DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 83

Nijeriya ce ta taimaka wa Benin ta dakile yunkurin juyin Mulki – Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ce ta taimaka wa Jamhuriyar Benin wajen dakile yunkurin juyin mulki da wasu sojojin ƙasar suka yi.

A cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta rabawa manema labarai ciki har da DCL Hausa, Tinubu ya jinjina wa sojojin saman Nijeriya da suka hanzarta tashi zuwa Benin domin kawo dauki, tare da tabbatar da cewa dakarun kasa ma sun isa can don tabbatar da ganin an kare tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.

Tinubu ya ce gwamnatin kasar ta Benin ce ta nemi taimako, kuma ya amince da gaggawa domin kare su daga sojojin da suka yi yunkurin karya tsarin mulkin farar hula a kasar.

Da alamu matsalar tsaro ta fi karfin gwamnatin Nijeriya – Kwankwaso

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce halin da ake ciki ya nuna Gwamnatin Nijeriya ta gaza a kokarinta na magance matsalolin tsaro a ƙasar.

Kwankwaso ya fadi hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce dakile rashin tsaro babban nauyin gwamnati ne tare da jihohi da ƙananan hukumomi, amma yadda ake tafiyar da al’amura ya nuna gwamnati na samun tangarɗa.

Ya yi suka kan yadda jihohi ke kafa kungiyoyin sa-kai masu ƙarancin horo, yana cewa hakan na kawo yawaitar makamai a hannun jama’a.

Kwankwaso ya kuma nuna damuwa kan karuwar tsangwama da nuna bambanci na kabilanci, inda ya ce ana kama mutane ba bisa ka’ida ba a wasu yankuna, abun da ke rura ƙiyayya a kafafen sada zumunta.

APC za ta yi nasara a zaben 2027 – Cewar Prof. Nentawe

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi nasara da rinjayen kuri’u a zaben 2027, yana danganta hakan da karɓuwar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da yake karɓar kungiyar Women Leaders Support Advancement, inda ya ce Renewed Hope Agenda na Tinubu ya kara bude damar siyasa ga matasa da mata.

Jaridar Punch ta ambato Yilwatda ya bukaci mata su ci gaba da mara wa gwamnati baya, yana cewa su ne ginshikin karfin jam’iyya a ƙasa, musamman yayin da APC ke shirin taron Caucus na kasa da kwamatin zartaswa da aka dage zuwa 18–19 ga Disamba a Villa.

Obasanjo ya ce bai san takamaiman shekarunsa ba

Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce bai san cikakkiyar adadin shekarunsa ba, yana dai kiyasta wa ne bisa ga abokan karatunsa da suka haura 90.

Jaridar Punch ta ambato shi a tattaunawa da Toyin Falola, ya bayyana cewa Obasanjo Presidential Library ɗakin karatun na adana tarihin rayuwarsa.

Tare da takardun makaranta, wasikun zamansa a kurkuku, rubuce-rubuce da sauran bayanai, domin kare tarihi da kuma ilmantar da masu zuwa gaba.

Obasanjo ya koka cewa rashin adana tarihi da bayanai yadda ya kamata na daga cikin matsalolin Najeriya, don haka ɗakin karatun nasa na da muhimmiyar rawa wajen gyara wannan gibin.

CAN ta ce ba ta da masaniya kan sakin dalibai 100 a jihar Neja

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ce har yanzu ba ta samu takamaiman bayanin hukuma game da labarin sakin dalibai 100 daga cikin waɗanda aka sace a Papiri, Jihar Neja ba.

Shugaban kungiyar ta CAN na jihar, Bishop Bulus Yohanna, ya ce da labarin ya tabbata, da zai zama abin farin ciki, amma har yanzu ba su samu sanarwa daga hukumomi ba.

A ranar 21 ga Nuwamba 2025 ne ’yan bindiga suka kai farmaki makarantar St. Mary’s Private Catholic School, suka sace mutane 315, dalibai 303 da malamai 12.

Rahoton da gidan talabijin na Channels ta fitar ya nuna cewa gwamnati ta yi nasarar kubutar da dalibai 100, abin da tsohon Janar John Enenche ya yaba, yana mai cewa aikin ceton ba abu ne mai sauƙi ba.

Nijeriya za ta rika ba wa kasashe bashin kudi nan da 2026 – Oluremi Tinubu

0

Uwargidan shugaban Nijeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ce nan da shekarar 2026 Nijeriya za ta rika ba wa wasu kasashen bashin kudade.

 

Oluremi ta bayyana haka ne a Ile-Ife da ke jihar Oyo, yayin bikin karbar sarauta ta Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua.

 

Jaridar Punch ta ruwaito Remi na cewa akwai kyakkyawan fata a gaba, tana mai jinjinawa gwamnatin Bola Tinubu, bisa ga yadda ta ce ta cimma nasarori masu tarin yawa cikin kankanin lokaci.

An kaddamar da kafar yaɗa labarai ta Hausa don mata zalla a Nijeriya

An kaddamar da Mata Media, kafar yaɗa labarai ta farko a Nijeriya da aka ware musamman domin mata, wacce ke aikin shirya labarai na abubuwan da suka shafi mata, ta hannun mata, domin mata.

Ƙwararrun mata ‘yan jarida da suka goge kuma waɗanda suka jajirce wajen tallafa wa mata, su ne suka kafa “Mata Media“ domin samar da kafar da za ta riƙa tattaunawar da ta shafi rayuwar mata.

Da take jawabi a yayin ƙaddamarwar, Fauziyya Kabir Tukur, babbar manajar kafar yada labaran Mata Media, ta ce an fito da wannan kafar ne don cike giɓin da ya dade a bangaren yaɗa labarai na Hausa.

“MUNA ALFAHARI DA KADDAMAR DA MATA MEDIA, SABUWAR KAFA MAI KISHIN MATA. BURINMU SHI NE SAMAR DA DANDALIN DA MATA ZA SU JI DAƊIN BA DA LABARANSU, BAYYANA RA’AYOYINSU DA DAMUWARSU CIKIN ‘YANCI, TARE DA KARFAFA  MATAN SHIGA HARKOKIN SHUGABANCI,” IN JI TA.

Daga cikin muhimman manufofin Mata Media akwai daukar nauyin horas da matasan mata ‘yan jarida, ta hanyar bayar da dama ga masu koyon aiki da sabbin shigowa su samu kwarewa a aikin jarida na Hausa.

Fauziyya wadda tsohuwar ma’aikaciyar BBC ce ta ce a halin yanzu, Mata Media na aiki ne kacokan ta yanar gizo, da shafukan sada zumunta na Facebook, Instagram, TikTok, YouTube.

A ƙarshe, babbar manajar ta yi kira ga sauran kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki su yi aiki tare da Mata Media domin ƙara ɗaga murya da tasirin mata a Nijeriya.

Ku daina nada baragurbin ‘yan siyasa a shugabacin Jami’o’i – Jega ga Tinubu

Tsohon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina nada ’yan siyasa marasa kwarewa da mutanen da ba su da cancanta domin shugabantar jami’o’in Najeriya.

Jega ya gargadi cewa irin waɗannan nade-naden siyasa suna lalata ingancin jami’o’in tare da raunana tsarin gudanarwarsu.

Jaridar Daily Trust ta ambato shi yana cewa ana bukatar shugabannin da suka dace, masu hangen nesa da kwarewa, ba masu neman ramko ko lada a siyasa ba.

Ya ce tsoma bakin siyasa wajen nada Vice Chancellors, shugabannin gudanarwa, da sauran manyan mukamai ya janyo durkushewar gudanarwa da tabarbarewar ingancin ilimi.

Ya jaddada bukatar tsarin zabe bisa cancanta da gaskiya, domin samun shugabannin da suka fi dacewa. Ya kuma gargadi cewa muddin ba a kawar da tsoma bakin siyasa ba, Najeriya za ta ci gaba da fitar da daliban da ba su da isasshen kwarewa ga ci gaban kasa.

Taron, wanda aka shirya don tunawa da marigayi Prof. Abdullahi Mahadi, ya haɗa manyan malamai da sauran masana a fannin ilimin jami’a a kasar.

NSA Ribadu ya gana da tawagar Majalisar Dokokin Amurka a Abuja

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya karɓi wata tawagar ‘yan majalisar dokokin Amurka a Abuja, domin ci gaba da tattaunawa kan al’amuran tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin sakon da ya wallafa a X, Ribadu ya ce ziyarar ta biyo bayan ganawarsu ta baya a Washington D.C., wadda ta mayar da hankali kan manyan batutuwan haɗin gwiwar tsaro.

Tawagar ta ƙunshi ‘yan majalisa kamar Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore, tare da halartar jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills. Ribadu ya ce hakan na nuna muhimmancin da ƙasashen biyu ke bai wa haɗin gwiwar tsaro.

A cewar NSA ɗin, tattaunawar ta ta fi karkata kan yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zaman lafiya a yankin, da hanyoyin inganta alaƙar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Ziyarar ta zo ne a lokacin da ake takaddama kan batutuwan diflomasiyya, musamman bayan matakin gwamnatin Amurka na mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take ’yancin addini, matakin da Najeriya ta musanta.

A baya-bayan nan, Ribadu ya gana da Sakataren Yaƙin Amurka Pete Hegseth, sannan Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa US–Nigeria Joint Working Group domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro.

Za’a sanya cibiyoyin lafiya a aikin titin Lagos–Calabar – Minista Dave Umahi

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa sabon titin Lagos–Calabar zai kasance da wuraren hutu, hasken fitilu masu aiki da hasken rana, da kuma CCTV domin kara tsaro da kuma bada agajin gaggawa cikin mintuna goma kacal.

Umahi ya yi wannan bayani ne yayin duba aikin Calabar–Itu da sassan 3A da 3B na cikin kilomita 71.4 da ake ci gaba da ginawa a Cross River.

Aikin yana gudana ne ta karkashin kamfanin HITECH Africa, wanda ke amfani da fasahar reinforced concrete pavement (wato kankare).

Jaridar Punch ta ruwaito shi ya kara jinjinawa Shugaban Kasa Bola Tinubu, wanda ya farfado da aiki da ya tsaya tun shekaru fiye da 27 da suka wuce.

Shugaban HITECH, Dany Aboud, ya tabbatar da cewa za su kara ma’aikata da kayan aiki domin kammala aikin cikin watanni 36.