DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 88

Gwamnan Osun Adeleke ya fice daga jam’iyyar PDP

0

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya sanar da ficewarsa daga jam‘iyyar PDP, yana mai bayyana rigingimun cikin gida a matsayin dalilin daukar matakin.

 

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, gwamna Adeleke ya tabbatar da cewa ya mika takardar ficewar ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar tasa.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ficewar ta zo ne sa’o’i kadan bayan da aka yi hasashen cewa gwamnan ba zai sake neman tsayawa takara a jam’iyyar ba, har sai an shawo kan matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta a tsakar gidanta na siyasa.

Sarkin Musulmi ya bukaci gwamnoni da su rika sauraron masu sukarsu

0

Sarkin ya bayyana haka ne a taron Gwamnonin Arewa da majalisar sarakunan gargajiya da aka gudanar a Kaduna a Litinin din nan, Sarkin Musulmi ya ce babu wani shugaban da zai nemi kuri’ar jama’a sannan ya yi watsi da su bayan hawa mulki.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ake yawan zargin gwamnonin da rashin daukar mataki, ya jaddada cewa kamata ya yi su fuskanci abubuwanda ke gabansu, musamman wajen yakar rashin tsaro, talauci da matsalolin tattalin arziki.

A cewarsa, ya zama wajibi shugabanni su dinga sauraron sukar da ake musu cikin lumana domin hakan na iya jagorantar su wajen yin abinda ya kamata ga al’ummarsu.

’Yan bindiga sun sake kai hari a Kano tare da yin garkuwa da mutane 11

0

’Yan bindiga sun sake farmakar wani kauye a jihar Kano, inda suka yi garkuwa da mutane 11 a Unguwar Tsamiya (Dabawa), da ke ƙaramar hukumar Shanono.

Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na daren Litinin, inda maharan suka dinga harbe-harbe ta sama tare da dukan wasu daga cikin mutane kafin su yi awon gaba da mutum 11, maza tara da mata biyu sannan suka yi awon gaba da shanu biyu.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya faru ne kwanaki kalilan bayan wani farmakin da aka kai ‘Yan Kamaye a ƙaramar hukumar Tsanyawa, wani yanki da ke iyaka da jihar Katsina.

‘Yan bindiga sun saki matashi da mata da suka sace a Abuja

0

‘Yan bindiga sun saki wani yaro mai shekaru 15 da kuma ’yan mata shida da suka yi garkuwa da su a kauyen Gidan Bijimi da ke Kawu, a karamar hukumar Bwari ta Abuja, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan biyu daga iyalansu.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar, dauke da makamai, sun kai farmaki kauyen ne a daren Laraba da misalin ƙarfe 9:30 na dare, inda suka yi awon gaba da mutanen yayin da suka kasa kama wanda suke nema Thomas Waha Sarki.

Wadanda aka sako sun haɗa da Blessing Awu, Abigail Kasabare, Asabe Joshua, Kankani Joshua, Talatu Jaba, Agnes Kasabare da David Awu.

An sako su ne a daren Asabar a dajin Kuyeri da ke cikin ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, inda aka kai kuɗin fansar.

Gwamnonin Arewa na taro kan matsalolin tsaro a yankin

0

Gwamnonin jihohi 19 na Arewa na taro a Kaduna domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da suka kunshi sace-sace, kai hare-haren ’yan bindiga da kuma karuwar tashe-tashen hankula a yankin.

Jaridar Punch ta rawaito cewa taron ya mayar da hankali wajen gano sababbin dabaru da matakan gaggawa da za su rage yawaitar hare-haren, tare da kawo karshen ta’addanci da ke addabar al’ummar yankin Arewa.

Masu shirya taron sun bayyana cewa tattaunawar ta haɗa da sabunta dabarun hadin gwiwa tsakanin jihohi, da kuma bullo da ingantattun hanyoyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnati na daf da fallasa masu ingiza ta’addanci a Nijeriya – Daniel Bwala

0

Hadimin shugaba Tinubu na Nijeriya Daniel Bwala ya bayyana cewa gwamnati na daf da kwarmata sunayen masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da ‘Television Continental’ a ranar Lahadi, yana mai bayyana cewa tuni gwamnatin Tinubu ta fara daukar tsauraran matakai kan lamuran tsaro a kasar, wadanda za su bayyana ga ‘yan Nijeriya nan ba da jimawa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito Hadimin shugaban na cewa gwamnatin ta kusa fallasa sunayen masu daukar nauyin duk wani nau’i na tashin hankali da ake fama da shi a sassan kasar.

Kazalika ya jaddada bukatar samar da hadin kai a tsakanin kasashe musamman masu makwabtaka da juna wajen yakar matsalar tsaro.

Ina fatan shugaba Tinubu ba zai sake tsayawa takara a 2027 ba – Hakeem Baba Ahmad

Tsohon mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce yana fatan shugaban Nijeriya ba zai sake neman kujerar shugabancin ƙasa a 2027 ba.

Ya bayyana hakane a gidan talabijin na Channels, inda ya ce Shugaba Tinubu bai nuna ƙwazo yadda ake buƙata ba wajen gyara kasar, duk da cika burinsa na zama shugaban Nijeriya.

A yayin tattaunawar Dr. Baba-Ahmed ya jaddada cewa tun bayan barinsa gwamnatin Tinubu, ya kan faɗi cewa shugaban ƙasar bai kamata ya sake tsayawa takara ba domin yanzu ya cimma burinsa ba tare da gudanar da mulki yadda ake tsammani ba.

Baba-Ahmed ya ce abin da aka san Tinubu da shi a baya na basira da himma babu alamun irin wannan jajircewar wajen gyaran ƙasa a halin yanzu.

Barcelona ke jan ragamar teburin gasar LaLiga

0

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta zama jagorar da ke jan ragamar gasar La Liga ta kasar Sifaniya bayan ta zarce Real Madrid da maki ɗaya

Rahotanni sun nuna cewa Barcelona ta samu sakamakon da ya ba ta damar hawa saman teburin gasar, inda Real Madrid ke biye mata baya da tazarar maki ɗaya kacal.

Zuwa yanzu dai Barcelona na saman teburin gasar da maki 34, sai Real Madrid da ke biye mata da maki 33, ta ukunsu ita ce Villa Real da maki 32.

Me kuke ganin ya jawowa Madrid fadowa zuwa mataki na biyu?

Ana zargin ‘yan bindiga da sace budurwa sa’o’i kadan kafin daurin aurenta a jihar Sokoto

0

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kutsa kauyen Chacho a karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto da tsakar dare, inda suka yi awon gaba da amarya da kawayenta sa’o’i kaɗan kafin a daura aurenta.

Lamarin, wanda ya faru misalin ƙarfe 1 da rabi daren Lahadi, ya shafi amarya, kawaye, tare da wasu bakwai mata da mutum ɗaya namiji da aka ce an yi garkuwa da su, yayin da mutum ɗaya ya jikkata.

Mazauna kauyen sun koka kan jinkirin zuwan jami’an tsaro, inda suka ce an sanar da su tun da wuri amma suka iso bayan awa guda kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar ’yan sandan Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa har yanzu cikakkun bayanai ba su fito ba.

Yan bindiga sun kai hari a wani coci inda suka sace Fasto da matarsa da wasu masu ibada a jihar Kogi

0

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da harin da aka kai wa Cocin Cherubim and Seraphim a garin Ejiba, karamar hukumar Yagba ya Yamma, da safiyar Lahadi, wanda ya jefa al’umma cikin tashin hankali.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar daga Lokoja, yana kuma Allah-wadaran harin da ’yan bindiga suka kai wa coci tare da sace fasto, matarsa da wasu masu ibada.

A cewar rahoton jaridar Punch, harin ya tayar da hankalin jama’a, inda mazauna yankin suka tsere domin neman tsira, yayin da gwamnati ke tabbatar da cewa tana ƙoƙarin kubutar da dukkan mutanen da aka sace.