DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 87

Kudin tikitin jiragen sama a wasu sassan Nijeriya ya haura Naira 300,000 – Punch

0

Wani bincike da jaridar Punch ta gabatar, ya nuna cewa kudin tikitin jiragen sama a wasu sassan Nijeriya ya zarta Naira 300,000.

 

Binciken ya nuna cewa yawanci yankunan da lamarin ya fi shafa sun hadar da kudu maso kudu, da kuma kudu maso gabashin Nijeriya.

 

An danganta wannan tashin farashin tikitin jiragen saman da yadda bukatar tafiye-tafiye ta karu musamman a wannan lokaci da ake dab da shiga bukukuwan karshen shekara.

An bukaci gwamnatin Nijeriya ta soke dokar shari’a a jihohin Arewa 12

0

An bukaci majalisar dokokin Amurka ta matsa wa gwamnatin Nijeriya lamba wajen cire dokar shari’a a jihohin Arewa 12 daga kundin tsarin mulki, tare da rusa hukumomin Hisbah.

 

Yayin wani taron hadin gwiwa na majalisar wakilan Amurka, mai bayar da shawara a majalisar huldar kasashe, Dr. Ebenezer Obadare, ya zargi cewa kungiyoyi masu haddasa tashin hankali na amfani da tsarin shari’a da hukumomin Hisbah wajen yada akidar tsatsauran ra’ayi, tilasta wa mutane sauya addini, tare da gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar hukunci ba.

 

Dr. Obadare ya kuma bayar da shawarar yin aiki tare da sojojin Nijeriya don kawo karshen ayyukan ta’addanci a fadin kasar, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Ma’aikatar tsaron Nijeriya na bukatar Æ™wararren shugaba – Shehu Sani

0

Tsohon dan majalisar dattawan Nijeriya da ya wakilci Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya nuna bukatar samun Æ™wararren shugaba da zai jagoranci ma’aikatar tsaron Nijeriya.

 

Kalaman tsohon dan majalisar sun zo ne bayan da ministan tsaron Nijeriya Badaru Abubakar ya sanar da yin murabus sakamakon dalilai na lafiya kamar yadda fadar shugaba Tinubu ta tabbatar.

 

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya ce a daidai wannan lokaci da kasar ke fuskantar ta’azzarar matsalar tsaro a sassa daban daban, ya zama wajibi Nijeriya ta iya kare kanta daga hare-haren ‘yan ta’adda, wanda samun kwararre ne kadai zai kai ga iya cimma wannan nasara.

Wike na rikewa Tinubu duk filin da gwamnati ta kwace a Abuja – Hadiminsa

0

Hadimi ga ministan Abuja Nyesom Wike, Lere Olayinka ya bayyana cewa duk wani fili da gwamnati ta kwace iko da mallakarsa a birnin na kasancewa a hannun ministan ne cikin aminci don ya rikewa shugaban Nijeriya Bola Tinubu.

Olayinka ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise, yana mai cewa a halin yanzu akwai filaye akalla 1000 da aka kwace ikon mallakar tasu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa kwacewar na zuwa ne sakamakon rashin bin ka’idoji ko kuma biyan wasu hakkoki daga mamallakansu.

Ya kara da jaddada cewa duk wanda ya karya doka, tabbas za ta yi aiki a kansa.

Ambaliyar ruwa ta dai-daita mutane 17,000 a Kaduna da Katsina – NEMA

0

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana cewa akalla mutane 17,000 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a jihohin Kaduna da Katsina cikin shekarar 2025.

 

Wannan bayani ya fito daga bakin shugaban ofishin hukumar na jihar Kaduna Suleiman Muhammad, yayin gudanar da aikin bibiyar yankunan da lamarin ya shafa.

 

A cewar Suleiman, irin asarar da aka samu ta tilasta hukumar yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen gudanar da ayyukan ceto da kuma na tallafi don rage radadi.

 

Kazalika ya bayyana samun rahoton asarar rai a jihar Katsina sakamakon ambaliyar, sai dai ba a samu asarar rai a Kaduna ba.

Atiku ya gana da shugabannin ADC a Abuja

0

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da shugabannin jam’iyyar ADC na jihohin kasar.

 

Atiku Abubakar ya tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa daukacin shugabannin sun kawo masa ziyara ne don yi masa barka da shiga ADC a hukumance.

 

Yayin tattaunawar, Atiku ya bukaci a samar da kyakkyawan hadin kai a jam’iyyar don tunkarar abin da ke gabansu, yana mai cewa babu bukatar bata lokaci a daidai wannan lokaci.

‘Yan bindiga sun sace manoma 11 a jihar Kaduna

0

An samu tashin hankali a Unguwan Nungu da ke mazabar Bokana a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna, bayan da ‘yan bindiga suka sace mutane 11 a lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.

 

Daily Trust ta ruwaito mazauna yankin na tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutanen cikin dazuka, ba tare da an san ina suka nufa ba.

 

Kazalika wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun nemi a biya su kudin fansa miliyan 11 kafin su sako mutanen da suka sace.

 

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya ta’azzara fargaba a zukatan mazauna yankin da kuma masu makwabtaka da su.

Gwamnonin Arewa za su tara Naira biliyan 228 don yakar matsalar tsaro

0

Gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya sun bukaci a dakatar da hakar ma’adanai a yankin na tsawon watanni shida, suna bayyana shi a matsayin babban dalilin ta’azzarar matsalolin tsaro a yankin.

 

Wannan ya biyo bayan wani taro da suka gudanar a ranar Litinin, domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar.

 

Kazalika sun bayyana shirin bude asusu wanda za su tara Naira biliyan 228 don inganta yakinsu da matsalar.

 

Karkashin shirin dai, kowace jiha da kananan hukumominta za su rika bayar da Naira biliyan 1 a kowane wata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Nijeriya ta bai wa dan adawar Guinea-Bissau mafaka

0

Gwamnatin Nijeriya ta amince da bai wa dan adawar Guinea-Bissau Fernando Dias da Costa mafaka, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

 

Wannan mataki dai na kunshe ne cikin wakikar da ministan harkokin wajen Nijeriya Ambasada Yusuf Tuggar ya aike wa da shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.

 

A cewar gwamnatin Nijeriya, daukar matakin zai taimaka wajen bai wa Fernando Dias tsaro, musamman yadda ya bayyana cewa yana fuskantar barazana tun bayan juyin mulkin.

 

A makon da ya gabata ne dai sojoji suka sanar da karbe iko da mulkin kasar ta Guinea-Bissau, daidai lokacin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana, lamarin da gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da shi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Kazalika tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, wanda ya kasance mai sa ido a zaben kasar ya nuna shakku kan juyin mulkin, yana mai zargin cewa hambararren shugaba Oumarou Sissoco Embalo ne ya kitsa shi.

‘Yan majalisar Amurka za su yi taro kan karuwar hare-hare a Nijeriya

0

Kwamitin hadin gwiwa na ‘yan majalisar dokokin Amurka ya sanar da cewa zauren zai gudanar da taro a yau Talata 2 ga watan Disamban 2025, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya.

 

Wani bayani da dan majalisa Riley Moore ya wallafa a shafinsa na X, ya tabbatar da cewa taron zai kasance ya kunshi kwamitoci daban-daban tare da sauran ‘yan majalisar.

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

Bayanin ya kuma yi nuni da cewa taron tattaunawar zai mayar da hankali kan karuwar hare-hare a sassa daban daban na Nijeriya musamman a baya bayan nan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.