DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 85

An gurfanar da alkali gaban kotu kan zargin karbar cin hanci a Gombe

0

Wani alkali da ke wata kotun majistire a jihar Gombe, Mohammed Kumo, ya gurfana a gaban kotu kan zargin sa da karbar cin hanci da kuma tatsar kudade.

 

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ce ta gurfanar da alkalin, kamar yadda yake a cikin wata sanarwa da ta fitar.

 

Sanarwar ta ce an maka shi ne gaban mai shari’a H.H Kereng da ke babbar kotun Gombe, ana tuhumar sa da aikata laifuka uku, kamar yadda EFCC reshen jihar ta mika.

 

Sai dai wanda ake kara ya musanta aikata laifukan, dalili kenan da mai shari’a ya bayar da belinsa, tare da dage zaman shari’ar zuwa ranakun 13 da 14 ga watan Janairun 2026, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

DSS ta kama likita da ake zargi da duba ‘yan ta’adda a Kwara

0

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke wani likita da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutane wadanda suka ji rauni kulawa a cikin daji.

Likitan da ake zargi wanda ba a bayyana sunansa ba, an cafke shi ne a yankin Jebba bayan bayanan sirri sun nuna cewa wasu masu aika saƙo suna kai kayan magani daga Sokoto domin jinya ga ‘yan ta’adda da suka ji rauni a dazuzzuka cikin jihar Kwara.

Majiyoyin tsaro sun ce da yawa daga cikin waɗannan kungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga ne a yayin arangama da jami’an tsaro a kwanan nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mai magana da yawun gwamnan Jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya ce kama wanda ake zargin wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na yaƙi da ta’addanci.

Kakakin majalisar dokokin Rivers da ƴan majalisa 15 sun koma jam’iyyar APC

0

‘Yan majalisar dokokin Jihar Rivers 16 karkashin jagorancin kakakin majalisar Martin Amaewhule, sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

 

Amaewhule ya sanar da yanke wannan shawara ne yayin zaman majalisar na yau Juma’a, inda ya bayyana rarrabuwar kai a cikin PDP a matsayin dalilin daukar matakin.

 

Ya shaida wa sauran ‘yan majalisar cewa ya sanar da masu ruwa da tsaki batun barinsa PDP, inda ya kara da cewa tuni ya ayyana shiga APC mai mulki a Nijeriya

Za mu bai wa mata ‘yansanda karin damarmaki a aiki – IG Kayode Egbetokun

0

Babban sufeton ‘yansandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya sha alwashin bai wa jami’a mata ƙarin damarmaki a aikin.

 

Kayode ya yi wannan bayani ne a Abuja, yayin bikin cika shekaru 70 da mata suka fara aikin dansanda a Nijeriya.

 

Ya kuma ce rundunar na alfahari da jami’anta mata, yana mai jaddada goyon bayan kawar da nuna bambanci, tsangwama da duk wani abu da ka iya zama kalubale gare su a tsarin aikin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Za mu biya bashin ‘yan kwangila nan da 20 ga Disamba – Gwamnatin Nijeriya

0

Gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin kammala biyan bashin da ‘yan kwangila ke bin ta, daga yanzu zuwa ranar 20 ga watan Disamban 2025.

 

Wannan dai na a matsayin wani yunkuri na daidaita lamura, biyo bayan zanga-zangar da ‘yan kwangilar suka fara gudanarwa kan halin da suke ciki.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ministan ayyuka na Nijeriya David Umahi ne ya bayar da tabbacin a jihar Nassarawa, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da kafa wani kwamiti da zai bibiya tare da tabbatar da cewa an biya su hakkokinsu.

Sojoji sun ceto mutane 318 da aka sace tare da kama 74 da ake zargi da hannu – Hedkwatar tsaron Nijeriya

0

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana cewa dakarun da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar sun ceto mutane 318 da aka yi garkuwa da su a watan Nuwamba, tare da kama wasu 74 da ake zargi da ta’addanci da fataucin mai da sauran laifuka.

A cewar Daraktan yada labarai na tsaro, Maj. Janar Michael Onoja, wanda ya yi jawabi an Abuja, ya ce a wannan watan kuma ’yan ta’adda 69 da iyalansu sun mika wuya a Arewa maso Gabas.

Hedkwatan tsaron ta ce dakarun sun kuma dakile satar mai da kimar ta kai sama da N217m, tare da rushe wuraren tace mai na bogi 16 da gano lita 201,700 na ɗanyen mai da lita 88,177 na dizal.

Onoja ya kuma yaba wa dakarun bisa ƙoƙarinsu, tare da roƙon jama’a da su ci-gaba da ba da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro.

Gwamnan jihar Zamfara ya gabatar da kasafin kudi N861bn na 2026 ga majalisar dokokin jihar

0

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 861 na shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin Jihar a Gusau, yana mai cewa wannan kasafi taswira ce ta sauyi, domin a cewarsa, kasafin ya kunshi kuɗin ayyukan ci-gaba na N714bn wanda ya kunshi kaso 83 da kuɗin gudanarwa na kusan N147bn (kaso 17).

Dauda ya ce gwamnatinsa, wadda aka zaɓa a kan alkawarin ceto, gyara da farfaɗo da jihar, ta yi aiki tukuru don farfaɗo da muhimman bangarori da kuma gina tubalin ci-gaba mai ɗorewa.

Hakazalika, Gwamna Lawal ya kara da cewa mutanen Zamfara yanzu suna ganin haske da ci-gaba, yayin da kasafin 2026 wanda ya kira kasafin tabbatar da daidaito da ci-gaba ke nufin zurfafa nasarorin da aka cimma ta hanyar shirin Six-Point Rescue Agenda.

Kasafin ya ba da fifiko ga tsaro, inganta aikin noma, sabunta fannin kiwon lafiya, faɗaɗa ilimi, gina manyan ayyukan raya ƙasa, da kuma ƙarfafa matasa, mata da marasa galihu, tare da tabbatar da cewa babu wani yanki ko al’umma da za a bari a baya.

Shugaba Tinubu ya aika da sunan Dambazau domin tantancewa a matsayin jaakada

0

Shugaba Bola Tinubu ya ya aike da tsohon ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, wanda ya taba zama shugaban sojin ƙasa, a matsayin jakada domin tantancewa a majalisa.

Haka kuma a cikin sunayen akwai Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon kwamandan sojin ruwa kuma tsohon shugaban rikon Rivers.

Sauran sun hada da Ita Enang, tsohon sanata, da Chioma Ohakim, tsohuwar uwargidan jihar Imo.

Wannan na zama rukuni na uku na jerin jakadu da shugaban ya aika majalisa domin tantancewa.

Fadar shugaban kasa ta ce sabon jerin sunaye na kunshe ne da mutane da za su wakilci ƙasar a muhimman ƙasashe, domin karfafa dangantaka da kare muradin Nijeriya a ketare.

Amurka ta ba da tallafin Dala miliyan 5 domin ceto yara masu fama da tamowa a Nijeriya

0

Kasar Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 5 ga asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin kai agajin gaggawa ga yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a Arewa maso Yammacin kasar.

Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka ya fitar ranar Alhamis ta ce kudin za su taimaka wajen kai tallafi ga akalla yara 70,000.

UNICEF za ta yi amfani da kuɗin wajen samar da abinci mai inganci kai tsaye, magunguna da sauran muhimman kayayyakin jin-kai.

Wannan taimako na daga cikin matakan Amurka na tallafa wa ƙoƙarin rage matsananciyar yunwa da inganta lafiyar yara a yankin.

‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara biyu sun fice daga jam’iyyar APC

0

’Yan majalisar dokokin jihar Zamfara biyu sun fice daga jam’iyyar APC, suna zargin tana fama da rikice-rikice da matsalolin jagoranci.

Shamsudeen Hassan Basko na Talata-Mafara Arewa da Nura Dahiru na Birnin-Magaji sun sanar da ficewarsu a cikin takardun murabus da aka karanta a gaban majalisa.

Hassan ya ce rabuwar kawuna, raunin jagoranci da wariya ga ’yan jam’iyya a matakan jiha da kananan hukumomi ne suka sa ya daina tafiyar APC, yana mai cewa hakan bai dace da alkiblarsa da muradin mazabarsa ba.

Dahiru wanda ya koma jam’iyyar PDP, ya ce barin jam’iyyar zai ba shi damar aikin da ya fi dacewa da bukatun mutanen da yake wakilta.

Dukkan su sun gode wa jam’iyyar kan damar da suka samu, tare da bukatar a dauki takardunsu a matsayin cikakken ficewa.