DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 86

Mun amince da tsare-tsaren harajin Tinubu ne don inganta tattalin arzikin Nijeriya – Sanata Barau Jibrin

0

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, ya ce sabon tsarin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar an amince da shi ne domin fadada hanyoyin samun kudaden shiga da karfafa tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da daliban Jami’ar Ilorin, inda ya ce manufar ita ce kasar ta daina dogaro da man fetur kadai.

Barau ya ce akwai manyan bangarori da ba a taba sosai ba wadanda yanzu za su fara ba da gudunmawa, wanda hakan zai samar da karin kudi don inganta ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da masana’antu wanda zai bude sabbin ayyuka ga matasa, tare da habbaka tattalin arzikin kasa baki daya.

Fiye da kaso 70 na masu yi wa Tinubu aiki sun taɓa sukar sa a baya, in ji hadimin shugaban Nijeriya Daniel Bwala

0

Hadimin shugaban Nijeriya, Daniel Bwala, ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na mutanen da ke aiki tare da Tinubu sun taba adawa da shi a baya.

Bwala ya bayyana haka ne a Arise TV yayin martani kan sukar jerin sunayen jakadu da cewa wasu sun taba yi wa Tinubu ihu a siyasance.

Bwala ya ce Tinubu ya sha gaya masa cewa mahaifiyarsa ta koya masa rungumar kowa ko da masu adawa ne, kuma fadar shugaban kasa ta yi shiru kan jerin jakadu ne don kada ta tsoma baki a aikin Majalisa.

Hakazalika ya kara da cewa tarihin Tinubu ya nuna cewa yawancin mutanen da ke kusa da shi a yau sun taba kalubalantar sa a siyasa, amma ya yanke shawarar yin aiki da su saboda salon shugabancinsa.

Tinubu ya jinjina wa majalisar dattawa kan tabbatar da CG Musa a matsayin ministan tsaron Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa majalisar dattawa kan saurin tabbatar da Janar Christopher Musa (ritaya) a matsayin sabon ministan tsaro, yana mai cewa nadin ya zo a lokacin da kasa ke fuskantar manyan kalubale.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Tinubu ya ce ya mika sunan Musa ga majalisar kwanaki biyu da suka gabata domin tantancewa da tabbatarwa.

Ya bayyana tsohon CDS din a matsayin “mutumin kirki” da ƙwarewarsa za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin tsaro.

Babu wata alama da ke nuna cewa Nijeriya za ta rushe – Tukur Buratai

0

Tsohon babban hafsan sojin kasan Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (rtd), ya ce maganganun da ke cewa Nijeriya na dab da rushewa ba su da tushe.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana hakan a matsayin kalaman da ba su dace ba kuma ba su yi la’akari da tarihin dorewar kasar ba.

Buratai ya ce Nijeriya ta sha tsira daga rikice-rikicen siyasa, matsin tattalin arziki da kalubalen tsaro da ka iya karya wasu kasashe.

A cewarsa, sabon salo na shugabanci mai kishin kasa na fitowa a gwamnati da bangarori daban-daban.

Gwamnatin Nijeriya na sa ran tara Naira tiriliyan 34 daga kudaden shiga a 2026

0

Majalisar zartaswa ta Nijeriya ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar na sa ran tara Naira tiriliyan 34.33 a shekarar 2026.

Ministan tsare-tsaren kasafi, Atiku Bagudu be ya sanar da hakan bayan zaman majalisar da shugaba Tinubu ya jagoranta, inda ya ce ofishin kasafin kasa ne ya gabatar da takardun ta hannun Darakta-Janar, Tanimu Yakubu.

Bagudu ya ce majalisar ta ɗauki matsayar samar da ganga miliyan 2.06 na mai a rana a 2026, sai dai don kauce wa gibin kudaden shiga, za a yi amfani da adadin ganga miliyan 1.8 wajen tsara kasafi.

Majalisar ta kuma amince da farashin gangar mai na Dala 64 da kuma musayar Naira 1,512 kan Dala ɗaya, la’akari da tasirin zaben 2027 kan darajar Naira.

Ministan ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya na sa ran tara kuɗaɗen shiga daga fannonin da ba na mai ba, inganta haraji, da faɗaɗa tattalin arziki.

‘Yan gudun hijira da ke komawa muhallansu a Nijeriya na iya fuskantar barazanar ababen fashewa a yankunansu – MDD

0

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa da cewa dubban ‘yan gudun hijira a Nijeriya na iya komawa yankunan da ke cike da ragowar abubuwan fashewa, musamman yayin da ake rufe sansanoni ba tare da samar musu da wurin zama a madadin muhallansu ba.

Masana a taron kasa da kasa da aka gudanar a hedikwatar MDD a Geneva sun ce raguwar tallafi a kasashe kamar Nijeriya da Afghanistan na kara jefa fararen hula cikin hadarin bamabaman da ba su tashi ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugaban shirin kawar da abubuwa masu fashewa na MDD a Nijeriya, Mista Edwin Faigmane, ya ce UNMAS ta horas da sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaron farar hula kan yadda ake kare kai da kuma yadda ake gano abubuwan fashewa a wuraren da ake fama da rashin tsaro.

Faigmane ya bayyana cewa horon ya fara haifar da sakamako, domin ana samun rahotanni daga al’ummomi da jami’an tsaro game da gano abubuwan fashewa da kuma mika su ga hukumomi da rundunonin tsaro.

Majalisar dokoki ta nemi a fallasa masu daukar nauyin ta’addanci a Nijeriya

0

Majalisar dokokin Nijeriya ta bukaci gwamnatin ƙasar ta bayyana sunayen mutanen da ke daukar nauyin ta’addanci tare da gurfanar da su a gaban kotu.

 

Wannan kira daga majalisar dattawa da ta wakilai, ya zo a daidai lokacin da gwamnati ta bayyana cewa ta fara daukar matakai don magance ta’azzarar matsalar a sassa daban daban na kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

A hannu guda, majalisar dattawa ta kuma bukaci a rika zartarwa da masu garkuwa da mutane hukuncin kisa, da kuma duk wanda ke daukar nauyinsu, ko yake taimaka musu da bayanai, yayin da ‘yan majalisar ke tattaunawa kan gyaran dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022.

Daga 2026 ₦500,000 kawai ɗan Nijeriya zai iya cira a banki cikin sati ɗaya – CBN

0

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fasalin dokokin cire kuɗi daga bankuna kan sabon tsarin da zai fara aiki daga watan Janairun 2026.

Babban bankin ya bayyana cewa an ƙirƙiri tsare-tsaren cirar kuɗi da dama a baya bisa la’akari da yanayin da ake ciki, dalili kenan da aka bijiro da wannan sabon tsarin.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 2 ga watan Disamban 2025, CBN ya ce daga cikin manufofin sauyin akwai takaita kashe kudi wajen gudanar da harkoki, ƙarfafa tsaro, da kuma dakile barazanar almundahanar kuɗaɗe.

Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, mutane za su iya cire kuɗi har zuwa Naira 500,000 a kowane mako, yayin da kamfanoni za su iya cire har zuwa Naira miliyan 5, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Ƴan kwangila sun girke akwatin gawa a ofishin ma’aikatar kuɗin Nijeriya

0

‘Yan kwangila sun girke akwatin gawa a kofar shiga ofishin ma’aikatar kudin Nijeriya da ke Abuja.

 

‘Yan kwangilar, karkashin inuwar kungiyarsu ta ‘yan asalin Nijeriya sun fara zanga-zangar lumana a ma’aikatar a ranar Talata, suna neman gwamnatin tarayya ta biya su bashin da suke bin ta.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa sun bayyana akwatin gawar da suka ajiye a matsayin wata alama da ke nuni da yadda mambobinsu ke rasa rayukansu sakamakon halin kuncin da suke ciki.

Gwamnatin Tinubu ba ta tattaunawa da ‘yan bindiga – Daniel Bwala

0

Hadimin shugaban Nijeriya Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta taɓa yin tattaunawa da ’yan ta’adda ko biyan su kuɗin fansa ba, duk da jita-jitar da ke yawo game da sakin yara ‘yan makaranta da aka sace.

 

A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Bwala ya bayyana cewa a wasu gwamnatoci da suka gabata, hukumomi na shiga tattaunawa da’ yan bindiga domin kare rayukan ’yan ƙasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Sai dai ya ce gwamnatin Tinubu ba ta amince da daukar hanyar ba, domin a cewarsa hakan na kara karfafar ‘yan ta’adda ne a fakaice.