DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 84

Rundunar sojin Njieriya ta jinkirta ritayar wasu dakarunta

Rundunar ta ce hakan ya fito ne sakamakon taɓarɓarewar tsaro da har ta kai ga Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a ƙasar.

An bayyana cewa fiye da mutane 600 aka yi garkuwa da su a watan Nuwamba kaɗai, ciki har da ɗalibai sama da 300 a Jihar Neja, masu ibada 38 a Kwara, da ɗalibai 25 a Kebbi.

Bayan haka ne Shugaba Tinubu ya umarci ƙara yawan jami’an tsaro da kuma tura karin ma’aikata zuwa jihohi.

A cikin wata takarda ta ciki, mai ɗauke da sa hannun Manjo Janar E. I. Okoro a ranar 3 ga Disamba, rundunar ta ce dakatar da ritaya na nufin karfafa aiki yayin da ake faɗaɗa yawan sojoji domin tunkarar matsalar tsaro.

JAMB ta fitar da ka’idojin rajistar jarrabawar UTME ta 2026

Hukumar JAMB ta fitar da cikakkun ka’idoji da matakan rajistar Jarrabawar UTME ta 2026, tare da jerin matsalolin da ɗalibai kan fuskanta wajen rajista.

Sanarwar ta fito ne ta shafinta na X a ranar Lahadi domin taimaka wa masu niyyar shiga jarrabawar su shirya tun da wuri.

JAMB ta ja kunnen ɗalibai su tabbatar da cewa duk bayanansu sun dace NIN, imel, da sakamakon A-Level, kafin su tura NIN don samun profile code.

Da zarar an samu profile code, ba za a iya canza shi ba, kuma bayanan ɗalibi za su fito kai tsaye daga NIMC.

Daga nan ɗalibai su je ofishin JAMB mafi kusa ko CBT Centre da aka amince da shi domin kammala rajista.

Ana sa ran fara siyar da fom ɗin UTME na 2026 daga Jumma’a, 31 ga Janairu, 2026, zuwa Asabar, 8 ga Maris, 2026.

Tsohon mamallakin Liverpool, Tom Hicks, ya rasu yana da shekara 79

Attajirin Amurka kuma guda cikin tsofaffin masu mallakar kungiyoyin wasanni, Tom Hicks, ya rasu yana da shekaru 79.

Hicks ya rasu ne a ranar Asabar a birnin Dallas, kamar yadda kamfaninsa Hicks Holdings LLC ya tabbatar a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Liverpool.

Rahoton da jaridar Punch ta ruwaito ya ce Hicks ya shahara a harkar kasuwancin wasanni a Amurka.

Ya mallaki kulob din Dallas Stars na NHL daga 1995 zuwa 2011, lokacin da suka lashe Stanley Cup a 1999.

Haka kuma ya kasance mai mallakar Texas Rangers na Major League Baseball daga 1998 zuwa 2010, inda kungiyar ta kai ga buga gasar World Series.

A 2007, Hicks ya saye rabin hannun jari a Liverpool FC, sai dai zamaninsa a kungiyar ya cika da rigingimu kan kudi da tafiyar da kulob din, wanda daga baya ya kai ga sayar da shi.

Faransa ta sha alwashin tallafa wa Nijeriya a yaki da ’yan ta’adda

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cikakken goyon bayan kasarsa ga Najeriya wajen yaki da matsalar tsaro, musamman barazanar ta’addanci da ake fuskanta a Arewa.

A wani saƙo da ya wallafa a X a ranar Lahadi, Macron ya ce ya yi magana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya tabbatar masa cewa Faransa za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.

Sanarwar ta Macron na zuwa ne bayan ƙarin hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Arewa, lamarin da ya ja hankalin ƙasashen duniya.

Najeriya na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashen duniya, ciki har da tattaunawar da Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi da Sakataren harkokin Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, a Pentagon domin inganta dabarun yaki da ta’addanci a Nijeriya.

Jirgin sojin Nijeriya ya yi hatsari a jihar Neja

Jaridar Punch ta rawaito cewa wani jirgin saman yaƙi na rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ya yi hatsari a kusa da kauyen Karabonde da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda matuka biyu suka tsira daga cikin jirgin kafin ya kama da wuta.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa jirgin ya tashi ne daga sansanin sojin sama na Kainji, kuma al’ummar yankin sun ce abin ya faru ne misalin ƙarfe 4:10 na yamma, inda aka ga wutar da ta tashi daga wurin da jirgin ya fāɗi.

Gaskiyar dalilan murabus din Badaru

Bayan murabus dinsa kwatsam daga kujerar Ministan Tsaro, wasu bayanai sun bayyana kan ainihin dalilin da ya sa Abubakar Badaru ya sauka daga mukaminsa bayan shekara biyu kacal a ofis.

A ranar Litinin, Badaru ya sanar da murabus ɗinsa yana mai cewa dalilan lafiya ne suka tilasta masa daukar matakin.

Jaridar Punch ta ruwaito yaddda Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabon Ministan Tsaro, tsohon CDS, Janar Christopher Musa (Rtd.), domin ya maye gurbinsa.

Mai ba shugaban kasa shawara kan bayanai da dabarun yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce murabus ɗin na da alaƙa da “ƙarin matsalolin lafiya.”

Amma binciken da Saturday PUNCH ta gudanar ya gano cewa rikici mai tsawo tsakanin Badaru da karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, shi ne ainihin dalilin da ya tilasta masa murabus — ba matsalar lafiya kawai ba.

Badaru dai ya hau kujerar minista ne a Agusta 21, 2023, bayan kammala wa’adin gwamnan Jigawa.

Inda aka nada shi bisa kwarewar mulki da tasirinsa a Arewa maso Yamma, yankin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da ta’addanci.

Kotun Koli ta yi hukunci kan kudaden kananan hukumomin Nijeriya

Kotun Kolin Nijeriya ta umurci gwamnatin Tinubu ta aiwatar da umurnin bai wa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye

Kotun ta nuna damuwarta kan yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa aiwatar da hukuncin da ta yanke a Yuli 2024 cewa a rika biyan kuɗaɗen ma’aikatar tarayya na kananan hukumomi kai tsaye zuwa gare su, ba tare da tsoma bakin jihohi ba.

Rahoton jaridar Punch ya ce hukuncin da Alkalin Kotun Koli Justice Mohammed Idris ya karanta jiya, kotun ta ce babu wata hujja mai kwair da ke nuna cewa Ministan Shari’a na Tarayya (AGF) ya ɗauki matakan da suka dace domin cika wannan hukuncin.

Kotun ta umarci gwamnati da ta gaggauta farawa aiwatar da hukuncin.

Malami ya musanta zargin daukar nauyin ta’addanci

Tsohon Babban Lauyan Nijeriya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta zarge-zargen da ke danganta shi da daukar nauyin ta’addanci, yana mai cewa zargin ba su da tushe kuma siyasa ce kawai ake yi da sunansa.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Malami ya ce hankalinsa ya kai kan wani rubutu da ke nuni da cewa shi da wasu mutane suna da alaka da wadanda ake zargi da ta’addanci ko taimaka wa masu aikata laifin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon ministan ya bayyana wadannan zarge-zarge a matsayin “ba su da tushe, balle makama.”

Ya ce ba a taba gayyatar sa, bincike ko kuma tuhumarsa ta kowace hanya daga wata hukuma ta tsaro a cikin gida ko waje ba kan batun daukar nauyin ta’addanci.

Malami ya jaddada cewa irin wadannan rahotanni na iya bata suna da tayar da hankali, don haka akwai bukatar a yi taka-tsantsan wajen yada bayanai marasa inganci.

Limaman coci sun musanta zargin kisan Kiristoci a Nijeriya

0

Wasu limaman coci sun yi watsi da zargin Amurka da ke cewa ana gudanar da kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya.

 

Limaman sun mayar da martani ne kan maganganun shugaban Amurka Donald Trump, wanda da fari ya yi barazanar daukar matakin soji a kan kasar.

 

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Bishop Timothy Cheren, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa akwai kisan kiyashi da gwamnati ke daukar nauyi ko kuma dauke kai daga haka.

 

Cheren ya yabawa kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen yaki da matsalar tsaro, tare da mika kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa kokarin da ake yi na kawo karshen ta’addanci a Nijeriya, kamar Daily Trust ta ruwaito.

Mun kashe Naira 100bn a fannin tsaron Borno cikin 2025 – Gwamna Zulum

0

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa da yadda ake kashe makuden kudade a fannin tsaro, yana mai cewa gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan 100 a fannin cikin shekarar 2025 da muke bankwana da ita.

 

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Sarkin Uba, Ali Ibn Mamza a fadarsa da ke garin Uba, karamar hukumar Askira/Uba a jihar ta Borno.

 

Zulum ya ce dalilin ziyarar ita ce duba halin da tsaro ke ciki a yankin, yana nuna damuwa da yadda matsalar tsaron ke sa a yi watsi da ayyukan tituna.

 

Sai dai ya sha alwashin cewa nan ba da jimawa ba, za a ci gaba da gudanar da ayyukan titunan, baya ga manyan makarantu da kuma cibiyoyin ilimin na’ura mai kwakwalwa.