abuja, inda ya ya bukaci jami’an hulda da jama’a su rika amsa kira cikin gaggawa a duk lokacin da labarai marasa tushe suka bayyana.

Ya kara da cewa jami’an su shirye suke su yi aikin sintiri, kan sahihan bayanan kai dauki, da haɗin gwiwa da jama’a da ‘yan jarida domin kare mutuncin aikin hukumar a kasa.

Amurka ta fara gamsuwa da matakan Tinubu kan tsaron Nijeriya

Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto yara 100 da aka sace daga St. Mary’s Private Catholic School a Papiri, karamar hukumar Agwara, Jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Moore ya ce wannan ceton yana nuna himma ta gwamnatin Najeriya wajen magance matsalolin tsaro karkashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu.

Dan majalisar ya kara da cewa an kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya don magance zargin tsangwamar Kiristoci a kasar.

Ziyarar Moore ta biyo bayan tattaunawar tsaro tsakanin Mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, a Washington a watan Nuwamba, inda aka tattauna zargin tsangwamar Kiristoci a Najeriya.

APC ta dage sauya shekar Gwamnan Taraba zuwa Janairun 2026

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Ibrahim Tukur, ya tabbatar cewa gwamnan jihar, Agbu Kefas, zai sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a watan Janairu 2026.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce an dage sauyin sheƙan da aka tsara ranar 19 ga Nuwamba saboda sace ɗalibai a Jihar Kebbi.

A wani taron manema labarai a Jalingo, Tukur ya ce an ɗauki matakan dakatar da wasu shugabannin ƙananan hukumomi saboda saba wa kundin tsarin jam’iyya, sannan ya nemi sulhu da mabiya maimakon zuwa kotu.

Haka kuma, an soke dakatarwar ɗan majalisar jihar Taraba, Abel Peter, da aka dakatar saboda zargin yin aiki da ya saba wa jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar ya kuma yi watsi da ikirarin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na ɗaukar mulki a Taraba, inda ya ce APC ta riga ta karɓi fadar gwamnatin jihar kuma ba ta da niyyar janyewa.

TikTok ya dakatar da ‘yan Nijeriya daga yin ‘Live’ da tsakar dare

TikTok ta dakatar da damar yin LIVE a Najeriya daga ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na safe

Kamfanin ya sanar da masu amfani da shafin a Nijeriya cewa wannan mataki yana daga cikin kokarin tabbatar da kariya ga tsaron bayanan al’umma.

Wasu masu amfani da shafin sun bayyana cewa ba sa iya kallo ko watsa shirye-shirye na LIVE daga kasashen waje a wannan lokaci, tun bayan fara aiki da waccan dokar, inda aka nuna musu sako “No Access”.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan mataki ya biyo bayan sabbin kididdigar tsaro da TikTok ta fitar a Yammacin Afirka.

A cewar kamfanin, a zango na biyu na shekarar 2025, TikTok ta dakatar da kokarin hawa Live miliyan 2,321,813 da 1,040,356 LIVE creators a duniya saboda karya ka’idojin monetization.

Haka kuma, an cire bidiyo miliyan 3,780,426 a Najeriya daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025, inda kashi 98.7% da aka cire kafin a kalla, ne kuma 91.9% an cire su cikin awa 24.

Nijeriya ta yi rawar gani a dakile yunkurin juyin mulki Benin – Dada Olusegun

Fadar shugaban kasa ta ce yunkurin juyin mulkin da aka dakile a Jamhuriyar Benin ya kara nuna rawar jagoranci da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke takawa wajen kare dimokuraɗiyya da zaman lafiya a Yammacin Afirka.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar Lahadi wasu sojoji karkashin Lt. Col. Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na gwamnati a Cotonou, inda suka yi ikirarin hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon.

Sai dai dakarun gwmnatin kasar da ke tsaron fadar shugaban kasar sun sanar da tarwatsa su cikin gaggawa.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban Nijeriya kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun, ya fitar a shafinsa na X, ya ce martanin Nijeriya cikin sauri ya tabbatar da matsayin Tinubu na kare tsarin mulki a yankin.